HUMAIRA!!!
Momi ta kira sunanta ta juyo a hnkl, Zo nan.
Momin ta fada.
Ta tako a hnkl tazo gbnta.
Zauna!! momi Ta sake fada tare da yin nuni da hannunta izuwa kusa da ita.
ba tare da gardamar komai ba humaira ta zauna.
Momi tamkar me jin nauyin yin maganar abnd take son fada sai data jima sannan tace “Humaira!!“
ta kira sunanta tare da dorawa da fadin “Na fahimci rashin farin ciki da nuna bakin cikinki karara a lkcn da aka ce daddynki zai samu lfy, nasan dalilinki nayin hakan amma dole zan gaya miki hakan da kikai bai dace ba.
Koba komai mahaifinki ne baki da tamkarsa a duniya kuma baki isa ki canzashi ko kankareshi daga wannan matsayin ba har abada.
Na yarda muma munyi kuskure akan abnd mukayi kuma kema yakamata ace kin dade da fahimtar hakan kuma kinyi mana uzuri, wlh mahaifinki nasonki kuma yana kaunarki ma2ka zan shaidi hkn a ko‘ina, abnd yayi yana ganin gata ne don ya rabaki da wahala sai dai bai sani ba ya rabaki da farin cikinki na har abada ne.
Kiyi hakuri humaira ki maida komai wurin Allah ina da yakinin ba haka kawai abnd ya faru ya faru ba lallai akwai wata izinah da Allah zai nuna mana, amma ki daina dauka cewa mahaifinki makiyinki ne kinji.“
wasu fararen hawaye suka yi saurin gangarowa ta kuma2n humaira ta grgz kai ckn kasa da murya tace “Bawai bana son daddy ko rayuwarsa bane wlh nafi son inga ya rayu fiye da kowa sbd bana son a nunani a kirani marainiya har karshen rayuwata, amma momi faru..k... duk sanda na 2na bansan inda yake ba ya mutu ko yana da rai??
A dadi yake ko a wahala??
Nakanji na tsani duniya da duk abnd ke cknta, lkt a asibiti ya bamu tbbcn akwai yakinin daddy zai warke yaci gaba da rayuwa ckn walwala da nishadi, inama kuma ace akwai wanda zai bani tbbcn faruk na raye kuma yana rayuwa ckn farin ciki da nishadi???
Dazan samu lbrn hakan kawai ya wadatar dani amma babu.“
gudun hawayen nata ya karu.
Momi ta kauda kai tayi saurin mayar da kwallar dake neman kwararowa daga idanunta, tana tausayawa humaira ma2ka.
Ta dafa kafarta tace “Nayi miki alkawarin daga sanda mahaifinki ya dawo to duk inda faruk yake a fadin duniya sai an nemoshi ma2kar dai yana da rai, koda nawa kuma za‘a kashe akan hakan.“
Humaira tayi saurin hada hannayenta ckn na momi ckn sheshsheka tace “Don Allah ku taimakeni momi... ina son na kara ganin faruk koda sau daya ne tak a rayu..wata..“
Ta zarce da kuka tare da kwantar da kanta bisa cinyoyin momi wadda ta shiga Rarrashinta.
****** ********************** ******
BAYAN WATA DAYA.
****** ********************** ******
A mafi yawancin lkt mutane kan nuna maka soyayya a zahiri har su rika kokarin wuce makadi da rawa wajen nuna sunfi kaunarka fiye da kowa a duniya, amma idan da wata masifa zata afka maka sune na farko wajen rige-rigen gudunka.
Duk da irin dukiyar Alh. isma‘il da yadda mutane da yawa ke cin gajiyarta ta bangarori da dama, da abokai hamshakai fitattu da yake takama dasu amma ya gane kuransa sanda ya shiga rashin lfyr data haddasa kowa ya guje shi, duk wanda ya ziyarceshi sau daya baya mararin ya koma musamman idan yaga matakan da ake dauka kafin shiga inda yake.
Lallai gskyr masu magana da suka ce harka ta duniya da me rai kuma me lfy ake yinta, shikam ya yarda da hakan don ya gani da idanunsa.
byn shafe wata guda curr!! da yayi a kasar finland ckn nasara aka kuma sa ranar dawowarsa, nan fa yaransa, ma‘aikatansa da duk wanda keda alaka ta kusa kota nesa dashi aka fara dafifin isa airport don taroshi.
**Misalin karfe 11:30 na safe fitaccen filin sauka da tashin jiragen saman AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT din yadau harama tare da daukar shiri na musamman daga ma‘aikatansa wadanda 2ni suka fara tbbtr da shiri ga inda katafaren jirgi saukar farko a yau zai sauka.
Ba tare da jimawa ba kuwa makeken jirgin na EUROPE AIRLINE ya dira a tirbar kasa daga sararin samaniyar daya shafe a awanni yana shawagi, daya byn daya mutanen jirgin suka fara fitowa yayinda jami‘ai suka hau kan aikin don tbbtr da cewa ba wani bata gari daya shigo ckn jrgn.
