Daddy yace “Yayi kyau faruk kuma ka birgeni akwai kudin da nayi maka alkawari zan baka ka tsaya ka karbi cheque din.“ Faruk ya juyo hawaye suka kwararo ta kasan glass din dake sanye a idonsa yace “ka rike kudinka bana bukata.“
Ya sake binmu da kallo wanda ya kara rikitani ya juya ya fice.
Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un.
Abin da AL‘AJABI sai kace almara!! Faruk da kansa ke furta rabuwa dani?? Da kafarsa zai fita daga inda nake??
Idona yakai ga fuskar daddy wanda keta murmushi yana annashuwa.
Da sauri na nufi hanyar fita inda faruk yabi nabi bynsa duk da kiran dasu momi keyi min baisa na dakata ba.
A guje na karaso inda yake tuni har ya fito harabar gdn duk da cewa da ma‘aikata masu yawa suna ta kaiwa da komowa bai hanani tarar gbnsa ba, na rike sandar dake hannunsa zafafan hawaye suka kwararo da idanuna ckn sheshshekar kuka nace “Faruk kana nema rana ka cnz min daga hakikanin yadda nasanka izuwa wani daban, ko a mafarki ban zaci haka daga gareka ba. Yanzu ma a haka tayaya zaka tafi??
Faruk ya grgz kai yace “indai don ta tfy ne karki damu na tbbtr salih yazo??
Yayi nuni da inda motar da muka zo take. Na juya na kll inda ya nuna, kwarai yazo kuwa. zcyt ta fada min.
Ya dora da fadin “Na gaya masa dama ya biyo bynmu zai daukeni ban bari kin sani bane sbd kada ki gane akwai wani abu.“
Na kara gyara tsayuwa nace “amma faruk yakamata ka tausaya rywta a karona biyu ka sani idan ka tafi ba lallai na dauki dogon lkc ba zan bakin ciki da takaici zasu kasheni, idan ma wani wuri kake so kaje na yarda zan bika muje ko ina ne kuma duk rintsi da wahalarsa zan iya jurewa....“
Ba inda zaki bini humaira kuma baki isa ki fita daga ckn gdnnan tare dani ba, na hakura dake na hakura da tarayyarmu 2nda ba wahayi akayi mana dole sai mun zauna tare ba.
Ya fada yana me daga murya.
Bakina yadau rawa na dan taka kadan izuwa gfnsa nace “faruk!! nice fa!! ni kake gayawa haka??
Anya kuwa kasan abnd kake fada??“
Ya gyada kai tare da cewa “kwarai!! da hnklna kuma duk abnd nake fada shine abnd nake nufi har ckn zcyt.“
Tfyr hawayena ta canja izuwa kara sauri nace “A takaice kana so kace duk irin kaunar da kake yimin a baya yanzu babu ita??
Duk yadda alkawuran da mukai zaka karya su??
kenan soyayyar da muka dade muna raina ta mu2, yanzu babu ita 2nda har zaka iya tafiya ka barni...“
Yayi saurin juyowa yace “EH! babu ita na dade da kankareshi daga zuciyata wanda shine ya bani krfn rabuwa dake.
Dai-dai lkcnne daddy da momi suka karaso.
Na dubeshi nace “idan ka tafi kai da kanka sai kayi dana-sani me girma...“
dana-sani??
Ya tambaya yana dubana ya dora da cewa “Ai na gama dana-sani 2nda na yarda na aureki, wannan shine kuskuren da nayi mafi girma a rywt.“
Kaina ya sara da karfi Bansan sanda nace “karya kake faruk!! Ni nasan baka isa ka tafi ka barni har abada ba ko ka daina so na ba.“
Ya juyo yace “Kece makaryaciya humaira amma ni duk abnd na fada gskyne, zan tafi na barki kuma bazan taba dawowa ba har abada.“
Ya yunkura zai tafi nayi saurin rike rigarsa ya juyo muka dubi juna nace “Ka daina zaton ni kmr kowa ce a gareka, nasan maganar da zaka fada ta gaske da wadda bata gaske ba.
