A wayewan yau ne naje garin Kano. Wurin misalin 4:00p.m na je tashar gyadi-gyadi domin in hau motan kaduna se na hadu da wata baiwar Allah, kamar yanda ta kira kanta da suna Aisha Abdullahi daga karkasara. Bayan mun gaisa. Irin yanda akeyi idan an shiga mota. Tayi min tayin biscuit da sweet din da take sha a Lokacin amma ban karba ba. Tana sanyene da uniform din islamiyya tareda alqur'ani, wanda hakan ya bani daman tambayar ta akan cewa :"Daga islamiyya ne tafiyam ya tashi mata?" se ta ce min a'a kawai xataje wurin mahaifiyarta ne saboda Jiya ta fada daga Gidan bene(upstairs). Ta nunamin irin ciwon da taji daga hannuwan ta har zuwa qafanta. Naji tausayinta matuqa se na tambayeta an kai ta asibiti dai ko? Ta amsamin da cewa ey an kaita. Na qara da tambayanta garin yaya ta fado? Se tace guje-guje sukeyi ita da qaninta. Ahakan dai muka 'dan yi Sabo irin na matafiya, kuma dayake yarinya ce qarama se na tayata hira ba wai dan na saba yin hakan ba. Katsna daga isowarmu kaduna se na tambayeta wani unguwa me xataje saboda ta fadamin bata taba hawa motan haya zuwa wuri me nisa ba. A Lokacin ne take fadamin wai ZANGO zataje. Na tambayeta ta wurin ina a zango din? Se tace bata sani ba. Na bata wayaa nace ta kira Maman nata awaya ta tambayeta daidai inane gidan nasu, se tace ay bata da waya a hannunta dan haka batasan number din ba. Daga nan ne se nace mata xata gane gidan idan anje unguwan? Saboda dare yayi ko a lokacin 7:30p.m gashi anata yayyafi. Toh dayake hanya daya ne da unguwan da nake da kuma ita unguwan da tacemin xataje se nace mu jira hanya Inyaso se in nuna mata inda xata hau keke napep din ya idan mun isa. Muna isa inda ya kamata ta hau napep se tace wai baxata sauka ba se a inda ni xan sauka. Nace mata ba wuri daya bane amma tace xata gane hanyan. Bayan mun sauka daga motan kenan se nace toh nidai zan tafi gidan mu ita kuma ga inda xata samu kike napep da xe kaita zangon. Daga nan se ta fara shesheqan kuka wai ita ba haka ba. Wai guduwa Tayi a sanadiyyan dukan da kishiyar mamanta tayi mata. Daga nan ta fara fadamin magananganu wanda hakan yasa na taho da ita gidan mu se mahaifiyana ya miqata ga hannu police dominated su tsananta bincike. Bayan sunyi iyakar abinda xasu iya na yau se suka dawo mana da ita domin mu bata abinda da kuma makwanci.Yanxun dai Haka a yayi da nake rubuta post din nan muna kwance tareda. Ita cikin koshin lafiya. Dan Allah kuyi broadcasting wannan message din har se Allah yasa ya kai ga wanda yasanta. Nagode... I remain MUNEERAH LAWAL ATK. For more details contact me via my number 09053338840 or 08034532118(Alh.Lawal ATK) or 08183746642/08101658480(Police in charge of the case)
Daga Muneerah Lawal
Title :
Daga Jama'a: Yau Na Gamu Da Abin Al'ajabi
Description : A wayewan yau ne naje garin Kano. Wurin misalin 4:00p.m na je tashar gyadi-gyadi domin in hau motan kaduna se na hadu da wata baiwar Allah,...
Rating :
5