*Kimanin 76 Daga Cikinsu Sun Mika Wuya
Kimanin membobin Boko Haram guda 76 wadanda suke neman abincin da za su ci ido rufe a yankin jihar Borno ne suka mika wuya ga dakarun sojoji, kamar yadda wata majiya daga dakarun sojojin da 'yan bangan sa kai suka bayyana a ranar Larabar da ta gabata.
Mutane 76 din, ciki har da yara da mata sun mika kansu ga dakarun sojoji dake garin Gwoza a ranar Asabar din da ta gabata, kamar yadda wani babban jami'in soja ya bayyana.
Majiyar ta ce yanzu haka dukkanin wadanda suka mika wuyan suna tsare a hedikwatar sojojin dake Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Title :
Yunwa Da Matsin Lamba Ta Soma Sanya 'Yan Boko Haram Mika Wuya Ga Sojoji
Description : *Kimanin 76 Daga Cikinsu Sun Mika Wuya Kimanin membobin Boko Haram guda 76 wadanda suke neman abincin da za su ci ido rufe a yankin jihar ...
Rating :
5