Dole ne idan dai har tsohon gwamnan jahar Bauchi wato Isah Yuguda yana so ya shiga jam'iyyar APC to dole ne ya bi ka'idojin jam'iyar wanda ya zama wajibi ya koma wajen shugaban mazabar sa domin samun rijistar zama dan jam'iyyar idan shugaban mazabar sa ya amince masa.
A ta bakin sakataren yada labarai na jam'iyyar APC na jihar Bauchi , Awwalu Jalla, ya bayyana cewa suna sane da gurbataccen halayen siyasa na Isah Yuguda wanda duk jam'iyyar da ta yi masa riga da wando sai ya yadure ta daga karshe. Inda ya bayyana cewa sanin kowane jam'iyar ANPP a baya ita ce ta dora Yuguda kan mulki amma kuma ya bar ta ya koma PDP, daga bisani kuma ya bar ta yana 'yan kame-kame.
Awwalu Jalla, ya bayyana jam'iyyar APC ba ta da wata doguwar bukata da Yuguda wanda har za ta yi wani azarbabin murna da shigarsa jam'iyyar. Haka kuma ya yi kira ga al'umma da su yi watsi da duk wani labari da ake yadawa cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC na neman Yuguda da ya dawo jam'iyyar ta su.
Idan dai ba'a manta ba kwannan ne tsohon gwamnan jihar ta Bauchi, Isah Yuguda ya bayyana ficewar sa a jam'iyyar PDP.
Title :
Dole Ne Yuguda Ya Bi Ka'idojin Jam'iyyar APC Idan Har Yana Son Ya Shiga Jam'iyyar
Description : Dole ne idan dai har tsohon gwamnan jahar Bauchi wato Isah Yuguda yana so ya shiga jam'iyyar APC to dole ne ya bi ka'idojin jam...
Rating :
5