Ya kai dan'uwa mai daraja ka DAURE ka KARANTA DOMIN akwai babban abun rabauta aciki.
Malam fiqihu suna cewa IMANINKA ZAI kARU IDAN KANA YAWAITA yin wadannan abubuwa guda UKUN
1- Tilawal Al-Qur'ani.
2- Qiyamul-laili.
3- Azkharrr. (Wato anbaton Allah)
Sun Kara da cewa ZAKA FUSKANCI MATSALA A QABARINKA
IDAN HAR KA MUTU DA ABU UKU.
1- Hakkin Wani.
2- Annamimanci.
3- Hassada da abinda Allah yayi.
Sun kuma ce IDAN KA RASA ABUBUWA GUDA UKU KUMA KAYI HAQURI ADALILIN HAKURINKA ALLAH ZAI GINA MAKA
KATAFAREN GIDA A ALJANNAR
SA, sune kamar haka.
1- karasa yaranka Qanana Guda uku Wanda basu balaga ba.
2- Rashin Mahaifinka, ko Mahaifiyarka.
3- Rasa wata ni'ima ajikinka Misali,
* idonka-
* Qafarka-
* Hannunka-
* jinka ko
* Ganinka.
Sun Kara da cewa akwai wasu ABUBUWA GUDA UKU SUNA
KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA, wato:
1- Yawan yin Istigfari.
2- Qiyamul-laili...
3- Da yawaita yin Sadaka don Allah.
Ya dan'uwa IDAN HAR ALLAH YA BAKA ABU UKU TO
KA NUNA GODIYARKA GA
UBANGIJINKA sune:
1- cikekkiyar koshin Lafiya.
2- Wadata na ingantaccen Arziki.
3- kaifin Basira mai inganci.
Malamai suna cewa KADA KA YARDA KA AURI MACE
MAI DABI'A kamar haka:
1- Mace mai yawan fushi..
2- Jahilar mata wanada take da karancin Sani.
3- Mata kazama wato marar tsafta.
Sun Kara da cewa kuma KAYI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN wadannan Abu.
1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana..
3- Hakuri da Jarrabawar Allah.
Sun ce ABUBUWA GUDA UKU KADA KA AIKATASU HAR SAI KAYI TAMBAYA AKANSU,
1- Yin ibadah.
2- Aure.
3- Sana'a.
Har ilayau akwai ABUBUWA GUDA UKU BAKA SAMUN
SAKAT AKANSU, HAR SAI SUN
RABU DAKAI,
1- Yawan yin Wasi-wasi..
2- Bashin da'ake binka.
3- Mugun Makofci.
Ga wasu ABUBUWA guda UKU muyawaita ROKON ALLAH
(s.w.t)YA TSAREMU DA AIKATA SU,
1- yanke Zumunta..
2- Zagin Sahabbai..
3- Mutuwa da hakkin wani
akanmu.
Ya dan'uwa MUTANE UKU KADA KA KUSKURA kayawanta
SAURARON MAGANAR SU,
1- Makaryacin mutun
2- Magulmacin bawa.
3- Malami maiyin abinda addini baizo dashiba.
MUTUM UKU KADA KA YARDA SU
DINGA KUSANTARKA,
1- Munafiki.
2- Mazinaci.
3- Mai hassada.
ABUBUWA GUDA UKU KADA KA
YARDA KA JINKIRTASU IDAN LOKACINSU YAZO,
1- Yin Sallah akan lokaci
2- Aure inkanada halin yi.
3- jana'izan mamaci.
Gawasu ABUBUWA GUDA UKU IDAN HAR KAYI RIKO DASU, ZAKA SHIGA ALJANNAH DA
IZININ ALLAH.
1- Mai tsananin hakuri da ikon Allah
2- Yawaita yin kiyamaullaili.
3- Amfani da Halal wajen Gudanar
da Rayuwa.
ABUBUWA GUDA UKU SUNA
SANYA MUTUM CIKIN HALIN QAQANI- QAYI.
1- Mutuwar Zuciya.
2- Hassada.
3- Talauci mai Tsanani.
ABUBUWA UKU SUNA MANTAR
DA MUTUM LAHIRARSHI.
1- Dogon Buri.
2- Rashin karanta Alqur'ani
3- Nisantar Wurin da ake Wa'azi
MUTANE UKU HAKKIN ALLAH NE
YA TAIMAKE SO.
1- mutumin da yake Neman aure
Don ya kare mutuncin kansa.
2- Mutumin da ya Tafi jihadi
Domin Daukaka Kalmar Allah.
3- (Bawa) Wanda aka Dora masa
Fansar kansa.
KASHEDINKA DA AIKATA ABUBUWA
UKU.
1- Zina, Da Liwadi, Da Madigo..
2- Shirka wa Allah.
3- Mu'amala Da Kudin Ruwa
(Interest).
KADA KAYI SAKACI DA ABUBUWA
GUDA UKU ARAYUWARKA,
1- Lokacin da Allah ya baka.
2- Lafiyar da Allah ya baka.
3- Ilimin da Allah ya baka.
ABUBUWA UKU SUNA SA ZUCIYA
TA QEQASHE, KUMA SUNA SA ZUCIYA TAYI BAQIQQIRIN.
1- Rashin yarda Da Qaddara.
2- Zagin Yardaddun Allah.
3- Wulakanta Iyaye Da Bijire musu.
KADA KA YARDA KA NEMI ILIMI
AGURIN MUTUM UKU,
1- Mai yawan Mantuwa.
2- Mai yaudara Duk iliminsa..
3- Malamin da ba'a yi masa
fatawa.
ABUBUWA GUDA UKU SUNA
SAURIN RUSA JIKIN DAN-ADAM,,
1- yawan yin jima'i.
2- Barin jiki da yunwa.
3- Shiga Cikin Damuwa..
YA dan'uwa mai daraja ka Sani
abubuwan Suna da yawa sai dai mu dan taqaita anan zuwa wani lokaci.
Dafatan Allah shi Kara bamu daman nashiha ma junanmu cikin gaskiya da amana, Allah kuma shi gafarta mana kurakuranmu, shi sa mugama da duniya lafiya, Amen.
Barkanmu da jumma'a.
Title :
Goron Jumma'a Daga Mai Martaba Sarkin Bauchi (Dr) Rilwanu suleimanu Adamu CFR.
Description : Ya kai dan'uwa mai daraja ka DAURE ka KARANTA DOMIN akwai babban abun rabauta aciki. Malam fiqihu suna cewa IMANINKA ZAI kARU IDAN KANA...
Rating :
5