.
"Na ji kamar motsin yara ne, ko da yake lokacin dawowarsu bai yi ba" duk da haka ta dan tashi ta leqa, don ta tsawata musu, zuwa dan anjima ta dawo "Ashe yaran maqwabta ne, wani lokaci haka za ka ji suna ta bubbuga min tagar uwar daka, duk yadda ka yi da su ko sun tafi sai sun dawo" M. Lawal ya daga qafa daya ya dora a kan dayar, ya mimmiqe sosai "To sai mu gode wa wanda ya ba mu su, wasu da dama suna son ganin irin wannan qiriniyar amma ba su samu ba... ina Zainab take ba qarfe Daya take dawowa ranar Laraba ba? Yanzu kusan Daya da rabi ba ta dawo ba!"
.
"Ta dawo tun dazu, ta ce tana son ta je wurin kakanninta ne na ce kar ta dade, don idan ka dawo za ka tambaye ta, amma na tabbata yanzu za ka gan ta don ta san ka kusa dawowa, ko ma ba don haka ba tana da aikin makaranta sosai, ga shi sun kusa fara jarabawar qarshe" in ji Maryam, M. Lawal ya kau da kai yana kallon talabijin "Ina ganin da zarar ta kammala jarabawannan za ta wuce dakinta kowa ya huta, ita ma ta sami hutu ko dan kadan"
.
An dan sami lokaci ba wanda ya ce komai, sai zuwa anjima Maryam ta sunkuyar da kanta ta fara magana cikin sassanyar murya "Na yi mamaki da na ga Amatu ta tsayar da Siddiq, na zaci suna ta samun sabani ne, ko da yake dan zamani abin duk da ya ce ka yi masa ka yi kawai don ku zauna lafiya" M. Lawal ya girgiza kai "A'a ba dai duk abin da ya ce ba, in dai aka ga ya dace sai a yi masa, abin da ya sa ma na amshi maganarsa don na san tarbiyar gidansu ne, Annabi SAW ya ce: Wanda kuka amince da addininsa da dabi'unsa ku aura masa, shi kam na san ubansa tun muna matasa ana yawon wa'azin qasa, dattijo ne ba ko shakka, ko da yake bai da abin hannu kamar yadda kika ce amma ya iya riqon gida, kuma yana da rufin asiri, mu kuma abin da muke nema kenan, mutum nawa suke da halin amma kullum iyalinsu cikin qunci?"
.
Maryam ko dago kai ba ta yi ba bare ta ce wani abu, M Lawal kadai yake maganarsa "Tunaninmu a yau 'ya ta auri mai kudi, alhali ya kamata mu san cewa kudi ba su ne kawai hutu ba, akwai buqatar abubuwa da dama kafin shika-shikan hutun su gama kammaluwa, za a iya samun mai kudi amma bai iya yalwata iyalinsa ta wurin abinci ko tufafin sakawa, wasu da dama ba sa iya zaman gida bare a sa rai da gamsar da iyalinsu ta fuskar shimfida, zancen tarbiyar yara wannan ko maganarsa ba a yi, ke dai tun da an sami wanda take so, ko na ce suke son juna addu'a kawai ta kamace su, bare kuma na ga kamar shi ma irinta ne, don har nan ya same ni"
.
Maryam ta dago kanta "O! Zamani mai dauke-dauke! In ba haka ba ya za a yi ya iya fuskantarka da kansa ya ce ka ba shi dama ya yi magana da 'yarka? Mu a zamaninmu wannan ai rashin kunya ne, ko shi ya isa ya sa a qi aurar masa da ita, don me ba zai fara turo iyayensa ba, sai kuma ya kamo hanya tinqis-tinqis wai ya zo neman aure! Wannan ai rashin kunya ne"
.
"To!" In ji shi "Ni dai da yake na ga babba ne, kuma na san gidansu da komai na sa na ce masa ya turo mahaifansa tukun mu yi magana, amma zancen fara zuwansa me za mu ce? Yaran yanzu gaskiya sun yi karatun da mu ba mu yi ba, wasu har qasar manzo sun je sun kwashe shekaru a can karatun kawai suke yi, in gaskiya za mu bi sai mu riqa duba hujjojinsu in sun tafi daidai da maganar Allah ko hadisi shi kenan sai mu dauka, ba wai mu ce al'adarmu ko iyayemmu ba haka suka yi ba, sabanin haka kuwa duk son zuciya ne, matuqar ba mu da hujjojin da za su kawar da nasu"
.
Maryam ta bude baki, ga alama mamaki ne ya cika ta "Malam kake fadin haka? Uwayemmu da ka suka yi nasu addinin? Balle ma wannan maganar aure da nemansa muke yi ba sallah da sauran shika-shikan muslunci ba, kuma ka lura, wasu abubuwan da muke ji suna faruwa a wasu wurare yau ga su a gidanka a dakinka ma ba yadda za ka yi sai dai ka zuba wa sarautar Allah ido" ta miqe ta bude firinji ta dauko jus din kankana ta miqa masa "Jiya Amatu ta karanto mana yadda ake hadawa a fesbuk, wai tana da wata qawa, malama Sadeeya Lawal Abubakar, ita take koyar da mata wasu 'yan hade-haden, gaskiya tana qoqari, wannan kam ya yi dadi" ta miqa masa sannan ta dauki rimot ta rage qarar talabijin din.
.
M. Lawal ya kurba "Maganar gaskiya zan cen uwayemmu sun yi kaza wajen neman aure bai ma taso ba, matuqar dai akwai dalili daga shari'a, da cewa kika yi ya kamata uwayensa ne za su nema masa damar yin magana da yariya ba shi ba, sai na ce gaskiya hakan ya fi mutunci, kuma ya fi dacewa, kin ga wannan maganar da kika kawo da kowa zai dauki zafi haka za a iya bata wani halalin dominsa, koda yake ni kaina da a ce ban san yaron da irin tarbiyar da ya samu ba, ba zan ba shi dama ba sai na kammala duk wani bincike, to amma yanzu ai an gama komai, ke ma murna ya kamata ki yi, don 'yarki ta sami kintsattse mabiyi koyarwar manzon rahama, Allah ya dada daidaita tsakaninsu amin"
.
Maryam ta dan yi murmushi "Ai kuwa sun hadu sun dace, don na ga ita ma Amatun akwai qoqari, ni ban taba jin ka ce mu sa niqabi ba, amma ita kam in ba da shi ba da wahala ka ga ta fita, ni na rasa yadda aka yi ya ga fuskarta har ya ji yana son ta" M. Lawal dai bai ce komai ba, ya ajiye kofin jus dinsa a kan teburi ya ci gaba da kallon talabijin, Maryam kuwa ta ci gaba da cewa "Ko da yake ana cewa mu mata kamar dafaffen qwai ne, in yana cikin qwansonsa a rufe ya fi daraja don kowa yana da tabbacin cewa ba mummunan abin da ya same shi, amma da zarar an bare ya fito fili, ko da dan tsattsagewa ya yi wurin dahuwa sai ka ga mutane suna zagaye shi ba sa son su dauka, to Allah dai ya taimake mu kan tarbiyyarsu, gaskiya dan yau sai a hankali"