Ckn wadanda ke fitowar harda Alhaji isma‘il, byn komai ya kammalu sun gama gaisawa da mutanen dake tsaye suna dakon fitowar tashi ne kuma jerin gwanon tsala-tsalan motocin y‘an tarbar tasa suka fice daga airport din tare da darewa bisa kwalta suka nufo gdnsa.
Ya warke sarai tamkar bashi ba tamkar kuma bazai taba dawowa haka ba, sukan dan taba hira kadan da wdnd ke tare dashi a motar msmmn idan yaga wani abu da ya canja masa a hanyar da suke bi.
Min2na klln suka kwashe suka iso gdn nasa tafkeken gate din gdn ya bude jerin motocin suka wuce ciki a jere kmr yadda suka taho.
Ckn min2na biyu kacal alh. isma‘il yayi godiya ya sallami kowa da kowa duk suka watse, shi kadai ya juya ya shige ckn gdn nasa.
*MINTUNA TALATIN DA DAWOWARSA*
Zaune yake bisa daya daga ckn kujerun dake zagaye da makeken tebirin dake zagaye da kayan abnc kala-kala, Ya dukufa akansa ckn annashuwa.
Hajiya na tsaye bisa kansa tana tsiyaya masa juices a kofi ya dago kai tare da cewa “wai yaushe rabona da cin abnc irin wannan harna manta.“
Kada dai kace can turai din abncnsu ba dadi.
Momi ta fada sanda ta juya ga plask dake kusa da ita.
Ya hadiye lomar dake bakinsa yadanyi dariya yace “hmm.. wai turawa!! wadannan abncnsu ai jagwalgwalo ne kawai, banda dole madai... amma abcnsu ba wani ciyuwa yake ba.“
hajiya ta zauna ckn murmushi tace “To da fatan dai an dawo lfy??
yadan gyara zama yace “alhmdllh!! tfy gashi tayi kyau sosai, saura kuma cuta daya daban samu waraka ba har yanzu kuma ta yiwu har abada.
...Na sani abu ne mawuyaci idan maganin cutar zai samu, gsky nayi kuskure ma2ka da har na kyamaci mu2m me karamci da mu2nci akan wata larura sai gashi ni naci karo da wadda tafi ta. Ina ma ace zan.....“
Isowar da humaira tayi wajen tare da dafa daya daga ckn kujerun wajen ta ari murmushi ta yafa a fuskarta, daddy ya dago tare da dakatawa da cin abncn.
Humaira tace “You are wellcome my dad.“ Daddy yace “my daughter yanzu nake shirin tambayarki ashe kina ckn gdn ma.“ Ina nan daddy ai banji shigowarka ba sai danaji hira tayi yawa...“
Ya katseta da cewa “Eh mana gata nan tasani a gaba sai zuba muke,“ Suka danyi shiru nadan lkc daddy ya bita da kll yace “Ya 2nanin faruk kuma???“
Lkc guda fuskarta ta fara sauyawa daga murmushin data kakala a baya, a hankali kuma hawaye suka fara ciko idonta har izuwa sanda suka gangaro bisa kumatunta.
Ta juya da sauri tabar wurin.
Daddy ya ture abncn dake gbnsa tare da dafe kansa yace “wai ba abnd ya ragu game da ita??“
Sai dai abnd ya karu.
Momi ta fada. Daddy ya grgz kai tare da cewa “gsky hajiya mun cuci yarinyar nan, ban taba zaton abin nan zai zama haka ba,“ yakai karshen maganar yana me grgz kai tare da yin ajiyar zuciya.
Tunanina kawai yaushe ne zan dawo mata da farin ciki??
Tayi dariya ta gaske bata karfin hali ba??
Yaushene walwalarta zata dawo kmr yadda take 2n asali??
Domin idan har bamuyi taimaketa da hakan ba zuciyarta ba zata taba yafe mana ba ko ta daina kllnmu a wadanda suka kawo karshen farin cikin rayuwarta wanda ni kuma bana son hakan, ina so ko byn raina tayi alfaharin cewa ni mahaifinta ne, amma ta yaya??“
Momi taci gaba da klln inda idanunta suke kmr me yin nazarin wani abu jim kadan tace “Hakan na iya yiwuwa idan da rabon zai yiwu, muna da damar da zamu iya yi mata hakan ta hanyoyi da dama saura kuma mubarwa Allah yayi zabinsa.“ Daddy ya gyada kai tare da cewa “A yadda nake ji a shirye nake na kashe ko nawa ne don dawo da farin cikin y‘ata, sai dai bansani a ina FARUK yake??
Tsorona ace ya mutu don hkn na nufin dorewar bakin ckn y‘ata har abada.“
Insha-Allahu ma bai mutu ba yana nan da ransa kuma zamu sameshi na tbbtr shima duk inda yake tunaninsa yana nan shima, ka cgb da cin abncnka yana wucewa fa.