Nasan abinda zai yiwu a wurinka da wanda bamai yiwuwa bane, abnd kake fada yanzu har abada bazai yiwu ba.
Nasan kana fadan hakane sbd kawai kana son na kyaleka ka tafi, idan kuma har da gaske kake ka juyo ka rantse min da Allah Ka daina sona kuma zaka iya tfy ka manta dani har abada!!“
Ya tsaya kawai ya kasa motsawa.
Na katse shirun ckn daga murya da cewa “Ka fada mana idan zaka iya“.
jimawa kadan ya juyo a hnkl tare da grgz kai yace “humaira kinsanni ma2ka fiye da kowa a duniya, kinsan abnd zan iya yi da wanda bzn iya ba.
Nayi karya idan nace “Zan iya cire sonki daga zcyt kona manta dake a tsawon rayuwata.“
Yayi kasa da murya yace “Amma ina so ki fahimta yau ba zabi bane a garemu, dole ne mu rabu.
Bashi da wani alfanu cgb da zama a yadda muke sbd kowa baya son zamanmu tare kuma ba wnd keda shirin taimaka mana, duk daren dadewa dole wataran zamu gaza watakila sanda lkc ya kure mana.
RABUWA itace kawai maslaha a garemu koda bama so amma dole mu hakura.
Kin sani bazan taba son mu rabu haka kawai ba, dalilaina nada ma2kar karfi wanda suka sa ni kaina naji na gamsu mu hakura da juna ba sonki nayi ba idan na barki kika bata da iyayenki akaina, na dawo dake garesu shine Kokoluwar son da zanyi miki sbd koda yaushe ryw aunata ake akan mizani, dole na fada nayi kuskure tun farko dana yarda na bata da kowa akan SOYAYYA kuma bazan so abnd nayi kema ki maimaita irinsa ba.
Kiyi hakuri ki fahimceni humaira don Allah.“
Na jinjina kai sanda sautin kukana ya kara fitowa nace “yanzu meye madogara a gareka ina zaka??“
yace “Allah ne kawai madogara ta gareshi na mika al‘amurana na tbbt bazan taba tozarta ba.“
Ya juya inda ya tbbtr anan su daddy ke tsaye yace “Alhaji yau mun rabu da y‘arka kmr yadda ka nema, ni kuma na tafi kmr yadda kake so, amma ka sani idan wai kayi hakan don ka samu farin ciki to ina me bkn ckn sanar dakai kayi bnkwn dashi har abada.
Na tbbt GUGUWAR KADDARA dake binmu tana gaf da zuwa kanka.
Alkhairi nayi amma ban tsira ba bare kai daka shuka mana sharri, ba fata nake maka ba amma kaji tsoron taka UKUBAR don dole sai tazo.“
Daddy murmushin keta kawai yayi don wasa ma ya dauki zancen.
faruk ya juyo gareni yace “Kada ki manta idan kika so nan da dan lkc kina da damar kîyi wani auren ba takunkumi akanki ya jinjina kai ya juya da fadin “ Na tafi humaira!! Sai wata rana idan muna da rabon saduwa.“
Bani da ikon hanashi a yanzu dole tasa nabishi da kallo har izuwa sanda motarsu ta fice daga ckn harabar gdnmu, a hankali kuma idanuna suka fara duhu kwakwalwata ta rikice, idanuna suka fara lumshewa a hankali ban ankara ba na sulale kasa sumammiya...
******** **********
¤¤ Ahmad dake karanta lbrn yayi saurin juyo shafin da yake karantawa sakamakon zuwa karshe da yayi, yayi saurin bin faffadan littafin dake hannunsa da kallo. Iyakar inda aka tsaya da rubuta labarin kenan, zuciyarsa ta fada masa.
Ya saki lttfn tare da kauda kai kmr ya fashe da kuka amma ai ba shikenan ba da saura sai meye kuma ya faru daga nan??
