.
Yanayin garin ba rana, amma sai dan karan zafi, sabo da iska ta tsaya cak ba ta ko kadawa, ga gajimare sai wucewa yake yi, wannan na shiga cikin wancan, dakuna duk sun dauki zafi a dalilin daukewar wutan lantarki tun sa'o'I Uku da suka wuce "Irin wannan yanayin da kike gani ruwa yana iya sakkowa a kowani lokaci, masamman yadda damina ta yi nisannan kin ga kusan qarfe Biyu kenan in ruwa ya tsinke sai ya raba dare bai dauke ba"
.
Maryam ta dan yi murmushi "Malamina kenan, na dai fahimci manufarka, 'yarka ce dai tana daki tun dazu, da za ka saurara za ka ji ta tana tilawar haddarta ta Madrasatu Tahfizil Qur'an, gobe Laraba za ta kai haddar" M. Lawal ya ce "Amma dai kina ganin garin ko?" Ta dan yi quta tare da daga kai sama "Q!" Ta juyo ta kalle shi "Malam irin wannan qa'idar ta ka fa ba ta yi min ba"
.
M. Lawal bai ce komai ba sai ya zuba mata ido yana kallonta "Ya za ka ce ba za ka ci abinci ba sai maqwabci ya dawo, shi da wani lokaci yakan wuce Biyu da rabi bai shiga gidansa ba? Ina ganin da ka dan sa wani abu abakinka da ya fi" "Na ji ikon Allah, yau kika fara ganin haka?" In ji shi "Ban iya cin abinci ni kadai ba, ke dai tun da kin cika qundunki shikenan"
"Wa din?"
"Ke mana"
"Q,q,q,q!"
"Me ya hana?"
"Maigida bai ci abinci ba sai kawai na yi riga-malam-masallaci? Ai tun da muke da kai ban taba cin abinci na qoshi kafin na tabbatar da qoshinka ba matuqar kana tare dani" in jita.
.
Ya ce "To mai ya sa hakan?" Ta ce "Haba dai malam! In abincin bai yi maka ba fa? In na ga ba za ka iya ci ba wallahi ko ni ba zan ci shi ba, sai na fitar da shi na sake wani, hali dai mun gode wa Allah muna da ma'aikata a gidannan da komai, amma bangaren abinci ban yarda wata ta sa min hannu ba, hatta jus din da kake sha ni nake hada kayana da kaina, malam in ka lura maigida ai maigida ne, ya za a yi na riqa wasa da abin da Allah ya damqa min a hannuna?"
.
M. Lawal ya dan yi murmushi ga alama ya ji dadin maganar, masamman yadda ta sauko qasa ta zo dab da qafafunsa ta zauna tana magana cikin sanyin murya da girmamawa, kai ko ba a gaya maka ba ka san zuciyannan tawa maqil take da dumbin qaunarka da Allah ya kwarara mata" sau da yawa ba ta iya daga kai ta kalle shi in tana magana, ba tsoronsa take yi ba tsabar kunyarsa da take ji ne, ga ta da 'ya'ya sun girma wata ma har sun fara zancen aurar da ita amma a kullum sai bude shafukan soyayya suke yi daya bayan daya, kai ka ce wadan da suka shafe shekara Arba'in ne suna soyayyar da ba a sami damar auren ba sai kwanannan,
.
Shi kansa M. Lawal bai iya zaman waje, ko ya fita bai jimawa sai ka ga ya kwano gida, hatta ita matar tasa Maryam, in dan wani sha'ani ya fitar da ita za ka ji ta fara neman hanzarin guduwa da cewa: Malam fa yana gida shi kadai, da ta fara fadin haka ba jimawa za ka neme ta ka rasa.
.
Yauwa ki ma tuna min, ya Zainab kuwa kin riqa sanya ta cikin ma'aikatan gidannan suna aiki tare?" "Qwarai kuwa" ta ba shi amsa, ya ce " Yauwa, don masu aikin cikin gidannan mataimaka ne, barinsu kuma su kadai su gama komai ba gata ne ba, dole ta saba da ayyukan gida gaba daya, ta yadda za a cire mata qiwar aiki, wannan zai taimake ta yi wa mijinta hidimar da ta da ce, zancen godiyar Allah kan ni'imar da ya yi mana tabbas gaskiya ne, amma in muka qi koya mata komai wai don taqamar muna da wadata, haqiqa mun cutar da ita"
.
Maryam ta amshe "Mhn! Su manya, ai ina tabbatar maka ba zan bari wani abu ya cutar da ita a gidan mijinta ba, tun tana yarinya qarama na sabar mata da duk wasu ayyukan gida, ban taba bari shagwaba ko qyuya sun bata min ita ba, to bare uwa-uba qazanta, tun lokacin da ka yi magana kan haka na sa suka raba aiki, yau ta wanke ban-daki, gobe ta gyara kicin, jibi ta tsaya wurin tsabtace cikin gida, dakinka da na wa kuwa ba mai gyara su ya share sai ni, ko kuma ita, wanke-wanke duk da ita ake rabawa, wani lokacin nakan hana a kai wanki don dai ita wanke duka, wannan don ta koyi yadda za ta fitar da kanta nan gaba"
.
Tana waiwayawa sai ta ga har ruwa ya fara saukowa, don haka ta miqe cikin farin ciki ta dauko abincisa ta bude masa a gabansa, ta saka masa cokali, a gefe guda kuma ga ruwan sha da salat din kabeji wanda aka hada da dafaffen qwai "Allah ya ga zuciyata" in jita "Wallahi ban son zamanka da yunwa ko kadan, ka ga ma na samu mu ci tare" ta dan yi murmushi, shi kuwa M. Lawal bai ji maganar qarshe ba, don bai mayar mata da amsa ba.
.
A maimakon haka sai ya dauko wani sabon batu ya dasa "Kuskuren da uwaye mata suke yi, masamman kuma a nan maraya, sai ki ga yaranmu mata sun girma amma ba su san aikin wahala ba, zai yi wuya ki ga sun iya wani abu, don komai yi musu ake yi, hatta ruwansha sai an debo wa wasu, shi ya sa in an yi auren ki taras ana ta samun taho mu gama, to an bar ban-daki, kicin da tsakar gida da datti, daki ba tsari ba komai, in ma abinci ta dafa sai ka ji ba dadi to an bar ta sai da ta kusa aure sannan aka fara koya mata zaman gida, wannan kuwa kuskure ne, ba ku ga mu 'ya'ya maza tun suna yara qanana muke koya musu iya riqe iyali ba?"
.
"Ai fa kuwa" in ji ta "Ga 'yar maqwabcinmunan, har nan uwarta ta zo ta roqe ni wai na bar Amatu ta je ta riqa koya mata girki, sai na ce sai ka dawo"
.
M. Lawal ya dan yi murmushi, ko ba a gaya maka ba ka san ya ji dadin maganar "Wace yarinya kenan? Kar dai wace aka yi aurenta mako Uku da suka gabata?" "Ita fa!" In jita "Sai daga baya na fahimci abin da kake nufi na koya mata ayyukan gida, tun lokacin na fara saka ta duk wadannan ayyukan, duk da cewa raina bai so hakan ba, gaskiya ko yau Amatu ta yi aure ban da shakka a kanta ta kowane bangare, dama ka ce a koya mata don kar ta auro wanda ba zai iya daukar abin da take gani a gida ba, ilai kuwa".