****** ************
Jikinsa baya motsi tamkar gawa, an killaceshi a inda ba kowa akalla tazarar meter 300 da inda wasu mutanen suke.
Shakar numfashi ma sai da kundun robar oxygen yake yi, ba wanda ke iya shiga inda yake sai da tsauraran matakan kariya gudun kamuwa da cutarsa ta alakakai. Yana mawuyacin hali ma2ka da gaske, munyi iya kokarinmu akansa ta hanyar amfani da dukiya ta wuce misali amma a banza, mun karyata asibitoci masu yawa da manyan likitoci masu yawa amma duk inda muka je ba abnd yake sauyawa daga abnd likitocin farko suka fada mana.
Dole tasa daga karshe muka hakura muka dawo dashi nan AMK TEACHING HOSPITAL inda muka guda 2n farko, abnd kawai lktcn suka gaya mana shine cutarsa sabuwar ce har yanzu masana na duniya bincike sukeyi akanta, da zarar an samu ingantacciyar hanyar maganceta zasu sanar damu domin sunsan kudi ba matsalarmu bane ko nawa ne zamu iya kashewa kai tsaye.
Sai dai rashin lfyr daddy zai wuya ya tash....“
Kuka ya kwace mata wanda ya haddasa ta kasa karasa dogon zancen data dauko.
Ahmad ya grgz kai tare da cewa “wato humaira duk wanda ke korafi akan yawan damuwarki to baisan tarihinki bane, Ashe wannan ma na daya daga cikin wani yanki na damuwarki??
Humaira tace “bazan ce maka A‘A ba amma magana ta gsky ban wani damu da halin da daddy na ke ciki ba sbd shine ya jawa kansa koma meye, sun rufe ido sanda suke da dama sun sakawa wanda yayi musu alheri da sharri.
Sbd kawai wata jarabta da Allah yayi masa gashi kuma shi ya kamu da wadda tafi ta faruk din, halin da daddy ke ciki a matsayin skyy na daukeshi.
Bazan manta sanda faruk ke fadawa daddy cewa ‘Na tafi kmr yadda kake so amma ka sani idan wai kayi haka ne don ka samu farin ciki to ba zaka samu ba, kuma ka saurari taka UKUBAR don dole sai tazo....
domin guguwar kaddarar data 2nkaro ba wanda zata bari.‘
Allah sarki gsky faruk BAWAN ALLAH ne gashi dai duk abubuwan daya fada suna ta bayyana, dalili daya ne kawai yasa nake son daddy ya warke, sbd na kalli ckn idanunsa snd zanyi masa wata tambaya guda daya tak!!
Amma badon haka ba ya.....“
Ahmad yayi saurin katseta sanda tare da grgz kai sanda ya fahimci abnd take son fada, ya bita da kallo zuwa can yace “bai kamata kice haka ba mahaifinki ne fa!!
Koba komai yakamata yaci darajar wannan, duk dan adam ka iya aikata kuskure a rayuwarsa.
Na tbbtr shi kansa ya dade dayin dana-sanin akan abnd yayi, abnd yakamata kiyi yanzu kawai shine kiyi masa addu‘ar samun sauki.
Sannan kuma humaira ki rage yawan damuwa da 2nanin da kikeyi sbd ba komai zasu haifar miki ba face matsala babba, wasu lktn sai kin manta rywr baya kafin ki iya shimfida sabuwar rayuwa.“
Humaira ta gyara zamanta tare da mayar da kanta izuwa inda take fuskanta tace “Nagode da shawarar daka bani,“ ta juyo ta kalleshi tare da cewa “amma ka sani bazan taba iya cire tunanin Faruk a ckn zuciyata ba dashi zan mutu na koma kabarina.“
Humaira ta riga tayi nisa ba zata ji kira ba.
Ahmad ya fada a zcyrsa lkc guda ya mike tare da duban agogon hannunsa yace “yamma na dada yi bari na tafi, nagode sosai humaira da kasancewata mu2m na farko da kika bawa dama nasan abubuwa da yawa game da ke.“
Humaira ta dago kai tare da cewa “bari na kira maka momi kuyi sallama mana!!“
Ahmad ya grgz kai dai-dai sanda yadan taka gaba kadan yace “A‘A basai ma kin kirata ba idan ta fito ki fada mata na tafi.
Nagode.“
Ya karasa fada tare da dunkule hannunsa a kirjinsa ya juya ya fice.