Ya tambayi kansa, ya shafi fuskarsa sannan ne yaji hawayen daya dade yana yi ashema kuka yake yi bai sani ba.
Tunda yake bai taba jin lbr na abin al‘ajabi da tausayi kmr wannan ba yayi saurin sake jawo lttfn ya bude farkonsa ya kurawa hotunan dake manne a farkon littafin ido, hoton musamman hoton faruk din dake gefen na humaira, Allah sarki!!
Ga kyau ga haiba ga annuri na tashi a fuskarsa, dukkansu farare sol tamkar larabawa sun dace ma2ka.
Ya dubi dan zanen da akai a tsakiyar ho2nan, hoton alamar LOVE mashi ya shiga ta tsakiya kasa kadan an rubuta:
<LIFE TOGETHER DIE TOGETHER>
littafin ya subuce daga hannunsa ya dafe kai kawai. Allah sarki!! Ashe ba banza ba humaira ta kasance koda yaushe ckn damuwa, shine dalilin da yasa ta zama wata iri harma ya kasa gane kanta.
Ahmad ya daga kai ya kalli agogon dake manne a dakin nasa karfe 3:12 na dare, safiyar ma da saura kenan!!
Ya fada.
sbd yadda yake ji kmr ya jawo safiyar tazo, so yake kawai ya ganshi a gbn humaira sbd akwai tambayoyi masu dimbin yawa da yake son yi mata.
Dukan kofar dakin nasa da akeyi a hankali yasashi dawowa hayyacinsa ya mike tare da takawa izuwa bakin kofar.
Waye??
Ya tambaya ba tare daya bude ba.
Nice.. Fatima ce.
Ya bude kofar a hankali ya dubeta tare da cewa “Menene ya faru??“
Tadan dafa bakin kofar tare da cewa “Yaya lafiyarka kuwa??
Ina kwance a daki 2n dazu nake jiyoka kana surutai kai kadai fa.“
Kai!! zancen zucin da nake dama a fili nake yinsa kenan??
Ya tambayi kansa a zcyrsa.
Ya juyo tare da cewa “a‘a.. kin... Waya nake yi ne da wasu abokan business dinmu muna magana ne akan yiwuwar wata yarjejeniya mu da su, bawai....wani abu bane...“
Waya har karfe 3:30 na dare??
Ta tambaya tare da cewa “gari na wayewa kuma karfe 8:00 ka fita, Allah yaya mutanen nan fa idan ka biye tasu zasu haukata ka!!
HAUKA????
yayî saurin tambaya.
Ya dora da fadin “kawai daga ina ayyukana sai hauka ko kuwa an gaya miki kwakwalwar mu maza irin taku ce??“
fatima Tayi dariya tare da cewa “To! Yanzu dai duk ba lkcn wannan bane don Allah ka kwanta kayi barci ka huta, ka kyale mutanen nan gobe sai ku karasa.“
Ya gyada kaî tare da cewa “To!! dama mun gama.“
Taja da baya da fadin “Sai da safe.“
OK!! ya fada sanda ya mayar da kofar ya rufe tare da takawa ya dawo kan gadonsa ya kwanta amma barcinma gagararsa yayi, 2nani kawai yake ta yadda zaiyi ya iya shawo kan humaira ta karasa masa lbrn nan.
Sai byn tsawon lkc barci ya daukeshi ba kuma wani dadewa yayi ba aka kira sallar Asuba.
*Tunda ya tashi bashi da wani 2nani sai asibitin da humaira take, 2ni ya mayar da komai ckn jakar tata kmr yadda take badon-badon ba da 2ni ya fice da sassafe amma dole tasa ya hakura.
Misalin 8:30 na safe suna zaune bisa kujeru su uku sunsa faffadan tebirin cin abinci a gbnsu wanda ke dauke da abinci kala-kala akansa, Ahmad da sauri yake kai abncn bakinsa burinsa kawai yaga ya kammala ya fita, Fatima ta kofin tea dake hannunta ta dubeshi tace “Yaya don Allah kaci a hankali, Mum jibi wani cin abnc da yake yi don Allah.“
Ya bîta da kll tare da cewa “Ina ruwanki??
