Bisa ga dukkan alamu Tala ba ta son fadin inda ta kalli Sunna tv din, don maigidansu ya hana kallon talabijin din 'yan Izala, duk da cewa shi kansa ya fadi qoqarin da malaman Sunna din suke yi wajen gyaran tarbiyya, jim kadan Fatu ta yi kasaqe kamar tana sauraron wani abu "Ina ji fa kamar yarannan suna yi miki mugun wasa ne a daki kar fa su fasa miki wani abin, dan yau sai a hankali" Tala dai ba ta ce komai ba, Fatu ta
jawo saqarta ta ci gaba da aiki "Ni na rasa abu guda qwaqqwara da zan yi, ni ban karanta littafinnan ba, ga saqar ta qi ci gaba, yau kusan mako Biyu kenan ina saqa wandon yaro" ta juyo ta kalli Tala da gefen ido, tana wani dan murmushi na tsokana "Ai tun da na ga kin shigo ba kya magana da kowa na san malam yana dakinki, a maimakon yadda ake ruwannan ki zauna ku sha soyayya sai kuma ki arce ki bar shi da yara, duk da ni ba malama ba ce na san dai hakan zunubi ne!"
.
"Barin mace da jahilci kuma fa ibada ne ko aikin samun lada?" In ji ta, "Na ce ki dauki littafi ki ce ya koya miki ai wannan ma mafita ce" in ji Fatu, Tala ta tuntsire da dariya ta taso ta zo gefen gado ta matsar da littafin Fatu ta zauna "Ke ban gaya miki ba!"
.
"Ba mu mu sha" in ji Fatu, Tala ta saukar da murya tana kallon qofa, kai da gani ka san gulma za a yi "Ai mai gidanki mu da shi samma kal, wallahi duhu ne kawai yake dukan duhu, ba ke kika koya min layin farko na alifun, baa'un ba? To da na je sai na ce tun da ba zai bar ni na je makaranta ba sai ya koya min, gogan na ki ya karbi littafin, ke kyace zai iya wani abu sai fada yake yi yana zazzare idanu" suka yi wata shewa gaba daya suka tafa, Fatu ta ce "A to ba damuwa in dai ya koya miki ai an gama"
.
"Ya koya min me?" In ji Tala "Cewa ya yi wai an yi asarar kudin tara, da girmana ban iya babbaqu ba, sai ya ce ina ne ban sani ba? Na nuna masa karatunmu na jiyan Jeemun, Haa'un, Khaa'un, wallahi na san bai sani ba, na mujiya kawai na yi masa, sai ya ce wai bara ya zo yana da wani a qofar gida, da yake na san kayana na bi shi ta tagar uwar daka ina hangen sa yana tambayar wani yaro!" Fatu sai yaqe take yi ta ma kasa dariya, ga bakin ya qi rufuwa, duk ta qosa ta ji yadda aka qare.
.
Tala kuwa sai labari take zubawa "Kin san sun yi kama da juna bambancin kawai na digo ne, wani a qasa, wani bai da digo, na qarshen kuma a sama, to ina jin ko dai ya manta ko kuma bai nemi a nuna masa ba, kin san namiji wani lokacin girman kai ne da shi" Fatu ta tuntsure da dariya ta kalli qofa "Kar ma su wane su ji, sai kullum a tsefe gemu a dauko wata tasbaha ana ja, in kika bibiya ba abin da yake cewa"
.
Tala ta ce "Mhn, ni dai da ya dawo ban wani kula da shi ba don na san tambayowa ya yi, to amma da ya zo sai ya tura min littafin wai: 'Ga shi nan dan wannan karatun ne ba ki iya ba, wani Kaa'un wani Jaamun!' Na ce to ya dan nuna min "Kaa'un" da "Jaamun" din sai ya daure fuska irin yadda yake yi dinnan in ya shigo ba mu gama abinci ba" suka sake sheqewa da dariya gami da shewa "Allah na gode maka, ni da ma na san haka za ta faru, ai in kika ga irin masu tsananinnan galibi a yi fatiha kurum a tashi, shekara nawa muna tare da
malam? Ke kin taba jin ya yi miki wa'azi in ba kun dan sami sabani da daddare ba?" Fatu kenan.
.
"Allah na tuba, ni ko irin
hadisannan na larabci da za ki ji maza suna karantowa ban taba ji ya yi ba sai bala'I kullum" in ji Tala, ta saukar da kanta qasa tana kallon
lallenta, ga shi nan jajawur gwanin sha'awa, "Ya ma kusa fita, bari sai gobe in za mu gidan suna zan biya ta wurin Hajiya tsohuwa na sayo lalle kin ga wannan ya tsufa" Fatu ta kalli tata qafar "Ni ba wai ina qin lalle ba ne, qafar tawa ce ta faye kamu sosai, ko na dan zizara shi daga qasa haka zai hawo sama ya bata min qafa, shi ya sa ya fita min a ka, ga gogan na ki ko kin yi ba zai ce ya yi kyau ba, m! Bara na yi shuru kar na tuna miki don na ga yau kin sako shi a gaba"
.
"Mhn" in ji ta "To ai ko na yi fushi da shi ba laifi don kuwa shi ya jawo da kansa, ni da wanne zan ji da hana ni zuwa makaranta ko da fada? Ki ji fa cewa ya yi wai ba zai yi asarar biyan kudin makaranta ba tun da yasan ko mun je ba fahimta za mu yi ba, ya ma qare ya ce wai fakewa kawai za mu riqa yi da makarantar muna satar unguwa, nan dai ya yi ta fade-fadensa, kin..." Shigowar Mari ta sa Tala ta katse maganarta suna kallon ta tsamo-tsamo.
Daga, Muhammad Alkasim
Title :
Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 2
Description : Bisa ga dukkan alamu Tala ba ta son fadin inda ta kalli Sunna tv din, don maigidansu ya hana kallon talabijin din 'yan Izala, duk da ce...
Rating :
5