Ta mike tare da komawa kan kujera ta kwanta, hafsat ta shigo ta dauke farantin juices data kawo.
Humaira na daga kwancen take canja tashar da take kallo da remote din dake hannunta yanayin da momi ta fito dashi yasata dakatawa tare da tambayar lfy kuwa momi??
Ta karaso jknta a sanyaye tace “daga Asibitine can inda daddynki yake aka kirani wai ana bukatar ganinmu da gaggawa, anya....“
Humaira ta cgb da harkar gbnta tare da cewa “meye ai bazai wuce kudi suke bukata ba wadancan sun kare ko kuma sun gaji da ajiyarsa anan zasu bukaci a daukeshi akaishi wani wurin.“
Momi tayi shiru tana me klln humaira kmr tahau kanta da duka, can tace “wai ke wace irin mu2m ce??
mahaifin naki na ckn hali irin wnnn amma bakya nuna wata dmwrk akai ko?
To ki shiga hnklnk wlh.
Kuma ki shirya zamu tafi yanzu,“ Ta juya izuwa ciki.
Humaira ta dago kai tare da cewa “Tare dani??“
Momi tayi saurin juyowa a fusace da fadin “Eh don ubanki, ko ba zaki bane??“.
Humaira ta mayar da kanta kawai tare da cewa “Allah ya wuci zuciyarki“.
Tayi tsaki ta juya izuwa ciki.
*Mintuna ashirin kacal suka kwashe suka fito daga gdn, zundumemiyar mota kirar Toyota PRADO suka hau direban ya tuka su suka bar harabar katafaren gdn nasu suka hau titin dazai sadasu da asibitin.
Momi duk ta rude sai salati kawai takeyi fatanta kawai Allah yasa ba mutuwa yayi ba.
Zaiyi wuya idan lfy a irin kiran da aka yi mata.
Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un.
Abnd take ta maimaitawa kenan.
Humaira kuwa a zahiri nuna tayi ko a jknta kmr yadda ta saba yi, kalle-kallenta kawai take.
A haka har suka iso harabar tafkeken asibitin kwararrun, ta ko‘ina mutanene ke shiga da fita wasu da marasa lfy wadanda ke iya iya shiga da kansu da wadanda ake dauke dasu, grmnsa ya wuce yadda ido ka iya hango karshensa.
Kll daya zaka yiwa asibitin kasan ya wuce tsarar karami ko matsakaicin asibiti sai ka kirashi mafi kurewar girma.
Kwararrun ma‘aikatane kawai ke kaiwa da komowa duk ta inda ka ratsa, asibitin AMINU KANO TEACHING HOSPITAL kenan daya daga ckn mafiya girma, shahara da kwarewa a fadin africa.
A hankali momi da humaira ke ratsa sashe-sashe na asibitin izuwa sashen da nasu patient din yake, ofis din da zasu je don jin halin da ake ciki.
Akan hanya suna gaf da shiga wani jami‘i ya taresu “inane kuna zuwa??“
Ya tambaya ckn dagulalliyar hausarsa.
Momi tayi saurin cewa patient dinmu ne a sashen an kiramu ana nemanmu.“
Mu2min ya grgz kai tare da cewa “No baku da kowa anan yanzu an dauke kowa daga nan, babu wani patient naku.“
Momi najin haka ta dafe kai tare da cewa “shikenan ya mutu sun daukeshi muje mutuware kawai, zata sulale kasa humaira ta tarota tabi jikin humaira izuwa kasa ta zarce da kuka ALHAJI ya tafi, innalillahi wa inna ilaihir raji‘un...
Abinda take nanatawa kenan 2n ckn kuka me tsanani, dan katon mutumin dake tsaye ya dubesu tare da cewa “Alaji??
which Alaji??
Kuna nufi me cutar nan daya dade anan??
Humaira ta dago kai tare da cewa “Eh..Ehh shi.“
Ya daga kansa tare da cewa “wannan ba mutuwa yayi ba.“
Momi da humaira sukayi saurin dago kai kukan da momi keyi ya tsaya, To yana ina??
Meya faru??
Momi ta tambaya.
Ehh! an fita dashi anan wurin.
Ya fada.
Me yasa to??
Humaira ta sake tambayarsa.
Ya dauke kai yace “Oho!! bana nan don a tambayeni kuje ofishi ku tambayesu mana.“
Momi tayi saurin mikewa suka koma da baya izuwa ofis din dake gaf dasu kai tsaye momi taja hannun humaira suka fada.
