Kasar Amurka ta bayyana cewa zata maido kudade kimanin Dala Miliyan 480 kimanin (Naira Biliyan 95) wadanda ake zargin cewa tsohon shugaban kasa ya sace su.
Jaridar The Nation ta bayyana cewa ana cigaba da tattauna sharuddan maido da kudaden gida Najeriya.
Ma’aikatar Shari’a ce ta Amurka ta fara binciken domin ware kudaden Najeriya wadanda aka sace aka kai ce domin a maido su gida najeriya.
Shirin maido da kudaden yazo ne bayan da Ministan Shari’a Abubakar Malami da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu suka je kasar ta Amurka suka tattauna da jami’an kasar akan cigaba da kokarin maido da kudaden najeriya wadanda jami’an gwamnati suka sace.
” Wadannan kudaden sune makudan kudade mafi yawa wadanda aka taba ganowa na wani tsohon jami’in Najeriya, majiyar a Amurka ta bayyana.
” DOJ da AGF da EFCC sun gama tattaunawa, yanzu mu shirye muke da mu maido da kudaden.
“Wasu lauyoyi na taimaka da yin haka, amma DOJ tafi san ayi magana gwamnati da gwamna.
” Ina mai tabbatar maku da cewa za’a maido kudaden, idan ma akwai wani abu daya rage shine sharuddan da Amurka zata sanya domin maido da kudaden.
Wannan ba shi bane karo na farko da aka fara anso kudaden da Abacha ya sata a lokacin da yake mulki soji. A lokacin Abdulsalam Abubakar, Olusegun Obasanjo, Yar’adua, Jonathan duk an anso kudade daga kasashen duniya daban daban wadanda duka ance na tsohon shugaban kasan Najeriya ne.
A wani labarin kuma, majalisar Najeriya na kokarin hana shugaban kasa Buhari maido da kasafin kudi na 2016 domin ayi mashi garan bawul akan wasu kura kuari da kuma sabani da ake cigaba da samu tsakanin gwamnati da yan majalisar Najeriya.
Title :
Amurka Zata Maido Da Kudaden Abacha Najeriya
Description : Kasar Amurka ta bayyana cewa zata maido kudade kimanin Dala Miliyan 480 kimanin (Naira Biliyan 95) wadanda ake zargin cewa tsohon shugaban k...
Rating :
5