Ta fada sanda ta mike ta cgb da shirya kayan dake ajiye bisa kayataccen faffadan tebirin, yadan dago daga dafe kan da yayi “Au ni harna manta wlh.“
Ya fada sanda ya jawo plate din daya ture dazu.
Byn dan lkc ya dago kai tare da cewa “Yauwa idan an jima da daddare zamu je AMK hospital dukkanmu.“
Ta dago kai da sauri da cewa “Baka gaji da kwanciya a gadon nasu ba kenan??“
Yayi dariya yace “Allah ya tsaremu da kwanciyar gadon nan, kinsan dole sun cncnci jinjina ta musamman kuma bata baki kawai ba....“
Yauwa dama ban gaya maka ba, jin dadi da farin ckn dana shiga sanda naji lbrn yadda akai bansan sanda na bawa su hukumar asibitin ten millions ba sbd muma yadda akayi mana ayiwa wasu.“
Ya mayar da kansa ga plate din dake gbnsa tare da cewa “Kin kyauta ma2ka da haka, amma akwai wadanda nake son zanyiwa kyauta ta bajinta sannan kuma ina bukatar a hada ni da masu gidauniyar nan.“
Momi tace “FISABILILLAH FOUNDATION!! ance fa basa bukatar asansu ko ayi musu godiya bare a basu tallafi, duk abnd sukeyi don Allah ne kuma suna da yakinin sunfi karfin hakan, ni a yadda nake gani ko su waye ma amma ba kananan mutane bane suna da arziki na wuce misali.“
Nima ina tsammanin hakan amma ina so naga waye??
wacece??
ko kuma su waye??
Ina sha‘awar ace nima an hada gwiwa dani wajen aikata kyawawan ayyuka irin wadannan.“
hajiya tayi murmushi tare da juyawa izuwa dan karamin firjin dake ajiye nesa kadan da inda suke.
Hakan nada ma2kar kyau kuma tunani ne me kyau kayi dama a kllm duk abnd ya faru ga mu2m ilimi yake karawa indai yana da hnkli, mafi kyawun dukiya itace wadda ake sadaukar da ita ga wadanda basu da hali, ake taimakon masu bukata kuma ake amfani da ita wajen saukakawa wadanda ke ckn matsi.“
Hira ckn nutsuwa taci gaba da gudana a tsakaninsu.
**************************
sai Misalin karfe 7:30 na dare ne tsaleliyar motarsu kirar mercedez (G. compressor) ke keta shimfidaddiyar kwaltar da hasken fitula ya gaurayeta tamkar rana, ko‘ina ka kalla mutane ne keta harkokinsu a ko‘ina ba tare da fargabar cewa dare ya tawo ba.
Su uku ne sai direba cikon na hudunsu, kallo daya zakayi musu koda kuwa daga wajene ka hangi motarsu akwai alamar arziki yaji ya wadacesu.
A hnkl direban ya karya kan motar ya sadata da inda aka tanada don yin parking na motoci byn da suka iso, jim kadan Alhaji isma‘il tare da hajiyarsa suka fito sai humaira data fito ta dayar kofar suka zagayo suka jera suka nufi ciki.
Tfy kadan sukayi suka iso ga tafkeken ofishin oga kwata-kwata, ba tare da wani jinkiri ba suka danna kai don kuwa ansan da zuwansu, ganinsu keda wuya ya mike tare da fadin “you are wellcome Ya hajj, suka gaisa ckn grmamawa.
Daddy yace “kaga yadda Allah yayi damu kuma.“
farin lukutin mu2min wanda fuskarsa ke cike da annashuwa yace
“Alhmdllh!! naji dadin hkn ma2ka, lallai wato alhaji... amma dai bismillah ku zauna ko!! bari a kawo muku dan abin sha.“
A‘ah ai ka barshi ma kawai me girma M.D da yake ba lallai mu wani jima ba, zuwa kawai mukai mu jaddada godiya da abnd akai mana, gsky wato idan akwai wani award ma kun cancanceshi a wurina.“
M.D din yayi dariya yace “ai ko ba award aikin mune hakan ba kuma akanka muka fara dawainiyar shigewa gaba a fita waje ayi masa aiki ba munyi da yawa, ai mu burinmu duk wani patient namu muga ya sami waraka koma a ina ne, kai!! naji dadi sosai wlh.“
Ya fada yana me binsu da kll.
Shiru yadan gudana tsakaninsu jim kadan Alhaji isma‘il yace “Ah me grm M.D gaisuwa da rokon iri nazo, ina so a hada ni da shugabannin gidauniyar nan fuska da fuska idan hali.“
Yayi saurin grgz kai tare da cewa “hmm... alhaj kafin kai mutane da yawa sunyi yunkurin hakan amma baya samuwa sbd su basa bukatar asansu ba kuma na zaton zasu bada damar a hadu dasu, don haka ba zaka taba sanin kosu waye ba har abada.“
kosuwaye da wannan gagarumin taimako..
Muhadu dasafe INSHA ALLAH..!
Dongin yanda lbrin xeqarike..!
ILALLIQA'a