Mataimakin shugaban kasa akan harkokin 'yan jarida, Garba Shehu, ya ce babu laifi idan Nijeriya ta ciwo bashi daga China domin ayyukan raya kasa da kuma jin dadin al'umma za a yi da kuɗaɗen.
A yau ne dai ake sa ran shugaba Buhari zai kammala ziyarar aiki ta mako guda da ya kai kasar China, Wanda ya tattaunawa da manya jami'an kasar akan ayyukan ci gaba da bunkasa kasa.
Masu sharhi akan tattalin arziki da kuma bunkasa kasa dai suna cewa shugaba Buhari ya je China ne domin neman rance ga Nijeriya, al'amarin da wasu 'yan Najeriyar suke suka.
Garba Shehu ya ce Nijeriya ba za ta iya zama a kaɗaice ba, ba tare da mu'amala da sauran kasashen duniya ba.
Dangane kuma da amfanin ziyarar ta China, Shehu ya ce kasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjeniyoyi da dama da suka hada da ayyukan titunan jiragen kasa da ayyukan wuta da noma.
Title :
Babu Laifi A Bashin Da Buhari Zai Ciwo - Garba Shehu
Description : Mataimakin shugaban kasa akan harkokin 'yan jarida, Garba Shehu, ya ce babu laifi idan Nijeriya ta ciwo bashi daga China domin ayyukan ...
Rating :
5