Daga Muhammad Alkasim
Koda yake kalmar bala'i abar gudu ce, amma in aka gwama ta da qauna takan sauya yanayi ta koma abar sha'awa wace kowa zai yi fatar a ce shi ake gaya wa wannan jumlar, wato: "Ina bala'in qaunarki!"
.
Ba abin da mace take so kamar ta ji wannan daga bakin wanda take qauna, ba ta damu da yanayin da ya fada ba, in dai zai fada bil haqqi har cikin zuciyarsa an gama.
.
A daidai wannan gabar ake tabka ta, domin kuwa mafi wayan wadan da suke furta wannan jumlar ko tantama babu maqaryata ne, kodai ya kasance sun fada ne don jefar da kashi su huta da quda, ko kuwa qara wa miya gishiri.
.
Dalilin fadin haka kuwa, ta ya za a ce ba ka zauna da mutum ba, ba ka san kyawunsa na waje da na ciki ba, ba ka qimanta yadda yake fushi da hanyar sanyaya masa rai ba, ba ka yi musayar so da shi ba, amma kai har qaunar ta kutsa zuciyarka ta gama da rayuwarka?
.
Lura da kyau ka gani, akwai maza masu fada wa mace irin wannan kalmar a hanyoyin sadarwa na zamani, ko hutonta suka gani ba ka sake jin duriyarsu, to bare kuma wasu da suka je wurinta suka yi ido biyu da ita.
.
Wani lokaci mace takan yi mamakin yanda namiji zai nuna yana mutuwar qaunarta, amma da zarar sun yi ido biyu sai ka ga in ba ita ta kira shi ba ba ya ko lura da lamarinta, a hankali sai ka ga abin ya mace gaba daya.
.
Ba wata soyayyar da za a fara ta a kan yanar gizo a kuma yi zaton wai mai dorewa ce, shirye-shirye ne kawai na yaudaran kai, da bata wa juna lokaci.
.
Soyayya ta gaskiya takan fara ne daga lokacin da namiji zai fita, tunaninsa kawai yabar wata a gida, wace ba ta da komai sai tattalinsa, shi ma din a waje zammarsa kawai ya tanadi abin da zai kai wa iyalin don ya faranta musu rai.
.
Da zarar ya dawo ya iske ta sai ransa ya yi haske ganin ya same ta da surar da yake tsammani, ita ma wani farin ciki ya lullube ta ganin cewa ya dawo lafiya.
.
Wannan a waje kenan, in suka shiga daki kuma Allah kadai ya san abubuwan da suke cikin zukatansu, da yadda kowa yake jin masoyinsa a zuciyarsa.
.
Zancen saurayin da bai auri budurwa ba, ta ina wannan soyayyar ta ginu har da za ta zame masa bala'i? Au na tuna, duk abin da ba a gina shi a turba na qwarai ba tabbas yana iya sauyawa cikin dan qaramin lokaci ya zama masifa ma.
.
Don haka, kin fara soyayya da wane? Yaushe kuka yi zai zo gidanku? Wa ya san abin da yake tsakaninku? Kina kuwa dan tuntuban magabata a kan wasu al'amuran da ba ki gane ba?
.
A duk lokacin da kika yaudaru da cewa INA BALA'IN QAUNARKI to ba shakka ke ma kin fara shiga wani bala'in, don in maganganun namiji ne, ko uwar mata ba ta iya kauce musu bare mace mai 'yan shekaru.
.
To kenan ba a soyayya a yanar gizo? Amsar ita ce ana dai musayar sha'awa, wace ko a al'adance ba marhabin ake yi da ita ba, bare kuma addini.
.
Gyara kayanka ba zai taba zama sauke mu raba ba.
Title :
Ina Bala'in Sonki
Description : Daga Muhammad Alkasim Koda yake kalmar bala'i abar gudu ce, amma in aka gwama ta da qauna takan sauya yanayi ta koma abar sha'awa w...
Rating :
5