Idan zaku iya tunawa, da farko dai ana maganar rashawar Dala Biliyan 2.9 ne. Daga baya ne hukumar EFCC ta bayyana cewa ta gano wani akawunt wanda a cikin shi akwai sama da Dala Miliyan 500. Amma ta kasa gano ko nawa nene, amma ta kulle shi.
Sannan kuma hukumar ta bayyana cewa ta amshe gwalagwalai daga hannuntsohuwar minstar Mai, Diezani Alison Madukwe
Sannan kuma hukumar ta bayyana cewa ta amshe wani mashin gwajin marassa lafiya wanda darajar shi takai na Naira Biliyan 2.6, a asibitin tsohon Hafsin sojin Sama, Adesola Amosu.
” Daga binciken mu, sama da Dala Biliyan 15 ce akayi al’mundahana da ita. An fadi rashawar Dala Biliyan 2.6 ne dmin wadanan sune wadanda aka ringa dauka ana rarraba ma mutane.
” zamu gurfanar da mutanen da kuma kamfanonin da suke da hannu cikin wannan rashawar. Amma abunda ke a gaban mu shine a gano kudaden.
Wata majiya ta bayyana cewa abunda hukumar EFCC ta gano a cikin shekara 1 da hawan Buhari, yafi abunda ta gano tunda aka kafa ta, inda yake fadada bayani akan rashawar Alison MAdukwe, da kuma dan kasuwa Jide Omokore.
Hukumar EFCC na cigaba da kokarin ganin ewa ana yaki da rashawa da kuma kwato kudaden da wasu manyan gwamnatin Jonathan suka sassace a cikin shekaru 6 na mulkin Jonathan din.
Title :
EFCC Ta Gano Dala Bilyan 12.9 Na Makamai
Description : Idan zaku iya tunawa, da farko dai ana maganar rashawar Dala Biliyan 2.9 ne. Daga baya ne hukumar EFCC ta bayyana cewa ta gano wani akawunt ...
Rating :
5