.
To da yake Amatu ba ta tanka mata ba sai ta wuce zuwa ban daki, ranta a bace, dama haka abin yake, in mutum ya shirya fada da kai fita harkarsa don kar ku lalace gaba daya, shurunta kuwa ya yi amfani, can dai ta dawo da sauri ta dauki jakarta "Har ina manta wa da jakata" in ji Mari, haka suka yi watsi da ita ba wanda ya ce mata "Ci kanki!" dan lokaci kadan Jummai ta daga kai tana kallon Amatu "Sai fa kin yi haquri da Mari, don ko dan giya bai kai ta buguwa ba, yanzu sai ta birkice miki ki rasa kanta, ko da yake ku take wa wannan shaqiyancin, amma ni ai ina, tunku ya san shurin da yake wa kashi"
.
Amatu ta dan yi quta "Q!" tana duban in da Mari ta shiga "To wai me ya sa mu ne kadai take wa wannan cin kashin, ke kuwa duk abin da kika yi mata ba ta iya ce miki komai? Ni fa ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni, wannan ai shi ne na dan Fulani: Mai raha yi raharka, mai dariya ka ga na ka! Ke da ba da labari, ni da daukan laifi" Jummai ta dan daki Amatu kadan a cinya ta ce "Ba ni nake raka ta wurin samarinta ba? Ba abin da ban sani ba nata, in na tubure mata dole za ta nemi sulhu"
.
Har Amatu ta yunqura za ta miqe sai kuma ta dawo ta zauna "Ban tambaye ki ba? Dazu kin dauko zancen Mr KB sai kika yanke, ca nake shi ne kadai ya tsane ta a duk cikin lakcarorinmu? Kullum fa zaginsa take yi in muna hira, kuma shi ma da ta fara masa rashin kunya zai kore ta daga ajin" "Wa din?" "Mr KB mana" "A ganinki?" "A ganin kowa ma, don ko jiya na ji an ce ya kore ta" Jummai ta qyalqyale da dariya, ta dan waiwaya ta kalli hanya, sannan ta saukar da murya ta ce "Kar fa ki yarda wani ya ji ... wallahi soyayyarsu suke sha!"
.
"Ban gane ba!" In ji Amatu, Jummai ta ce "To ki lura, ai dazu na gaya miki irin shigar banzan da take yi a duk ranar lakcarsa" "A! Ba raina shi ta yi ba? Ca nake rashin kunya take yi masa, shi kuma yana qoqarin yi mata magana, shi ya sa take haka don ta baqanta masa rai, ba ta san kuma saba wa mahalicci take yi ba" Amatu kenan, "Mhn" in ji Jummai "A fahimtarku ba? Amma gaskiya da walakin domin in ya kore ta cewa yake yi ta jira shi a ofis, to mu dauka ba hira suke yi ba, kin taba ganin ta fadi ko da test dinsa bare exam? Me ya sa bai taba kai qararta wurin wani ba?"
.
Amatu ta yi shuru tana tunani, kamar dai tana taro abubuwan da suka riqa faruwa a baya, Jummai ta ci gaba da cewa "Ko exam dinsa za a yi ita take fara fita, kuma bata taba samun qasa da B ba, amma ita da ba ta da note dinsa kuma ba ta cika zama period dinsa ba ya za a yi ta riqa cin jarabawarsa? Ni ba na zargin ta da komai, ko na ce suna yin wani abu, amma ba shakka irin siyasar duniya dinnan ce, ki ji qasa da qasa suna zagin juna har ana qona tuta da zanga-zanga da atisaye kala daban-daban amma har ki gama rayuwarki ba za ki taba ganin yaqi a tsakaninsu ba, sun fi kowa zaman lafiya.
.
