===>AZAL<====part 8
NA
Aubakar AUYO...
A lokacin da Dan Hajiya ya zowa da Kotu da muradi na karshe cewa Alkali ya yiwa Allah a samo masa sigari Aspen ya tuttulawa cikinsa kafin rataya, a lokacin ne Tanko ya shigo kotun da Sadiya, Sadiyar da ta wayi gari da rashin sa’a ya cafko ta a wani kwararo, ta zo kotun da wani batu mai sa dimauta, cewa
“Nine na kashe mijina, wanda a ke zargi da aikata kisan, bai san komai ba, hasali ma azal ce ta afka masa, ina fitowa a gida bayan aikata kisan muka hadu da shi a karo na farko.
Jama’a suka sau baki suna kallon-kallo, Dan Hajiya ya bi mutane da wasasshiyar fuska sa’an nan ya bi Sadiya da kallon tsana, yayin da a bangaren Alkali ya fara rubuce-rubucensa har zuwa lokacin da wani firgitaccen Likita ya sukwano cikin kotun a guje ya na cewa
“A gafarce ni, sakamakon gwajin zanen yatsun wannan bawan Allah da na jikin wukar kisan ba daya ba ne, wasu Mutane ne da suke tsama da shi suka zo suka bani wasu makudan kudi a kan na fitar da sakamakon karya.”
Alkali ya bada umarnin a kamo mutanen, sa’an nan ya ci gaba da cewa
“Kotu ta wanke Dan Hajiya bisa zargin da a ke masa, sa’an bisa cin amanar aiki, Likita zai tafi gidan Dan Kande na shekara hudu, sa’an nan bisa amincewar Sadiya wajen aikata laifin, kotu ta…”
A dai-dai nan Cecelia Dadiron marigayi Mubarak ta shigo kotun a kan keken guragu tana rokon alkali ya ba ta dama ta yi Magana, a ka ba ta
“Eh, tabbas Sadiya ita ce ta aikata laifin kisa amma bisa kuskure, a lokacin da wannan al’amarin ya faru ina gidan saboda ni Yarinyar Marigayi Mubarak ce, bayan mun rabu da shi sai na zagayo ta baya na leka ta taga ina kallon abun da yake faruwa kuma ina recording ta waya ta, saboda haka a kan idona komai ya faru., abun da ya hana ni bayyana da wuri shine ina fitowa a gidan wata mota ta yi gaba dani zuwa cikin lambatu, na farfado da karyayyiyar kafa a asibiti, kafar da ciwo ya shiga ciki har sai da a ka yanke.”
Mutanen da ke kotun suka fara kallon - kallo tare da mamaki
”Za mu iya ganin Videon?” Alkali y ace
Cecelia ta ciro wayarta ta kunna Videon, Prosecutor ya karba ya kaiwa Alkali, Alkali ya karba ya fara kallo, kallon komai a kan kisan kuskuren da Sadiya ta yiwa mijinta a kokarinta na ceton kai!
.
KARSHE!
Fatan kunyi enjoying labarin na AUYO???