Doctor meya faru??
ina patient dinmu??
Bangaren da yake ma gaba daya a kulle me yake faruwa??
Momi tayi saurin tambayarsa.
Dan siririn farin mu2min dake zaune bisa kujera yasa faffadan tebiri a gaba dake dauke da files akansa.
Ya gyara zaman glass dinsa da dan yatsa yace “Alhaji isma‘il mahmud??“
Humaira da mominta suka dubi momi tayi saurin cewa “Eh.. shi muke nufi doctor.“
To bismillah ku zauna ko??
Ya fada tare da yi musu nuni.
A hankali suka karaso tare da zama bisa kujerun dake fuskantarsa cike da zakuwa da jin abinda zai fito daga bakinsa.
Kafin yace komai saî murmushi mai kama da dariya ta kwace masa yace “Ta ina ma zan fara??
To magana ta gsky Alhajinku ba mu2wa yayi ba hasalima an tafi neman lfyrsa da yakinin samun sauki da yardar Allah.“
Ban fahimta bafa doctor.
Momi ta fada. Ya gyara zama tare da cewa “Ah! dama kamar yadda kuka sani ne mun fada muku duk sanda aka samu sahihiyar hanyar da za‘a bi ta neman lfyrsa zamu sanar daku, akalla sati biyu da suka wuce muka samu rahotanni daga wani Babban asibiti a kasar finland akan sunyi gwajin aiki akan cutar kuma sunyi nasara gagaruma. Toda muka tbbtr da hakan munyi iya kokarinmu akan mu sameku sai ya zamana lambar da kuka bane da address mun nemesu mun rasa, akalla wajen kwana goma kenan sai yau muka gani muka kiraku.
Lkcn da muka rasa yadda zamu yi ne kwatsam! sai ga wata gidauniya me suna FISABILILLAH FOUNDATION da suka ji abinda ke faruwa da kuma halin da ake ciki na bukatar aiki da gaggawa sai suka dauki gbrr daukar nauyin fita dashi bama tare da kun sani ba, sune suka dauki dawainiyar komai kuma yanzu haka ina tbbtr muku sun isa finland harma an fara aiki kuma komai zai kammala ya kuma warke ras a kasa da wata daya.
Amma badon anyi haka ba a hasashen da mukai bazai kai yanzu da ransa ba Allah ne kawai yayi da kwanansa a gaba, ta silar wannan gidauniya.“
hawayen dake idon momi ya hade da murmushi daya ziyarci fuskarta yanzu ta juya suka kalli juna ita da humaira, humaira ta wani dauke ba wani alamun jin dadi data nuna.
Momi ta juya gareshi tace “Alhmdllh!! bansan irin godiyar da zanyi garesu ba dama ku kanku gsky kunyi mana kokari sosai, FISABILILLAH FOUNDATION!!
Ta fada tare da yin shiru tace “Na dade ina jin lbrnsu wajen aikata abubuwa irin wannan kuma kmr yadda sukayi mana muma munyi alkawarin daukar dawainiyar kashe linkin abnd aka kashe akanmu ga wasu marasa lafiyan dake bukatar taimako.
Idan da hali ina so a sadamu da wannan gidauniya donyi musu godiya, idan kuma da wani tallafi da suke bukata don ci gbnsu muna iya basu tallafi muma.“
Mu2min ya gyara zama yace “maganar gsky gidauniyar nan ba zasu taba yarda asan su bama bare aje ayi musu godiya ko wani abu makamancin haka, amma ba2n kashe kudi akalla Alhajinku an kashe kusan miliyan biyar akansa...“
Mu kuma zamu bada naira miliyan goma, samu masu bukatar aiki da basu da hali ayi musu har sai kudin sun kare.
Farin mu2min ya gyara zama yayinda murmushinsa ya kasa boyuwa yace “Hajiya wato da ace za‘a rinka samun irin hakan da ba karamin nasara za‘a samu ba, sbd sau tari zaki ga wadansu akan wasu kudi da basu taka kara sun karya ba wlh sai dai patient dinsu ya mutu sbd basu da yadda zasu yi.
Zaki zubar da hawaye idan kika ga rai ya salwanta akan rashin kudi naira dubu ashirin ko goma ke kasa da haka ma, kuma mafi yawan wadanda yakamata su taimaka basayi.
Momi ta gyada kai tare da cewa “Mun dauki izinah daga abnd ya faru kuma insha-Allahu zamu dage wajen aikata ire-iren abubuwa irin wadannan.