Amatu ta dan yi murmushi ta ce " Ok rigimar Isra'ila da Iran ba? Kullum cikin zagin juna ne, amma alaqarsu ta fi ta kowa gyaruwa, to amma in ta yi wari za mu ji... ya maganar Yakubu? Tun da muka tattauna sau daya ban sake ganinsa ba!" Jummai ta dan kalle ta da gefen ido tana dariya, "Hajia Amatu, ya sami shiga ne na yi masa albishir?" Ta ba ta amsa cikin sauri "No kin gane ko? Ba na son ya ga kamar na wulaqanta shi ne kin gane? Ban bude masa fuskata ba, wato ni da ina so ya zo gidanmu ne tukun albashi ma san juna a can, kin ga irin wannan wurin kin gane ko? Sai ya zama kamar kamar..."
.
Jummai ta katse ta da cewa "Kin gane ko?" Amatu ta kai mata duka, Jummai ta sa hannu ta tare "Ni dai kun mai da ni jaka, wannan ta tafka wancan ma haka, to yanzu me kike so a yi? Kin gane ko?" Amatu ta dan yi dariya "A'a in da zai zo gidanmu sai mu tattauna sosai yadda za mu san juna, kin ga nan gaskiya galibin alaqoqin da ake yi ba su cika qarko ba, samarin yanzu sun faya son kansu"
.
Wannan hirar dai dole ta yanke tun da Mari ta dawo "Na wanke kwalliyar don masharranci ya ji dadin qararwa" in ji ta, Amatu ta dan yi murmushi "Mari manta da Jummannan kawai, ita fa in ba ta tsokani mutum ba hankalinta ba kwanciya yake ba, ko da yake wani lokacin takan yi qoqarin fadin gaskiya, Mari yaushe za ki ziyarce ni?" "Mhn, akwai wani wa'azin qasan ne?"
.
Suka qyalqyale da dariya "Allah ya shirye ki Mari, ni ba wa'azi zan yi miki ba, ji na yi kikan ziyarci Jummai, ban da wannan ma mu kullum muna tare amma qafarki ba ta taba taka gidanmu ba, kin san kuwa zumunci bai ce haka ba" Mari ta sami wuri kusa da qarshen benci ta zauna tana kallon wani wuri.
.
"Ku ai ba zuwa gidan malamai ne matsala ba, a riqa maka kallon wani fandararre, shi ne problem din, gaskiya in dai kina so ki zo gidanmu mu kowa na mu ne ba ruwanmu da rayuwar wani, kowa ta kansa yake yi"
.
"Wai yaushe muke da class ne? Ni fa na gaji da zamannan wallahi" maganar Jummai kenan, tana yatsina fuska kamar wace take hira da saurayi, ta wuce sa'a daya tana taunar cungam guda daya, sai tauna shi take yana qara, wani sa'in ma ta huro shi kamar balam-balan, Amatu ta ce ko kin manta ne? AA ba zai so ba sai qarfe Hudu daidai, kin san shi dan qa'ida ne, sai dai abin da yake burge ni da shi ba ya fita sai ya kammala darasinsa kuma zai yi wahala ka ga an qosa ya fita, kowa yana son koyarwarsa"
.
"Ko dai...." In ji Mari Amatu ta kalle ta "Ba za ki gane ba, ni ai kin san principles dina a kwalejinnan ba kowa nake kulawa ba, duk da na san cewa ba wai na fi kowa kyau ne ko mahaifina wane ba, amma kin san wani abu?" Mari ta zuba mata ido, amma ba ta tamka mata ba, ita kuwa ta ci gaba da magana "Mu dinnan da kike gani kamar kwano ne da aka zuba wani abu a ciki ana so a sayar, in kina so a ga darajarsa to ki rufe shi, wanda suka san shi za su tabbatar qudaje ba su bata shi ba, wadan da kuma ba su san shi ba za ki ga ba abin da suke so sai su ga me ke cikinsa har da ake rufewa?"
Daga, Muhammad Alkasim
Title :
Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 5
Description : . To da yake Amatu ba ta tanka mata ba sai ta wuce zuwa ban daki, ranta a bace, dama haka abin yake, in mutum ya shirya fada da kai fita h...
Rating :
5