Malam Lawal ya shige turakarsa, Maryam ta bi shi riqe da jaka, tana tafiya tana tambayarsa "Gaskiya wannan jakar ta yi nauyi, me ka zubo mana ne? Ni dai na san ba haka na shirya ta ba" Malam Lawal bai ko juyo ba, qoqarinsa kawai ya bude daki ya shiga "Me kike tsammani za ki samu a ciki, Hajia garaje?" Ta dan yi dariya ta dada kusantarsa, ga turare na tashi, ga alama ba ta fesa ba sai da ta ji isowarsa, ta ce "Na sani ko kayan auren wannan 'yar ka fara sayowa? Tun da ta fara hira da saurayi kai ma ka san yanzu za a fara maganar aure, in dai ba jira kake sai sun zo neman a sa rana ba" ta dan yi dariya alamar tsokana.
.
Malam Lawal ya yi murmushi ya tura qofa "Ku dai mata ba ruwanku da wata matsala, iyakacinku ku ce: Siyo kaza, ba ka siyo kaza ba, iyakar turancin kenan, zancen nawa yake? Ya za a sami kudin? Duk ba matsalarku ba ce ... wace magana kike min dazu, na ce ki bari sai na dawo tukun?" Bai tsaya sauraron amsa ba, yana shiga ya bude daki ya tube riga ya rataye ta a kan hanga "O! Damina ce fa amma kin ji yadda gari ya juya gaba daya ya koma rani, Allah kenan Almusawwiru, sai ya juya abubuwansa yadda ya ga dama, a lokacin da yake so, ba tare da wata halitta ta yi masa katsalandan ba, ya Ubangiji ka tausaya mana, kar ka duba ayyukan masu zagin tsarkakan bayinka"
.
Maryam ta rufe jakar bayan ta gama bincikawa, "Ai ma duk littafai ne, ni da na zaci irin ayabar shekaran jiya dinnan ce ka kuma kawo mana ... To bara na barka ka huta, in ta so na dawo mu kammala maganar dazu, na ga kamar a gajiye kake, M.Lawal ya kallo ta, wa ya gaya miki? Yi maganarki yanzu, don ina farkawa ficewa zan yi, ke ma kin san haka" ta dan yi murmushi kamar yadda ta saba, ta saukar da murya, yadda ka san mata masu wayau sukan yi a lokacin da suke magana da mazajensu, "Yauwa" in jita "Dama ina so ne mu tattauna maganar Amatu, don na ga kamar kai har yanzu kallon yarinya kake mata, a zahiri yaran yanzu sun dan wuce duk inda uwayensu suke tsammani"
.
"Wa kike magana, Zainab?"
"I"
"Me kuma ya faru?"
"To ai kai ne kamar ba ka fahimci tana girma ba"
M. Lawal ya dawo kan wata doguwar kujerar da ya saba zama, ya fasa kallon talabijin din da ya kunna, a qa'idarsa kullum ya shigo gida sai ya kalli Sunna tv, nan dai ya zuba mata ido yana jin me kuma take so ta ce "Malam!" In jita "Shi wannan yaron haka zai riqa ratso mana cikin gida kullum muna ganinsa? Ina ganin ba gwara a riqa bude musu qofa ta waje can suna zancensu ba? Amma hakan ai akwai takura gaskiya, ba wai ta bangarena kawai ba shi ma ba zai iya sakewa da ita sosai ba, ita ma na lura ba ta iya sakar masa su yi zancensu, ga yara dan binni-binni sun kutso daki, wani sa'in ma ba sa ko yi musu sallama, sai nake ganin kamar in da a waje suke da zai fi, ba dai dare ne ba bare kuma a ji musu tsoron wani abu"
.
M. Lawal ya yi dariya "Shi kenan?" In ji shi, Maryam ba ta ce komai ba don ta san halinsa, tana qara wani abu maganar za ta iya zama babba, qarshe ta sha fada, sau da yawa in bai yi niyyar yin abu ba ko gardama ba ya yi, da an gaya masa sai ya ce to, shi kenan ya shashantar da ita, masamman ma zancen Amatu, yana yawan sanya ido a duk kai-komonta "To ka yi haquri in shawarar ba ta yi maka ba, ni da ina gani kamar wai haka din zai fi ne, duk da na san dan yau sai a hankali" ta gama jera littafan a kanta ta dawo ta zauna.
M. Lawal ya kalle ta ya ci gaba da cewa "To wanne kike son a yi?" Ba ta tanka masa ba, don ta san magana daya rak ta yi masa, ita ce maganar Amatu, ga shi kuma yana neman ta zabi daya, da ya ga dai kamar ba za ta ce komai ba sai ya ci gaba da cewa "In kina ganin a bar ta ta riqa fita waje hiran ne ai shi kenan in ta so ma sai ki ce ta gaya masa ya riqa tahowa da daddaren, ina ganin wannan ya fi rashin takura!"
.
