Fitacciyar mawakiyar nan Binta Labaran wadda aka fi sani da Fati Nijar ta yi wakoki na musamman domin jinjinawa shugaban sojoji Janar Tukur Yusuf Buratai kan yadda yake kokarin dawo da martabar tsaro a kasar nan.
A yayin da wakilinmu ya tuntubi zabiyar ta waya kan dalilin da ya sa ta rera wakokin, Fati ta bayyana cewa "ba komai ne ya sa na rera wakokin ga Janar Buratai ba, sai don na jinjina masa kan yadda yake kokarin dawo da martabar tsaro a kasar nan, musamman yankunan Arewa maso Gabas da suke fama da rikicin Boko Haram".
Fati ta kara da cewa rera masa wakar tamkar kara karfafa masa gwuiwa ne kan namijin kokarin da yake yi.
Fati ta rerawa Janar Buratai wakoki ne har guda hudu, sannan kuma nan bada jimawa ba wakokin za su shiga kasuwa da na bidiyo da kuma wanda ba na bidiyo ba.
Zabiyar ita ta dauki nauyin gudanar da kundin wakokin a karkashin kamfaninta na Girma-Girma, inda kuma Abu Sarki ya shirya tare da bada umarni.
Sources Rariya
Title :
Fati Nijar Tayi Wakoki Wa Janar Burutai
Description : Fitacciyar mawakiyar nan Binta Labaran wadda aka fi sani da Fati Nijar ta yi wakoki na musamman domin jinjinawa shugaban sojoji Janar Tukur ...
Rating :
5