.
Ba abin da kake ji sai zuban ruwa kamar da bakin qwarya, garin ya yi tsit ko qarar mota ba a ji, sai dai qanqarar da take dukan kwanoni da qofofin jama'a, galibi idan damina ta yi nisa akan iya samun ruwa ba iska ko mummunan hadari, ga dai Fatu can a gefe guda tana karanta wani littafi na Rabi Yusuf Maitama mai suna ('Yan talla), "Amma kina ganin malam zai iya dawowa cikin ruwannan kuwa?" Tana tambayar Tala, sai dai ba wata amsa da ta samu, don haka ita ma ta yi watsi da ita, sau da yawa Tala in ta yi zurfi cikin tunani ba ta kula kowa, don ko magana ba ta ji bare ta ba da amsa.
.
Cikin dan qaramin lokaci sai aka ji wata qatuwar tsawa
mai gigita dan adam, nan take Tala ta razana har ta matsa daga jikin tagar da take leqen zubar qanqaran, nan fa Fatu ta tuntsure da dariya "Ina ruwan na dankama manzonka hoge, ba ka jin kira sai jifa, nan kika bar ni ni kadai kika fada kogin soyayya ko magana ba kya ji, kin ga in ba ki ji maganata ba ai dole kya ji ta mahalicci ko?" "Mhn" in ji Tala "Fatu ni raba ni da murdadden mijinnan na ki, shi komai na sa daban, duk
in da maza suka yi Gabas, shi sai dai ki isko shi Yamma, wallahi duk na
rasa yadda zan 6ullo masa" kafin Fatu ta ba ta amsa har ta koma kan kujerarta ta ci gaba da kallon zuban ruwanta.
.
Fatu ta ajiye saqarta kusa da wani dogon-yaro wanda take kwalliya da shi, ta kunna fitilar qwai tana cewa "Yau dai ruwan ba iska, na san zuwa anjima kadan za mu sami wuta... to amma ke mai zai sa ba za ki fita sha'aninsa ba tun da ya ce ba da shi ba?
.
Ni wallahi na karanci maza, nacin da muke musu don su ba mu wani abu shi ya sa suke dada jin dadi suna qara fadin hanci, in aka daka tasu sai mutum ya bushe sabo da wahala buqatarsa ba ta biya ba, kwanaki da na ce ya ba ni jari ai hanawa ya yi, amma da na fita harkarsa ba ki ga na samu ba har da ma ban haquri?" Tala ta yi wata quta "Q! Wa zai daka ta ki da malam?
Ai ke kuna dasawa, in ma ba ki roqa ba ba ki za a yi"
.
"Aaaa! Ai haka za ki ce?"
"I mana ai ke ma kin san gaskiya"
Fatu ta dan yi murmushi, kamar ba ta fahimci maganar Tala ba, ta ci gaba da cewa "Malam ai cinnaka ne, in don maganar makarantar mata ce ko ni na yi na gaji amma shuru kamar an shuka dusa, in da za ki lura malam fa karatunnan ne ba ya so, na ce za mu shiga ta Dangoggo ya ce wai wani karatun Allah ne za a tara matan mutane da daddare wani qato yana koyar da su? Na ce to ya saka mu a ta Malam gajere don na ga shi da rana ake yi, amma gogan na ki sai ya ce wai bai amince da malamin ba!"
.
Tala ta tube takalmin qafar
hagu ta dora qafar a wani qaramin gado da yake dab da taga ta ce "Ni wannan qanzon kuregen na gaji da shi, ba ya son barimmu ne kawai amma in da gaske yake yi shi mai kishi ne don me ya hana mu sanya niqabi? Ke dai in mutum ya so ya yi kuka ko ruwa ya dan diga masa cewa zai yi ya karya shi, gwara ke ma kin dan yi boko mu da ba wan ba wan me za mu ce?
.
" In ji karatun dan kama ba?" Fatu ta fadi tana dariya, Tala ta ci gaba da maganarta "Ni wallahi tun da na ji karatun Kabiru Gwanbennan jikina ya yi sanyi, don abubuwa Talatin dinnan da ya lissafo a Sunna tv ba na tsammanin da wanda ba ma yin sa a cikin gidannan, sai dai Allah kawai ya yi mana rahama"
.
Fatu ta fashe da dari ta daki cinya "Allah na gode maka yau su Tala hankali ya tashi, in dai wannan wa'azin ne ki sha kuruminki kawai ai an ce wasu malaman sun cika tsanani, kinanan wani kuma zai ce miki ba laifi ya halasta, ni wallahi in ma ya hana ruwansa, don in mun yi karatun shi zai sami sauqi, kar ma ya bari, amma a wani gida kika kalli Sunna tv din?" "M! Bar maganar a nan, bari ki gani" ta miqe.
Daga Muhammad Alkasim
Title :
Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 1
Description : . Ba abin da kake ji sai zuban ruwa kamar da bakin qwarya, garin ya yi tsit ko qarar mota ba a ji, sai dai qanqarar da take dukan kwanoni ...
Rating :
5