Babu ko shakka maganar Maryam ta zama gaskiya, duk da cewa a cikin tsanaki da sassanyar murya yake magana, babu ko shakka ransa a bace yake, takan fahimci fushinsa ko da kuwa dariya yake, sau da yawa in irin wannan abu ya faru takan yanke duk wata hirar da take tsakaninsu, in dai ba shi ne ya so a ci gaba ba, haka dai ya ci gaba da fadarsa "In ban da halin mace ba, a dakinnan shekara Uku kenan da suka gabata, kike ce min 'ya'yan Maizana duk sun zubar da ciki su Biyun din gaba daya"
.
Ya dauko kofi ya dan zuba shayi ya fara sha "Ban tambaye ki ba kike gaya min irin wannan sakacin, kika ce hirarrakin daren ne kuwa duk suka samu, ta ya mutum ba zai kula da diyarsa ba? Koda yake na yarda da tarbiyyar da na ba wa Zainab amma gyara kayanka ai ba zai taba zama sauke mu raba ba" Maryam dai ba ta iya dago kanta ba, magana take yi cikin sassanyar murya "Ai na ce ka yi haquri, ka san mu mata mantuwa ce da mu, da ma ni gani na yi babba kamarsa ai ya wuce wasa, bare kuma ga ilimi, shi kansa da yana son su fita wajen ai da ya nemi hakan a wurinta, ganin hakan ya sa nake tunanin ya sami duk wata natsuwa ko a qofar gidan ne ma dai in sha Allahu ba wani abin da zai faru"
.
M. Lawal ya yi shuru kamar ba zai ce komai ba, sai dai ya yi gajin haquri ya bara "Ko hakan ma dai ba hujja ba ne, ki dai fadi abin da kike wa tsoro, ko an gaya miki wani abu ne game da shi?" Maryam ta dan yi murmushi "Malam kenan, kana dai roron maganar da za ka yi fada ne a kai, amma ai kana fara magana na fahimci na yi kuskure, kuma na ba ka haquri.
.
To amma ganin kamar ransa a bace sai ta ci gaba da rarrashinsa a dabarce kamar yadda ta saba "Malam ba yabon kai ba, zamana da kai kawai ya ishi mutum ya san rayuwar duniya, mun dai gode wa Allah" M. Lawal ya dan yi dariya "Har kin tuna min zuwa zancen da na yi kina bera, kika fara yi min kuka a cikin gida!" Maryam ta dan kawar da kai tana dariya "Haba Malam abin shekara Talatin har da Biyu kana dawo da shi? Ko da yake kai ba ka san dalili ba ne, a lokacin Izala ba ta gama bayyana sosai haka ba, ni ji na yi: Ya za a ce ina qarama kuma za a riqa zuwa min zance? Sannan ka san yaranta, qawayena suka riqa zuga ni wai a gaban iyayena za a riqa zance da ni?" Lawal ya yi murmushi "Su A'ishah Tsakuwa ko?" Ta girgiza kai "Su Balaraba, Habiba da Hadiza, ka san sun dan girme ni kadan sun rigani yin saurayi"
.
Bayan kamar dan lokaci kadan sai M. Lawal ya kunna talabijin ya ci gaba da cewa "Ai ko ba don halin dan yau ba barinsu a wajennan matsala ce babba, gwara dai su riqajin cewa ana bibiyar duk abin da suke ciki, zancen rashin sakewa kuwa ai hakan ake so, daga ranar da ya kai ta dakinsa wace sakewa kuma za su buqata? Shugowarsa cikin gidannan tana da fa'idoji da dama, na farko: Akwai tsaro sosai ko a muslunce ma, na Biyu kuma: Ita kanta yarinyar mutuntata aka yi, tun da a dakin mahaifinta take zance da saurayi, sannan shi kuma dole ya riqa lura da tsawon lokacin da ya zauna da ita, da tazarar wurin da za su zauna, da irin kalaman da zai riqa furtawa, da ma ranakun da zai riqa zuwa, duk da kin ce kullum yake zuwa, amma na lura sau Biyu yake zuwa a mako, ba ma kowani mako ba"
.
Maryam ta ce "Haka ne, to ai shi kenan an gama, ka san ban taba aurar da yarinya ba, ita ce ta farko, in muka yi ido Biyu da shi ne sai na ji wata iriyar kunya ta rufe ni"
"Shi fa?"
"Shi ma haka"
"To ya daina zuwa?"
"Ina fa! To ai malam qwaqwalwarmu ba iri guda take da taku ba, don shi kam gaskiya ba laifi yaro ne mai ladabi da biyayya ga ganin girman mutane"
.
M. Lawal ya juyo yana kallonta yana dariya "Su wance masu surukai, to ai da yaron da kike cewa yana shugo miki gida da Zainab din duk 'ya'yanki ne, daga ranar da aka daura musu aure ya zama muharraminki har abada, yanzu ke kina yi masa kallon yaronki ne, shi kuma yana yi miki kallon mahaifiya, ke dai mu roqi Allah ya dada ba mu damar tarbiyantar da su kawai, amma barin yara balagaggu su mannu da juna a waje, cikin duhun dare, ga shaidan yana ta kai komo gaskiya ba qaramin abu ba ne, komai natsuwar yarinya da iliminta ba ta kai shedan ba, don wallahi ban da dadewar da ya yi a duniya, da a ce shi gaula ne, da bai tara irin wannan jama'ar ba, kawai mu sanya musu ido, kuma raka su da addu'a.