Kin ganki...“
Mum din tace “gsky ta fada ai irin wannan cin abinci kmr zaka tashi sama??“
Ya dan daga kansa yace “wlh mum akwai abnd nake so naje nayi ne da gaggawa..“
Aiki ko??
Ta tambaya ba tare data dubeshi ba.
fatima tayi saurin cewa “Shine mana mum ai kllm zancensa kenan.“
To!! Fadi ba‘a tambayeki ba.
Ya ture kwanon dake gbnsa ya mike tare da cewa “Mum daga daki wucewa zanyi sai na dawo.“
A dawo lfy Allah ya bada sa‘a.
Mum ta fada ahmad ya amsa da ameen tare da takawa.
Fatima tace “A dawo lfy yayana na kaina.“
Ya waigo tare da cewa “Allah yasa kanwata ta goshina.“
Fatima ta kyalkyale da dariya.
Mum kanta sai data murmusa tare da cewa “kudai abin dariyarku yawa gareshi.“
ahmad da sauri-sauri ya dauki abubuwan daya saba dauka hade da jakar ta humaira da key din motarsa ya fice daga gdn.
Tafiyar da yakeyi akan kwalta kanta ba irin ta kllm bace hakan yasa a y‘an kalilan min2na ya iso asibitin, ya karasa da motar tasa inda aka tanada yayi parking kai tsaye ya wuce ciki.
Allah yasa ta farfado ta dawo hayyacinta, Allah yasa ta yarda ta taimakeshi da abnd yake son ji.
A hnkl ya 2ra kofar dakin wanda ya kasance na musamman a asibitin ya shiga, Ido hudu sukai da ita yayi saurin canja tafiya.
Alhmdllhi! ya fada a ransa ganin yadda ta dawo tamkar ba ita ya bari a wani hali jiya ba.
Ya karaso a hankali tare dayi mata sallama sanda ya iso gaf da ita ya zarce ga kwantaccen tsukakken tebirin dake jikin gadon da take ya jingina zuwa can yace “Sannu humaira, ina fatan saukin jikinkinki ya wuce yadda nake gani a zahiri Sannan da fatan zaki yi hakuri da abnd ya faru nasan nine na jawo miki.
Ya zanyi? dole na hakura mana, na hakura rabin jiki na ma ya tafi nake zaune da rabi!!
bare wannan.
Ta fada tare da yi masa nuni daya bata jakarta dake hannunsa.
Ya tako ya dawo yana me cewa “banga kowa ba sai ke kadai??
Momi na ce kawai dama kuma ta fita amma zata dawo yanzu.
Ya mika mata jakar yana me dubanta lkc guda yace “Naji faruk ya tafi kin suma a wancan lkcn daga nan sai me kuma ya faru??
Humaira ta saki jakar dake hannunta tare da binsa da kll tace “Abnd nake gudu sai daya faru kenan??
Ina ruwanka da jakata??
Meye na bude min??
Da izinin wa kayi hakan??
Ahmad ya grgz kai tare da cewa “kiyi hakuri nasan bai kamata bude miki abin sirri ba amma Allah ya kaddara ta hakan zansan lbrnki, naga abbwn AL‘JABI da yawa a cknsa ki taimaka ki kawar da dubunnan tambayoyin dake min yawo a zuciyata.
ckn fusata humaira tace “Ba za‘a fada maka ba to! Sbd banga wani dalili ba da zaisa dole sai kasan komai gameda rayuwata ba 2nda idan ma ka sani ba abnd zaka iya yi.“
ka daina taso min da tsohon ciwo ka fita ka tafi kawai.
Ta nuna hanyar fita..
Uhmm mumadai dabe karanbanin budewaba da bazamusan labarinkiba humaira..
Kuma muna buqatan aqarashemana..kobahakaba abokai..!??