.
Mari ta bude tsakiyar littafinta ta yago falle daya ta zauna a kai, suka ci gaba da dariya "Wa ya gaya miki Borno Gabas take?" In ji Jummai, ta juya wajen Zainab ta ci gaba da magana "Da ma na gaya miki ki fita harkarta da kanta za ta zauna, don ko 'yammazan yanzu kin ga suna juriyar tsayuwa ne? Ita ba soja ba, ba wata 'yar sanda ko mai gadi ba, to meye na qona energy?"
.
Da kamar Mari ba za ta tanka ba amma sai ta gajiya ta bara "Ku ba ku sani ba ne, wani dan dolo ne da ya dame ni kwana Biyunnan nake buya masa, yanzu ma na tsaya ne don in na gan sa na ce masa yanzu zan wuce don kar ya bata min rai" "To ke in da gaske kike yi ki jefar da kashi mana ki huta da quda" in ji Zainab "Ni fa a ganina mu muke jawo wa kanmu duk wannan matsalolin, soyayya ba a yin ta dole, in ina son ka, ina son ka period, in kuma na ga alama kai dan dauki bi su ne tuni zan tura banza black list wallahi kuwa"
.
Jummai sai dariya take yi, sabo da saninta da cewa Mari da Zainab duk da cewa kullum suna tare juna, kuma komai tare ake yi, amma zai yi wahala ba a qare da rigima ba, don Mari tana ganin cewa Zainab tana qoqarin tura mata ra'ayoyinta ne a dole, abin kuwa da ta rantse kan cewa ba zai taba faruwa ba kenan "To ke wa zai zo wurinki kin zama ninja?" In ji Mari, ganin maganar ba ta yi wa Zainab dadi ba sai Jummai ta yi maza ta shigo "A'a ke ma Mari ya kamata ki riqa taunawa kafin ki fadi, Zainab tana da samarinta ko ni na san guda Biyu, wani ma ta hannuna ya biyo wai na taimake shi, ga shi dan ustaz irinta kyakkyawa kuwa wallahi, na san kuma zai yi wahala ta ce ba ta son sa"
.
Zainab ta kalli Mari cikin fushi "Ni wallahi ban damu ba don ta ce ban da samari, don kuwa a wannan zamanin sai dai mace ba ta kama kanta ba saurayi sai wanda ta zaba, amma ban jin dadi mutum ya riqa yi wa addini izgili, ni ban ce dole ki sanya niqabi ba don haka ki iya harshenki, wasa da addini hatsari ne, kina iya saba wa mahaliccinki a kansa"
.
Mari ta yi wata quta "Q!" Tana hararar Zainab, Jummai ta ce "Koda yake
ni ma shigar tawa ga ta ga irinta amma gaskiya ta dan fi ta Mari, tun da ba na fita ba mayafi, warara ne amma akwai rufin asiri, ita kuwa wannan shigar ma mai kyau ce, amma ke kin ga ta jiya kuwa?" Zainab ba ta ce komai ba, Mari ya wub ta ba ta amsa "A taimaki shedan ba?" "Wallahi kuwa shi ta yi, don har qirjinta ya dan fito, muna tsaye a qofar kantin ice cream din can jiya muka ga wani abin dariya"
.
Mari ta yi qoqarin toshe wa Jummai baki da hannunta, amma sai ta ture hannun ta miqe tsaye tana cewa "Wallahi sai na fada" ta dawo kusa da Zainab "kin gani ko Amatu?" Sunan da suke kiranta da shi kenan, cikakken sunan Amatullahi, wato Baiwar Allah "Na farko dai" in ji Jummai "Mari ta caba ado na gani da qarawa, don wallahi ta yi kyau ko ni na fada, sannan ta sa wasu damammun kaya, ai kin san su wasu pink colour haka, in kika lura ta fi saka su ranar Talata da yake Mr KB yana da lekca"
.
Mari ta harare ta, amma Jummai ta kau da kanta kamar ba ta gani ba "To mun fito dan break haka sai ga wasu gayu sun nufo mu, ita kuwa Mari ta sha wani baqin gilashi irin no respect dinnan qatoto, yadda kika ga na shugaban qasannan" "Shegiya masharranciya" in ji Mari, zagi a bakinta kamar 'yar gambara, sai dai idan mutum ya lura da irin tarbiyyar da ta taso a ciki ba zai yi mamaki ba, haka dai ta bi Jummai da gudu, ita kuwa miqe a Saba'in ta zagayo ta dawo gaban Amatu tana dariya "To abin dariyar shi ne, su gayun kansu yana kanmu, sai kallon Mari suke yi, to ashe ke daganan wani mai tallan fima-fimai a keke shi ma kallonta yake yi, wallahi haka suka yi karo gammm! Da me keken da wanda aka daka haka duk suka watse a qasa" Mari ta qyalqyale da dariya tana qoqarin sake bin Jummai.
.
"A qarshe dai haka suka miqe suna qoqarin ba junansu haquri, da suka
fahimci cewa dukansu dodo guda suke wa tsafi sai suka tafa kawai suna wa juna dariya"in ji Jummai, Mari ta harare ta "J Baby, ba zan sake fita break tare da ke ba tun da na ga abin na ki har da sharri ne" Jummai ta ce "Ki rantse da Allah ba haka aka yi ba, wallahi ba sharri na yi mata ba, don har Amir dinmu sun gargade ta jiya, shi ya sa ta dan yi shiga mai kyau yau, cewa ya yi wallahi in ta sake shugowa haka sai sun yi mata tsirara kamar haihuwar uwarta!
.
Kin san kuwa za su aika don wadannan mutanen jin kansu suke yi kamar wasu waliyyai" Amatu ta dan yi gyaran murya ta ce "Maganar gaskiya Mariya kina buqatar gyara, don ke karan kanki kin san abin da kike yi ba daidai ba ne, in ba haka ba me ya sa kike canja shiga in kin baro gida?" Jummai ta amshe "Kuma in za ta koma gida sai ta sake canjawa ba? Wallahi ko wannan kwalliyar da kike gani a ladies loo take yi, sannan za ki ce na gaya miki, in za ta koma gida takan wanke shi tsab" Amatu ta yi tsaki "Mts! Allah ya kyauta, amma gaskiya akwai gyara, duniyannan da kike gani ta ishi kowa riga da wando"
.
"Allahu Akbar!" Inji Mari "Ai da na san yau wa'azi za ki yi da na ruqo miki sadaka, amma ba damuwa next time" Amatu ta girgiza kai ta ce "Ai da ma na san ba kya son jin gaskiya, amma ki sani, cutar iyayenki kike yi, don kuwa ba su san abin da kike yi a waje ba, koda yake su ma ai ya dace su riqa bincikawa"
.
Mari ta tsaya a gabanta cikin fushi "Kin ga ba na son haka, duk abin da za mu yi a tsakanimmu ki daina sako iyayena a ciki, wallahi Zainab ki daina ganin muna girmamaki wai don ko muna kiranki Amatu ni mai iya zagewa ce mu ci uban juna! Yauwa" Amatu ta ja bakinta ta tsuke, kai ka ce ba ita ce ta yi wannan maganar ba.
Daga Muhammad Alkasim
Title :
Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 4
Description : . Mari ta bude tsakiyar littafinta ta yago falle daya ta zauna a kai, suka ci gaba da dariya "Wa ya gaya miki Borno Gabas take?"...
Rating :
5