Har Musti ya ciro kwalin sigari zai sha sai kuma ya tuna alqawarin da ya yi, ga kuma maganar da ya gaya wa su Sani yanzu-yanzunnan, sai nan take ya mayar da shi aljuhu, Sule ya harare shi, ya yi wani tsoki "Mts!" Ya juya ya kalli Sani " Don Allah kana ganin abin da nake gani kuwa? A ganinka abin nan da yake yi da gaske yake? Ni ina ganin kamar yaudarar kansa yake so ya yi, don wanda ya ce ba ya son kaza ko romonta aka ba shi ba ya so, shi ya ce ya tuba da shan sigari, amma ya ci gaba da yawo da ita a aljuhu, dazu ma me ka gani?"
.
Sani ya gyara zama ya dan qyale murya yana kwaikwayon maganar Ustazai, kamar dai yadda ka san batattu suna yi "A'uzubillahi minas shatanir rajim! Kai Musti in da gaske kake yi ka tuba, wato ainihi ba ka da mafita sai dayan abubuwa guda biyu, ainihi ko dai ka ba mu sadakar sigarin da ke aljuhunka don neman lada, ko kuwa ka mutsittsikata gaba daya ka watsar, wannan kuwa wato ainihi ba ko shakka almubazziranci ne da kudi, ko me za ka ce ne Asshek Sule?"
.
Sule ya amshe, shi ma din dai ya qyale muryar sai cewa suke yi "Ainihi" har ma a inda bai dace ba "Ba shakka almubazziranci babban laifi ne, ina ganin wannan laifi ya kai a kira shi da babban zunubi, don haka dole maganar Sani kawai za a bi, dole kawai ka yi sadaka da wannan sigarin, sannan in za ka bayar kuma mu ya kamata ka ba wa, don mu ne 'yan uwa makusanta, ainihi komai da na gida ake farawa ba na nesa ba.
.
Musti ya sa hannu a aljuhu àyana qoqarin ciro kwalin sigari "Dadina da Musti daukan nasiha, ko rukoda ta shafa masa lafiya" in ji Sani, Musti na zaro kwalin sai ya mutsuttsika shi gaba daya, tabar da ke ciki nan take ta zama gari, nan fa Sule ya bude baki ya kasa rufewa kallon Musti kawai yake yi yana mamaki, ya juyo ya kalli Sani ya ga ai shi ma kallon Musti din yake yi, ba wanda ya zaci haka a cikinsu.
.
"Amma Musti ka san kan tsiya wallahi, to wannan me kenan? Ka san dai duk karatun da zaka yi yanzu ba sakaran da zai dauke ka a matsayin malami, ba nau'in tabar da ba ka sha ba, duk wata barasa ka dibga, sannan yau ka zo ka ce ka zama malami su kuma su saurare ka? Gwara ma ka sake tunani, don ka makara" In ji Sani, Musti ya juyo ya kalle shi, bisa ga dukkan alamu da gaske yake "Sunana Mustapha"
.
Sani ya qyalqyale da dariya ya miqe ya daki qasa da qafa "Yau ka yi karo da shedan ba shakka, mu za ka gaya wa cewa sunanka Mustapha? Ko dai yau giya ka shawo ne? Kai mu je ma a Mustaphan wanne ne a ciki, Almustapha na Abacha, ko Mustapha Jakolo ko na Hausa fim? Bábá wasu fa sun riga ka, sun tafi da sunan gwara ma kawai ka riqe sunanka na muslunci" "Musti din?" In ji Sule, ba dai wanda ya amsa masa, mamaki kawai yake yi, yana jira ya ga me Musti zai sake fadi.
.
Da dai Sani ya ji ya yi shuru sai ya dora da cewa "Ga alama dan iskannan fa da gaske yake, yanzu za ka ga shi ma ya fara yi wa mutane kallon alatsine" Sule ya kalli Sani "Irin wannan ai mun saba gani, ya kuka qare da 'yar taqawa zahiriyyan nan da ka nema? Ai kai ma ka canja gaba daya" ya juya ya kalli Musti yana dariya ya cewa "Su Sani ne da jallabiyya da jan rawaninnan irin na Saudiyya ga wata doguwar tasbaha don dai kawai Hafsah ta ce shi na qwarai ne, yau ba ga shi da ta watsar da shi ka dawo gidan jiya ba? Qyale shi shi ma ya gama zaqin dan Ustaz dinnan nan zai dawo ne mu tafi tare, za kuma ka ce na gaya maka" Sani ya daga hannu yana girgizawa alamar rashin yarda da maganar Sule, har ya yi shuru kamar ba zai ce komai ba amma ya kasa hadiyewa sai da ya bara.
.
Ya dubi Sule cikin sauri "Kar ka hada matsalata da ta Musti, don wallahi ba don 'yan sa ido ba da na auri Hafsah, don duk wani goyon baya ta ba ni, har ranar daura aurenta ma ta aiko min da wasiqa tana ba ni haquri, ta ce wallahi ba ita ta qaurace min ba an dai fi qarfinta ne kawai, na kuma gaya maka kai ma ka sani, ba wanda zai nemi aure a cikinmu sai an sami munafukan da za su kai qararka, su kwaso gaskiya da qarya su watsa a kunnin uwayenta, in ba dace aka yi ba sai ka ga neman ya fara tangadi, ko ma a rasa gaba daya, sai dai dadinta duk sharrin mutum bai isa ya ce muna daukar abin wani ba, sai dai ya ce muna shaye-shaye, wannan kuwa ko a Saudiya ana yi"
.
Sai da suka zo wannan gabar Musti ya shiga maganar "Au! To ai tun farko ta gano ka cewa kai ba Ustaz din gaskiya ba ne, kana taka wando, a iya sanina duk wandunansu a dage suke, sannan kana kwande gemu gaba daya, ka taba ganin malamin gaskiya ya cire gemu in ba 'yan Shi'a ba? Ko su din ma ba dukansu ba, ban da wannan ma, su fa 'yan izala suna da shakku game da jan tasbaha, kai kuwa ka dauki wata doguwar tasbaha ka nufe ta, wallahi na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, ba ka ma san abin da masu riqe da tasbahan suke cewa ba"
.
Sani ya dubi Sule ya ce "Ka ji dan iskan na ka tun bai gama shiga ba, qafa daya ciki daya waje har ya fara kiran mutane jahilai, ai ba mamaki, ba ga su nan muna karantawa a fesbuk ba? Kowani matashi ya dan fara fahimtar karatu, malamansa ne kuma abin zagi, wadan da kowa ya san qoqarin da suka yi wa muslunci! Kai ma sai ka shiga tawagarsu"
.
Sule ya dora tasa maganar kan ta Sani 'Ba shakka an ce abin da suke yi kenan a 'yan kwanakinnan, amma kai ma Sani in za a fadi gaskiya kai da bakinka ka ce ta tambaye ka ko ka san Tajiwidi, ka ce: A wace unguwa yake? Ta ce: Na karatun Qur'ani mana, ka ce: Qwarai ka san shi sosai sai dai ka manta ko a izifi na nawa yake, sannan ma ba ka san cewa iyakar Qur'anin izifi sittin ba ne har ka fara qoqarin cewa kanajin bai dai qarisa izifi na dari ba!" Ba wanda bai yi dariya ba, Musti har yana hawaye "Sule ka san dalilin da ya sa ya ce ya manta izifin? Yana qoqarin ya riga ta ne kar ta tambaye shi, ai Sani ni kam wallahi daga yau na yi wa kaina fada, ina roqon Allah ya taimake ni kan niyyar da na yi".