.
CIKAKKEN LABARINA. labarin humaira kenan?? ya tambayi kansa, yayi saurin gyara zamansa ya karasa karanta abinda aka rubuta a kasa, labarin farin ciki na gajeren lokaci daya jawo bakin ciki na har abada. Labari me tsuma zuciya da sanya shauki. Labari me tare da tarin Al'ajabi. Ahmad bude shafin gaba ya fara karanta labarin humaira daya dade yana burin yikakken SUNANA Aisha humaira, sunan mahaifina Alhaji Isma'il ishak daya daga cikin hamshakai kuma fitattun yan kasuwa a africa. Haifaffiyar garin kano unguwar hausawa......kuma Ya kasance sananne wanda sunansa ba boyayye bane sbd Allah yayi arziki na gaban kwatance, hakan yasa ya tara mutane masu yawa matuka kama daga ma'aikata, abokai da yan maula daban daban dake kaiwa dake nanike dashi a kowanne lokaci. Ni kadai ce wacce mahaifina ya mallaka a matsayin Y'A hakan yasa na taso cikin gata, so, kauna da kulawa. Tun daga yarintata ba abinda nake nema in rasa, komai nace ina so sai an mallaka min ban taba yin kukan rashin wani abu ba. a kowanne lokaci mahaifina na nuna min ba abinda bazan samu ba sai dai idan bana so, tun dai bana yarda har na yarda domin kwakwalwata ta gaza tunano min abinda zan nema dukiyar mahaifina ta gaza samar min shi. Saboda son da mahaifina keyi min yasa kowa ke nan-nan dani da nuna kulawarsa akaina don ya samu abinda yake so a wurinsa, duk kuwa wanda ya kuskura ya taba ni to kashinsa ya bushe a wurin mahaifina. Matsala daya dana tashi da ita itace na raina mutani da nayi musamman talakawa da marasa galihu, gashi ko kadan bana son kula mutane bare na girmamasu sbd bana ganin kan kowa da gashi. ban damu na shiga harkar kowa ba kuma mafi yawa idan aka shiga tawa raine ke baci, hatta kawaye ban damu nayi ba sbd yadda nake jin nafi kowa. Ba wadanda nafi rainawa na taka yadda raina ke so irin yan aikin gidanmu kuma dole su kalleni don suna tabani sun san hukuncinsu kora ne don haka dole suka kyaleni nake cin karena ba babbaka, mutum dake da karfin taka min birki a wasu lokutan itace mahaifiyata da nake kira da MUM.
.
Wani lokacin idan na dauko rashin mutuncin daya wuce hankali takan kwabe ni wadda ita kadai ke yin hakan domin mahaifina komai nayi dai dai ne a wurinsa.
.
********* ************ *********
.
Tun ina da shekaru hudu aka saka ni a nursery ta musamman ba kamar saura ba, me tsadan gaske ce da kudin da ake biya a shekara daya kawai ya isa a dauki nauyin karatun yayan talakawa guda uku tun daga primary har zuwa jami'a. Direrba aka tanada don kaini kuma ya daukoni, idan ya kaini baya tafiya har sai an tashi ya dawo dani. Shekaru biyu kacal nayi aka matsar dani izuwa hamshakiyar makarantar da duk wani dan me akwai ke burin ganinsa a cikinta, wadda tun daga sunanta kasan tafi karfin talaka koma uban talaka, makarantar nada kyan yanayin data burgeni har yakai ban taba korafi da ita ba. Ina daya daga cikin dalibai abin alfahari a makarantar sbd kwakwalwata ta saurin gane abu wanda hakan ke kara min girman kai matuka. Duk da cewa makarantar kowa naji da kansa domin ba dan talaka a cikinta kowa ka gani daga gidan arziki yake, amma fa nawa girman kan yafi na kowa domin ko kawa daya ban yi ba sbd a ganina duk babu me aji dai dai dani. Sai dana shafe shekaru goma sha biyu anan primary & secondary, da shekaruna 18 na gama ta.
.
A dai- dai wannan lokacinne kuma kari kan da ZUNZURUTUN KYAU ya kara bayyana, Wohoho!!!!!!!!!!! Kai idan ka ganni sai ka rantse da Allah ni balarabiya ce domin kadan zubi na bana hausawa bane, kamar yadda ake fada kuma nake gasgatawa a duk sanda na dubi kaina babu kamata a wannan zamanin indai fagen kyau ne. Nasha jawo accident idan ana tafiya dani a mota ban daga glass ba, nasha jawowa mutane karo da juna idan ina tafiya, duk wadda ke ji da kanta idan ta ganni sai ta fashe da kuka don taga karshen kyau, wasu fashewa suke da kuka suna cewa ina ma su sami 1/10 kyawu na. Kwalliya ma bata wani dameni ba sbd a cewata idan kyau bai cika bane ake neman kwalliya ta karasa cikashi amma idan kyau ya cika babu bukatar hakan. Mafi yawa harkar sharwoliya bata dameni ba koda a shigata nakanyi kokari na rufe jikina, mafi yawa kayan da nafi sawa ba wadanda basu kamata bane sbd ni ako yaushe na yarda na tsare mutuncina kuma a ko'ina. Bayan na kammala secondary a nigeria mahaifina ya nema min admission amma fa a oxford university dake kasar england, nayi murna sosai sbd ina da buri na bar kasata izuwa wata musamman kasashen turai. Da yake harka ce ta kudi nan da nan komai ya kammala kuma aka saka ranar tafiyata domin fara degree na farko a fannin kimiyar tattalin arziki wato (economics) da kuma lissafi. Ana gobe zan tafi ne bayan komai ya gama shiryuwa zaune nake nasa tafkekiyar televission din dake manne a jikin bango nesa kadan dani a cikin katafaren falon alfarma na gidanmu, cikin kwanciyar hankali nake kallon ba wani abu dake damuna. kaso 99% na hankali ya tafi ga kallon film din na DHOOM yadda jarumin film din ke raina hankalin yan sanda da dabaru daban daban, wucewar da daya daga cikin yan aikin falon tayi ta gabana yasa banga karashen abinda ya faru ba abinda ya tunzira ni kenan wulakancina ya motsa na kira sunanta da karfi.
.
HANNE!! Ta juyo da sauri tana kyarma, nace " Zo nan" Ta fara matsowa a hankali a hankali na daka mata tsawa nace " gidan uwar wa zaki je??" Tace " uhm... haji..ya ce ta kira...ni. ". Nace harareta nace " kuma don ubanki shine ta gabana zaki wuce ko? Duk nan ba hanya bace??" Tayi shiru kawai tana makyarkyata bata ankara ba na zabga mata mari hade da fadin " ba tambayarki nake ba??". Karfin marin sai daya sa ta fadi kasa lokaci guda ta zarce da kuka." Ahmad ya kauda littafin daga karantawar da yake yace " Lallai wannan wulakanci har na siyarwa kina dashi ya gyara kwanciyarsa tare da mayar da idonsa ya dora da karantawa.......
.
Karar data kwalla ne ya jawo hankalin mum ta fito da sauri tana tambayar lafiya kuwa?? Ta tsaya kawai tasamu a gaba tana kallo hade da hararata cikin takaici.......
Title :
Al'ajabi Part 5
Description : . CIKAKKEN LABARINA. labarin humaira kenan?? ya tambayi kansa, yayi saurin gyara zamansa ya karasa karanta abinda aka rubuta a kasa, labar...
Rating :
5