.
Musti ya kama hanya kamar zai wuce, sai kuma ta ba shi cewa ya kwano ya yi musu sallama "Da wa ya ce ka wuce?" Sai da Sani ya harareshi kafin ya tambaye shi "Shedan mana, in ba shi ba wa zai ba shi umurni? Ko ba komai ai kasan abokai ne, don ko barci ma ba ya shiga tsakaninsu" in ji Sule, nan take Musti ya mai da masa da martani "Maganarka dutse Sule, wallahi kuwa shedan ne ya sanya na wuce, don har na yi niyyar tsayuwa a nan sosai, ganinka ne ya sa na wuce"
"Me kake nufi, ma'ana ni ne shedan din?"
"I, ai ka san ba ma ga-maciji, duk inda yake ni kam sai dai wani bigiren"
"Ka ji maqarya ci"
"Wa din?"
"Kai mana!" Sule ya juya wurin Sani "Don Allah ba kullum muna tare ba? Amma da yake ya yi niyyar sharri wai ba ma ga-maciji"
.
Musti ya yi saurin fara magana kafin Sani ya tanka "Kai ma ai cewa ka yi ina tare da shedan ko barci ba ya raba mu, na san kuwa da kai nake kullum ko barcin baya shiga tsakaninmu, yau ma abin da ya sa na guje ka, wa'azin Malam Jafar na ji wanda ya firgita ni, wallahi ranar lahira da aiki ka ji, don mafi yawancin matasa a yau sai dai Allah ya yi mana rahama, don wallahi daya daga cikinmu ya yi sakaci ya baqunci lahira yanzu ubansa zai ci! Don na lura abubuwan da ya lissafo dinnan akwai matsala, bábá rabonka da yin sadaka ko bin jam'i fa?" Sule ya fara wuri-wuri da ido, Sani ya dan daure ya fara magana "To kai me ya kaika saurara?" "Qaddara mana" inji Sule.
.
Sani ya ci gaba da cewa "Ai fa kuwa qaddara, don tsakani da Allah in har gaskiya za a fada, mutuminnan ya yi nesa da duk ayyukan ashar, ni wallahi har yau dinnan ban ga kamarsa ba, ko don iya ilimina kenan oho, mu din ne sai a hankali, koda yake wani lokacin sai dai a bar kaza kawai cikin gashinta, laifukan da dama, kuma shedan bai mutu ba, kwanaki na yi niyyar zuwa wajen karatun Shek Dahiru Bauchi, don an ce ya fi dan dama-dama, sai na tuna shi kuma yana yawan cewa ban da shan sigari, mu kuwa in za a hana mutum diban hayaqi to me aka yi kenan? A yi sha'ani dai kawai" Musti ya tuntsure da dariya " Wai an cuci na qauye ba? Shi fa farar sigari yake ma magana ba ma aljanar ba ... Sani ka tuna lokacin da aka hada wa Sule qwaya a shayi?"
.
Sule ya duqar da kai yana kashe sauran sigarin da ke hannunsa, Sani ya kalle shi cikin dariya "Ina wata kwata wace in ka karyo kwanar qofar Danbaba take yamma? Ai cewa aka yi tun daga Sabuwar kasuwa gogan naka ya falle bai zame ko'ina ba sai cikinta! Nan fa ya fara daddafa kai yana cewa " Zai fashe! Ina dan tattara shi ne" suka yi wani ihu gaba daya "Kai dan qwaya, da dan shalusho ba wanda ya fi su hauka, wai ka ji kansa ne ma yake tattarawa, kuma in kabibbiya bai ma san abin da yake yi ba"
.
Sule ya daga kai "Ai na yi alkawari ban sake dibanta wallahi, wato qwayoyin barci ne D5 na ce a hada min a ruwan shayi qwara 7, da Nescafe cokali 5 sai a zuba gishiri, shegen mai shayin naka sai ya juye 15 din gaba daya da rabin gwangwanin Nescafe, wallahi na kusa haukacewa don na kusan kwana Biyar ban san in da nake ba!" Musti ya ce "Qara min kwanaki yallaboi, makonka Uku ba ka a duniyarnan tamu, yayin da ka farfado ba a ma sallame ka ba ka lallaba ka bar asibitin, daga uwayenka har mu ba wanda bai sha wahalar neman inda kake ba, sai ma daga baya ne tsohonsa ya aika musu da kudinsu" Sule ya ce "To ai gwara ni tsaba ce kawai na sha, ku da kuka hauka ce ba tsabar ba komai fa!"
.
Sani ya sunkuyar da kansa qasa yana murmushi "Ai Musti ya jawo, yana
sane da cewa ba a zuwa fitsari a filin kuka da daddare, ni ma ban zuwa, tsautsayi ne dai ya fitar da ni a ranar, to kasan fararen kaya, masamman in aka ce maka da daddare ne, na gama fitsari kenan na miqe zan sa wando, kai ashe Musti ma ya fito bai san ina wurin ba, muna hada ido sai na ji ya qwala ihu, ni kuma ban san shi ne ba, sai ni ma na qwalla ihu na nufo shi, haba! Sai ya juya, ya ce qafa mai na ci ban ba ki ba, haka muka koma daki kowa sai ihu yake, sai da mutane suka shigo da tociloli sannan muka fahimci ai mu din ne dai!"
.
Ba ka jin komai sai dariya, Musti ya ce "Kai! Amma fa an ji kunya ranar bábá, don wallahi na kasa fitowa mu yi ido biyu da mutane da safe, don ina jinsu da daddaren suna cewa tabar shedan suka sha, ni wallahi da na ga Sani na yi zaton aljani ne, ganinsa na yi ya qara tsawo, ga kai dan tsit kamar an roqa, sannan tun farko abin yana raina, to ashe shi ma ya yi zaton aljanin ne ya biyo shi, mts! Gaskiya a yiwa kai fada, wallahi shaye-shayenan bai da wani amfani, in banda ya jajibo wa mutum baqin jini a jama'a, ga talauci, kuwa ka je yin magana da shi sai ya yi zaton abin hannunsa ka je nema, sannan mutum in ba sa'a ya yi ba wallahi haka zai tashi ba ilimin duniyar bare kuma na lahira"
.
Sule ya sake gyara zama "Ai ni zan gaya muku rashin amfaninsa, ka ji wai Ladidi qanwata, wace ni fa na sha nono na ba ta, amma da aka tashi yi mata aure hatta Sama'ila da yake qasanqasana an kira shi wajen taron, ni kuwa ba wanda ya san ma Allah ya yi ruwan tsirata a cikin qannina, tsohuwa ce ma ta dan ce a kira ni, boss ya ce a manta da ni kawai, ka san dole a dan yi wa tafiyar kwaskwarima wallahi"
.
Musti ya fara wasa da qafa kamar zai ce wani abu amma kuma ya yi shuru, sai sani ya amshe "Ni aure ma na ke nema, wani shegen munafukin ya je ya ce ina shaye-shaye, ka ji dan iskan maqaryaci, ba fa shaye-shayen da nake yi, ni ba abin da nake sha in ban da dan wiwin dinnan, sai dan shalisho, shi ma in ba kudi na samu ba ko kallonsa ba na yi, madarar sukudaye ce ma nakan dan sha sau daya a rana, ita din ma na aske ta in ba zan kwanta ba" Sule ya qyalqyale da dariya "To irin wannan hade-hade ba dole a ga aljani cikin dare ba!".
Daga, Muhammad Alkasim