.
Nan suka yi wub gaba daya suka miqe za su canza wuri, don rana ta riski in da suke zaune, Mari ta nuna musu wani wuri da yake dan nesa da maza "Ka ji ta sai ka ce wata baiwar Allah, ni na san ba don Allah kike gudun maza ba" in ji Jummai, Mari ta ja ta tsaya tana hararar ta, Amatu ta sa hannunta a bayanta tana tura ta kadan-kadan "Ke sai ka ce ba ki san halin mutuniyar ta ki ba? Ba wace za ta gaya miki halinta, ke da ita Alu ce da lamjaye, kullum kuna tare"
.
Mari ta fara magana cikin fushi "Bar ta kawai, wai mun hadu da ke ne fa take nuna kamar ita wata ta Allah ce, wallahi in kin san ma ina yin wani abu to tare muke yi, don ko'ina tare muke shiga mu fita tare, ban da wani abu da nake yi ni kadai sai zani gida, ita kuma hostel" Jummai ta qyalqyale da dariya ta miqe "Bara na shiga loo, ina dawowa yanzu, wace kuma ta yi gulmata Allah ya isa! Don wasu jira suke ki ba da baya a bude shafinki, duk na san komai" Suka dan yi murmushi, ai kuwa tana juyawa kan ta tafi Mari ta kalli Amatu tana cewa "Kin ga Jummai? Wallahi samarinta sun fi nawa yawa, kawai dai an dan fi ganin nawa ne a sarari"
.
Jummai ta dawo ta zauna "Na ma fasa tafiya, na ga shedan yana son ya bude tasha a nan, su waye samarin na wa? Ca nake JY ne kawai BY Bello? Ke kuwa fa, ni wallahi yanzu in kina so sai a kasa kowa ya kwashe" Amatu ta yi dariya "Ato ai gwara dai ku tona wa kanku asiri daga qarshe ku ne da jin kunya, tun da na san ko kun yi fada yanzu dan anjima tare za a ganku" Mari ta sami wuri ta rashe, "In bari ku gani na sami wurin hutawa, ku kuwa in ta so ku fi bishiyoyi tsayuwa"
.
Jummai ta dubi Amatu "Wato kin gane ko? Samarin yanzu ne sai a hankali, daga fara karatuna zuwa yau, shekarata ta qarshe kenan, samarina Goma Uku, ciki har da malamai, na fesbuk da na zahiri, da gayu da 'yan iskan zahiri da na boye, ba wanda ban gani ba a matsayin masoyi, a qarshe dai duka manufar guda daya ce, da wahala ki iya tantance mai qaunarki sabo da Allah, kowa ya fito zai nuna miki cewa shi na gari ne, wani ma har wa'azi yake yi, ga fara'a irin ta su 'yan kabu-kabu daga nesa, sai kun fara alaqa ki fahimci ko shedan bai kai shi barna ba, ni mutum ba zai ce yana so na na wulaqanta shi ba, amma duk wani mai son mace sabo da Allah to ya bi ta gidansu, shi ya sa na ga gaskiyar maganarki ta dazu, duk qaunar da wani da namiji zai yi min in har ba zai so uwayena su san alaqarmu ba to wallahi na yafe, komai qaunar da ya ce yana yi min kar ki qara kar ki rage qarya yake yi"
.
Kafin Amatu ta yi magana har Mari ta amshe "Kin ji munafuka!" Tana kallon Amatu tana qaryata Jummai "Waye bai san alaqarta da JY ba? Wallahi ko wancan mai awarar ta gaban hostel dinku kika tambaya za ta ce miki JY ne saurayinta" ta juyo ta kalli Jummai "Haba wa Jummai mune fa idon gari, ko mu ne za a wa rufa-rufa kuma? Ok na ma sani, tabbas kina tsoron Amatu ne, ba damuwa ci gaba kawai".
.
Amatu ta rasa abin da za ta ce, don tana tsoron ta yi magana su fara daga murya a tsakaninsu, don Mari ba ruwanta tana iya auka wa kowa da bala'i, wannan ba sabon abu ba ne, ko watan jiya ma ta kusa fada da wani namiji "JY ba ya jin magana ne" in ji Mari "Na gaya masa ba ma sau daya ba cewa ba ni da lokacinsa, ya qi ji, ba shakka mun jima da shi kuma ga alama yana so na, but we are mature now, me zai hana shi zuwa gidanmu in da gaske yake yi? Ya ce ba zai iya turo iyayensa yanzu ba sabo da bai kammala karatu ba, na ce ba komai to ya hada ni da 'yan uwansa mata, ya ce wai za su yi masa cinne a gida, duk dai na yarda a tafi a kan ba ni da wayau din, na ce to ya zo gidanmu, ya ce wai me zai ce wa iyayena in suka tambaye shi? Ke da ganinsa kin san ba shi da gaskiya, wallahi yaudarata kawai yake yi, ko kuwa akwai wani abin da yake nema"
.
Amatu ta dan yi murmushi ta ce "Kar fa maganar Mariya ta zama gaskiya, ko ni na sha ganinku tare, don har dibo miki ruwa yake yi" Amatu ta sosa wa Mari in da yake mata qaiqayi "Ai ta ma mai da shi bawa, last week da muka je gidansu na ce mu yi wanka a can tun da muna da matsalar ruwa a makaranta, cewa ta yi wai JY yana aikin mene da ba zai debo ba? Wayata ta karba ta kalallame shi da baki, gogan na ki kafin mu isa har ya kai mata qofar daki, to ni wa na taba yi wa haka? Koda yake ni ba a hostel nake kwana ba amma ina sane da cewa in wahalar da gayu ne wallahi ba macen da ba ta yi, ko ke ma din Amatu" Jummai dai ba ta tanka ba, sai in wannan yana magana ta kalle shi, in wancan ya amsa ta juya kai gare shi.
.
"To ke ki yi magana mana" in ji Amatu, Jummai ta ce "Mhn! To me zan ce? Mutum ne ka nuna masa duk gaskiyar da za ka iya ya kasa fahimta to me za ka yi? If you cannot convince him just confuse him, wasu in ba haka kika yi da su ba wallahi ba za su taba fahimtarki ba" "Kin ji ko?" In ji Mari, tana tambayar Amatu, Amatu ta duqar da kanta qasa don tana dan jin nauyin jummai "Samarin yanzu ababan tsoro ne, in ma kina tunanin kina da wayau ne, matuqar ba ki yin shawara da uwayenki wallahi sun kai ma tuni sun baro"
"Ban fahimci manufarki ba" in ji Jummai, Amatu dai bata iya kallonta ba "Namiji zai iya nuna miki cewa shi dolo ne ya yi ta bin ki a hankali, komai kike so ya ba ki da rawar jiki, amma wallahi shaho ne, muminin kare ne ma, lokacin da zai fizgi kayansa ba za ki taba iya sani ba, na ga wadan da suka fada tarkon maza barkatai, wasu sun sha da qyar, wasu sai dai a yi musu jaje, bakin alqalami ya bushe"
Daga Muhammad Alkasim