Wasu abubuwa bakwai da suke taimakawa wajen samun bugun zuciya, da kanyi sanadiyar mutuwar mutane batare da jinya mai tsawo ba. Wasu masana da suka gudanar da wani bincike akan wasu mutane masu yawa, a jami’ar Australia, suka bayyanar da hakan.
Na farko idan mutun ya kasance yana yawaita kallon akwatin talabijin na kwamfuta mai kwakwalwa, da na talabishin, wanda idan sukan kalli skirin din na sama da awowi hudu a rana, hakan na haifar da hadarin kamuwa da cutar bugun zuciya “Heart Attack” a turance. Haka idan mutun ya yawaita samun bacin rai, to ya hanzarta magance wannan bacin ran, da neman shawarwarin masana, haka ya kaurace ma wannan abun da yake haddasa mishi bacin ran da gaggawa.
Samun bacci da yake karancin awowi shida shima wata hanyace da take iya haifar da cutar bugun zuciya. Akwai bukatar mutun ya yi baccin awowi takwas a dare, wanda hakan zai taimakama na’urorin jikin mutun wajen samun damar aiki yadda ya kamata. Sannan yanayin waje da keda yawan turniki na haykin ababen hawa da yadda ake kona bololi da dai makamantan su sukan, haddasa bugun zuciya.
Daukar wasu damuwa na yau da kullun batare da magance suba, ko neman taimako daga wajen masana kan iya haifar da bugun zuciya. Yanayin zafi batare da amfani da na’urorin sanyaya yanayi ba, kan taimaka wajen samun bugun zuciya shima. Hakan na nuni da cewar mutane su kokarta wajen sanyaya zuciyar su da jikin su a lokacin da abubuwa sukayi yawa.
Sources Dandalin VOA
Title :
Abubuwa Da Kan Haifar Da Cutar Bugun Zuciya
Description : Wasu abubuwa bakwai da suke taimakawa wajen samun bugun zuciya, da kanyi sanadiyar mutuwar mutane batare da jinya mai tsawo ba. Wasu masana ...
Rating :
5