ALLAH YA ISA BAN YAFE BA! // 3
.
"Don tsayanan" cikin tsawa "Kar ki jiqa min carpet a banza, yanzu sai ki sa dakin mutum ya kama wari, ban da rashin sanin ciwon kai duk da irin wannan katafaren hadari amma mutum ya yi zamansa a waje har ruwa ya same shi, duk da haka ya kasa fakewa ga irin wannan uban ruwa da ake shantabawa har da qanqara amma ki kamo hanya tsamo-tsamo don gobe ki kwanta min ki ce ba ki da lafiya, to wallahi na gaji da zuwa Kyamis wannan karon sai dai ubanki ya biya
kudin magani!"
.
Mari ta koma gefe guda tana rawar dari, ganin haka sai Tala ta yi wuf ta miqe, tana cewa "Amshi wannan zanin koma can gefe ki cire wadannan sai ki rataye su a wayan jikin baranda, albashi gobe a matse su" ta dawo kusa da Fatu tana cewa "Ke ai dan yau ba a masa haka, ko ni da nake da 'ya'ya maza ban taba yi musu fadan fakewa a wani wuri ba bare 'ya mace, daga irin fakewannan ce ake farke mutum, tun ma ba mace da take da hanyoyin da za a cutar da ita da dama ba"
.
Fati ta tabe baki, maganar Tala ba ta shige ta ba, ta dubi Mari da ta shigo yanzu "To wuce uwar daka ki ba mu wuri, in kuma ba zuba mana ido za ki yi ba" ta juyo kan Tala "Wannan ai ta wuce yarinya, ni fa irin tadodin tsofaffinnan ba ruwana da su, don ko tun muna 'yammata mu ba a matsa mana ba, bare kuma yanzu da wayewa ta dada bazuwa a ko ina, Mari ai ba yarinya ba ce, in ma ta yi sakaci ai jiki magayi budurci tsada ce da shi ta san haka, wace duk ta yi asararsa shi kenan har abada, ba wani abu ne da za a ce za a ga likita a kansa ba".
.
Tala dai ba ta ji dadin zancen Fatu ba, don haka ta share maganar gaba daya ta dauki littafin da ke kusa da ita tana dubawa "'Yan talla sunansa? Na ji ana ta cewa Hajiannan za ta fito da wani littafi mai matuqar mahimmanci, ana ta tallansa kafin ya fito wai shi (Dominki da Mijinki)"
.
Fatu ta waiwayo "Ok na Rabi Yusuf Maitama ko? A
gaskiya tana qoqari, da wuya ki ga ta yi littafi maras ma'ana, dubi dai wannan, ai wancan yana fitowa zan sa Mu'azzam Funtuwa ya turo min, ko wata likita sunanta Marnaf, ita ma tana da qoqari in dai abu ne na addini ... ya maganar auren malam da gaske din ne ko wasa? Don na ji maganar ta yi shuru ne"
.
Tala ta ajiye littafin gefe guda ta miqe tsaye tana gyara daurin zane "Ni ina ruwana? Ke ce amarya, in ya so ya auro Biyun ma gaba daya, na san dai ko waye ya auro dole dai ta dafa abin da zai ishe mu ni da 'ya'yana" Fatu ba ta gamsu da amsar da Tala ta ba ta ba, sai dai wannan bai baqanta mata rai ba don tana da tabbacin ita ma kishin ne gare ta, ba tsiyar da ba a kwasa ba lokacin da take amarya, kusan kullum sai an raba su dambe.
.
"Kai! Amma namiji ba dan goyo ba ne wallahi, sai ya gama kwande ka ya ce ka tsufa ya je ya dauko maka tsarar 'yarka, in ta zo ta kama daddaga maka kai ... amma ba komai ni wallahi zan iya zama da kowace shegeyar yarinya, don ba zan yarda a riqa ci min kashi a ka ba" in ji Fatu.
.
"Iye!"
"Qwarai kuwa"
"Kika ce qwarai"
"Tabbas"
"To da wa za ki yi?"
"Da kowa ma"
Fatu tana magana tana kallon fuskarta a dogon yaro "In mutum ya ce shi muganci ya sa a gaba ai kuwa shi ma ya san ba za a zauna lafiya ba"
.
Tala ta dawo ta zauna tana kallon Fatu tana dariyar qeta a ciki "Dan yayyafa mata ruwa" in jita, Fatu ta ba ta amsa "Au, ni fa na san abin da nake yi, ba wata wutar kishi da take cin zuciyata mutumin na ki ne bai da rahama a zuciyarsa ko kadan, yanzu in ban da muganci ba ki dubi yarinyannan yadda ta girma, ba don ma na tsaya sai ta gama karatu ba da yanzu an fara maganar aurenta, a zuwa yanzu kin taba ganin ya kawo wani abu wai don ya kusa aurar da ita?"
.
"Tabdijan!" In ji Tala "Ke kika san abin da yake yi? Wani namijiji ne zai nuna miki aljuhunsa? Kina ina zai rantse mana da Allah wai ba shi da ko sisi daga baya su Auwalu su ce mana sun gan shi yana cin indomie da qwai a wajen mai shayi? Ai namiji duk in da yake ki bar shi kawai"
.
Fatu ta fara fada tana daga
murya "Wallahi abin ma da rainin hankali a ciki, ta ya mutum kullun kana mana qaryar babu-babu muna haqura, sannan daga baya muji wai ka fara neman wata 'yar kucilar yarinya sa'ar 'ya'yanka? Ni wallahi ban ma san yarinyar ba ne, amma wallahi da na sa yara sun nakada mata dukan tsiya ko ma ni na tunkare ta da kaina, muga kuma me zai yi? Kulle ni zai sa a yi ko daukan mata fansa?"
.
Tala ta yi murmushi tana magana a hankali "Akwai yara fa a daki, ga Mari can ta shigo yanzu kuma kina sane, kibar wannan hirar kawai" ta miqe ta leqa waje ta kallo baranda, ta dawo ta zauna "Kin san yanzu maza ma sun lalace, su suke gulma da maqe, gogan naki yana iya fakewa da ruwannan ya tsaya a baranda yana jin
maganganummu, masamman ma namiji in ya so aure.
.
Fatu dai ba ta ce uffan ba, Tala ce take ta maganganunta ita kadai " Shawarata ki qyale shi kawai, duk bala'in da za ki yi wallahi kallon ki kawai zai yi, amma sai ya yi kayansa, ni ba wani da namiji da zai ce min wai ya yi alkawarin ba zai sake yin aure ba na yarda, wallahi ko dan sarkin Madina ne kuwa, ina ce qarshen imani dai kenan?"
.
Ban da yatsine ba abin da Fatu take yi, in dai za a tabo maganar kishiya, ko na maqwabta ta dinga fada kenan, to bare kuma a ce tata ce, Tala na yin shuru suka ji Malam Salisu yana kira, Tala ta miqe ta fita da gudu da hannu riqe da dankwali tana qoqarin sake daurawa.
Daga Muhammad Alkasim
Title :
Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3
Description : ALLAH YA ISA BAN YAFE BA! // 3 . "Don tsayanan" cikin tsawa "Kar ki jiqa min carpet a banza, yanzu sai ki sa dakin mutum ya...
Rating :
5