An haifi Jafar a garin Daura ranar 12, ga watan Febrairu, 1960, ya rasu ranar 13, gawatan April 2007. Ya fara karatu a makarantar horar da malamai ta Gwale, cikin shekarar 1984. Ya kuma kammala karatunsa cikin shekarar 1988.
Cikin shekarar 1989 ya samu shiga kasaitacciyar jami'ar addinin musulunci, wacce ke Madina. A nan ma ya yi shekaru hudu yana karatu, ya kammala shi cikin shekarar 1993.
Yana dawowa gida bai yi wata-wata ba ya kama wa'azi, ya kuma kafa cibiya mai suna Usman Bin Affan. Cikin shekarar 1995, wannan cibiyar ta shahara kuma ta zama wacce take cin gashin kanta. Yana koyar da mutane da yawa karatu na addini, duk watan Azzumin Ramadan, ya kan yi tafsiri a garin Maiduguri.
Har ila yau shi ne shugaban asusun wannan cibiya ta Usman Bin Affan. Ya wakilci Najeriya a gasusukan karatun Al'kur'ani a lokuta daban-daban. Yana cikin kwamitin Malamai na jihar Zamfara da Bauchi. Yana gudanar da karatuttuka a gidajen rediyo, da talabijin daban-daban. Kamar Rediyo, Kaduna, Bauchi ARTV Kano, DITV, Kaduna NTA Borno, OITV Damaturu, NTA ayola.
Ya rasu ranar juma'a 13, ga watan Afrilu, 2007, kimanin karfe 5:30, na asuba. A lokacin yana jagorantar Sallar Asuba, a Babban masalacin Juma'ar dake unguwar Dorayi. Wasu ne wadanda har yau din nan, ba a gano su ba. Da makamai suka shigo, har cikin masallaci suka bindigeshi. Sun harbe shi a kirjinsa da wurin cibiyarsa.
An yi hanzarin wucewa da shi babban asibitin koyarwa na Aminu Kano, amma ko kafin likitoci su zo gare shi, ya bar duniya.
A karin bayanin da za mu bayar anan shine, ya yi digiransa na uku, wato digirin digirgir, a jami'oin Bayero, da Danfodio. Sannan zuwansa Kano daga Daura, ya yi karatu irin na Alo, sannan, yaxyi dalifta, a wurin maluma da yawa, a Kano.
Allah ya jikan Sheik Ja'afar Mahmud Adam, Allah ya albarkaci zuru'arsa. Ibrahim Suleiman ya bada gudunmuwa da wasu shafuka, kuma a yanar gizo da muka bi.
Title :
Gajeren Tarihin Sheikh Jafaar Mahmoud Adam
Description : An haifi Jafar a garin Daura ranar 12, ga watan Febrairu, 1960, ya rasu ranar 13, gawatan April 2007. Ya fara karatu a makarantar horar da m...
Rating :
5