Ah idan mun isa gida zan aiko maka da chak din kudin da kuma... dan ladan albishir naka kaima.“
Takai karshen maganar tana murmushi.
Likitan me lambar kwarewa mafi kololuwa ya gyara zama ckn murmushi yace “A madadin ni kaina da duk wadanda wannan taimako zai shafa dama hukumar wannan asibitin muna mika godiyarmu, Allah ya saka alkhairi.“
Momi da humaira suka mike momi tace “ Mun gode sosai sai yan aiken nawa sun karaso“
To hajiya muma mun gode.
Ya fada.
Suka juya tare da ficewa ya mayar da kansa ga abnd yake yi.
Motarsu suka hau kai tsaye suka nufi gd momi nata farin ciki da annashuwa.
Suna isowa gd worn daya direban yayi tafkeken gate din ya fara budewa jim kadan motar tasu ta wuce izuwa harabar gdn, momi da humaira suka fito daga cknta kai tsaye suka wuce izuwa ckn gdn.
Tafiya kadan sukayi suka iso katafaren falon alfarmar gdn nasu, humaira ta cire mayafin dake jikinta ta wurgashi kan kujera ta taka ta tafi da nufin wucewa izuwa dakinta.
HUMAIRA!!!
Momi ta kira sunanta ta juyo a hnkl, Zo nan.
Momin ta fada.
Ta tako a hnkl tazo gbnta.
Zauna!! momi Ta sake fada tare da yin nuni da hannunta izuwa kusa da ita.
ba tare da gardamar komai ba humaira ta zauna.
Momi tamkar me jin nauyin yin maganar abnd take son fada sai data jima sannan tace “Humaira!!“
ta kira sunanta tare da dorawa da fadin “Na fahimci rashin farin ciki da nuna bakin cikinki karara a lkcn da aka ce daddynki zai samu lfy, nasan dalilinki nayin hakan amma dole zan gaya miki hakan da kikai bai dace ba.
Koba komai mahaifinki ne baki da tamkarsa a duniya kuma baki isa ki canzashi ko kankareshi daga wannan matsayin ba har abada.
Na yarda muma munyi kuskure akan abnd mukayi kuma kema yakamata ace kin dade da fahimtar hakan kuma kinyi mana uzuri, wlh mahaifinki nasonki kuma yana kaunarki ma2ka zan shaidi hkn a ko‘ina, abnd yayi yana ganin gata ne don ya rabaki da wahala sai dai bai sani ba ya rabaki da farin cikinki na har abada ne.
Kiyi hakuri humaira ki maida komai wurin Allah ina da yakinin ba haka kawai abnd ya faru ya faru ba lallai akwai wata izinah da Allah zai nuna mana, amma ki daina dauka cewa mahaifinki makiyinki ne kinji.“
wasu fararen hawaye suka yi saurin gangarowa ta kuma2n humaira ta grgz kai ckn kasa da murya tace “Bawai bana son daddy ko rayuwarsa bane wlh nafi son inga ya rayu fiye da kowa sbd bana son a nunani a kirani marainiya har karshen rayuwata, amma momi faru..k... duk sanda na 2na bansan inda yake ba ya mutu ko yana da rai??
A dadi yake ko a wahala??
Nakanji na tsani duniya da duk abnd ke cknta, lkt a asibiti ya bamu tbbcn akwai yakinin daddy zai warke yaci gaba da rayuwa ckn walwala da nishadi, inama kuma ace akwai wanda zai bani tbbcn faruk na raye kuma yana rayuwa ckn farin ciki da nishadi???
Dazan samu lbrn hakan kawai ya wadatar dani amma babu.“
gudun hawayen nata ya karu.
Momi ta kauda kai tayi saurin mayar da kwallar dake neman kwararowa daga idanunta, tana tausayawa humaira ma2ka.
Ta dafa kafarta tace “Nayi miki alkawarin daga sanda mahaifinki ya dawo to duk inda faruk yake a fadin duniya sai an nemoshi ma2kar dai yana da rai, koda nawa kuma za‘a kashe akan hakan.“
Humaira tayi saurin hada hannayenta ckn na momi ckn sheshsheka tace “Don Allah ku taimakeni momi... ina son na kara ganin faruk koda sau daya ne tak a rayu..wata..“
kai wannan love haka..
Allah ban wadda xatasoni kaman haka..!
#Ilalliqa'a
muhadu gobe.
Inkarike daure muku zaren labarin INSHA ALLAH..!