Y'AR AMANA Part 7
wth==>Aßdool-azeez ßeen Aßoußakar
** shewar tasu ta zagaye ilahirin makarantar har wadanda ba'a wajen suke ba sai da suka dauka, a hnkl me suna ibrahim din ya tako ckn kasa da murya yacewa nusaiba "yar amana waccan faridar taki tana da matsala ki rinka yi mata fada koda dai mu ba zamu taba dai-daitawa da ita ba."
me yasa???
Tayi saurin tambaya.
Sbd batayi ba ko kadan.
Ta kauda kai izuwa inda farida suke zaune su biyu da kawarta ta dawo gareshi tadan bata rai tace "kaga ya isheka to!! Karka kara gaya mata haka sbd yar uwata ce idan ka tabata ni ka taba, don haka don Allah ka bari komu bata."
Yayi saurin cewa "a'a rufa min asiri! Idan kika bata dani ai na shiga uku a makarantar nan, a hnkl yaja da baya da cewa "muna jiranki a class fa!! Kada ki manta."
tabisu da kll kawai yadda suke nufar ajin daukar lakcar tamkar itace lecturer din.
*Zaune suke su biyu bisa wani dan dakali dake faffadar harabar, kasancewar hali yazo daya yasa suke tare koda yaushe a makarantar. Wai ya naga duk an tafi class ne gashi kuma lecturer baizo ba??
Hadiza ta tambayi farida ckn salon munafunci.
Faridan ba tare data dubeta ba tace "zai wuci wannan banzar ce zatayi musu bita, kinsan ba laifi ajin namu ya tara dakikai masu yawa."
hadiza ta dauke kai tace "ba haka bane sister din taki ce kwanyarta babba ce, duk yadda ka fahimci abu idan kazo gbnta sai kaga baka fahimci komai ba ko zamu je ne muma zamu karu fa!."
da sauri ta harareta tace "kema banza ce wani lkcn fa! Muje ina??
Ita ta isa na zauna ta karantar dani??
Allah ya sawwake."
takai karshen maganar ckn gadara.
Hadiza ta kyalkyale da dariya tace "baki da dama kawas! Bakya dagawa gajar kafa ko kadan."
tayaya zan saurara mata??
ki bari ma ina gaf da binciko wani abu indai yazo min a dai-dai to nusaiba da kafarta sai ta gudu daga gdnmu wlh. Farida takai karshen maganar sanda suka fashe da dariya tare da tafawa, ckn dariyar hadiza tace "amma kada fa kaza ta tono wukar yankata!!"
ina! wannan kazar hatsin cinta zata tono. Suka zarce da dryr.
Basu tashi ba sai da suka hangi lecturer dinsu.
*** Sai can misalin karfe 1:30pm tsilli-tsillin dalibai suka fara fitowa, y'ar amana na daya daga ckn na farko-farkon kai tsaye jikin wata bishiya ta dosa wacce daga ita zuwa motar data kawosu tazarar bata da yawa ta jingina a jknta.
Hnnta rike yake da zundumemiyar jakarta yayinda bironta ke makale tsakanin y'an yatsunta, tsayuwarta keda wuya ta fara hange-hangen ganin farida ta fito sun tafi domin tuni direbansu ya iso.
Sai can jimawa data rasa abnd zatai ta dago biron dake hnnta ta fara zanawa a hnnta sai dai ina! Tuni ya dauke baya zana komai, ta tabe baki da cewa "kai! Anyi banzan biro wlh allah yasa ma ba'a class yayimin haka ba."
Ta cillar da biron duk da cewa batasan inda ta jefashi ba, karar dirarsa a jikin mu2m kawai taji kirjinta ya doka da karfi, kada dai ace ta jefi wani dashi??"
tambayar da tayiwa kanta kenan tayi saurin dago kai izuwa inda ta jefa biron hannunta akan bakinta ckn jimami sai dai lkc daya tayi saurin canjawa sanda suka hada ido.
Tun daga kalarsa da shigarsa ta dan kwalisa na gaske, kyakykyawa da sigar kyan hali ke rubuce a fuskarsa ta kara tbbtrwa lallai shi din ne.
USMAN!! Me kuma ya kawoka makarantarmu??
Abnd bakinta yayi saurin tambaya kenan. Ya kauda kyakykyawan ruwan kasar glass dake da fadin karawa fuska kwarjini dake idonsa ya kllt sosai tare da sakin murmushi byn daya tbbtr ita dince, a hnkl ya tako da cewa "ni dama ai a NBC UNIVERSITY nake kara2 nan kenan."
amma me yasa bamu taba haduwa ba?? Ta sake tambayarsa.
Ya karaso inda take sannan yace "department dinmu ne ba daya ba kinga abune mawuyaci mu hadu, yanzun ma wajen abokina nazo ashe rabon kaddara ta sake hadamu ne."
ya sake yin murmushi yace "2n sanda kika cemin sunanki Y'AR AMANA nasan ba'a sannan nasan sunan ba tbbs ina jin sunan a wani wurin, sbd sunan ya zagaye kaf fadin jami'ar nan a yanzu kin yarda nasanki a kunne tun tuni??"
Kafin ta bashi amsa ya dora da cewa "Bama dai wannan ba me yasa kika kwala min biro haka kawai??
Ko kinsan idan nakaiki kara sai an ciki tara??" dariya tadan kwace mata tace "ko zaka jaraba ne??"
waneni??
Ai idan da zanyi haka toda zaman makarantar nan sai ya gagareni sbd y'an department dinnan naku suna ji dake ma2ka, duk wanda ya tabaki zai gane kuransa a wurinsu. Amma fa duk da hkn idan da laifukan da nayi miki bakya hakura toda yau bame rabani dake sai Allah, sai dai ke shugabar masu hakuri ta duniya ce dole kema idan kinyi a yafe."
dai-dai lkcnne farida ta jingina da motarsu dake nesa da inda suke tana wani hade rai tace "ke nusaiba dalla kizo mu tafi!!" nusaiba ta juyo gareshi tace "to mu zamu tafi da fatan dai ka hakura ko??"
yayi murmushi tare da cewa "uhhm! Sai nayi tunani, ki bani lambar wayarki idan na gama thinking sai na kiraki na sanar dake na hkr ko a'a."
ta sake fashewa da dariya tare da karbar wayarsa daya miko mata tasa mai lambar tare da mayar masa da wayar, ya karba zata taka kenan yace "kinga Nama gama tunanin na hakura." tayi murmushi tace "to ban lambata."
a'ah ki barta dai ko don gaba!!
Dariya tasa ta wuce, shima yabita da dariyar. Har motar tasu tabar wurin binta yake da kll yana murmushi lkc.
Ya maida kansa ga wayar tare da fada "Y'AR AMANA" ya wuce ga inda zashi 2n farko.
¤dai-dai sanda motar tasu tadau hny ne farida ta gyara zama ckn yatsina fsk tace "Shi kuma wancan mu2min a ina aka samoshi??" nusaiba ba tare data dubeta ba tace "hmm.. A duniya, dah a ina ake samun mutane??"
* farida ta kara bata rai gami da zunburo baki tace "to naji ai ba cewa nayi ki gaya min bakar magana ba."
kiyi hakuri idan wai kinji haushi ni ban fada don ya bata miki rai ba.
Faridar taja dogon tsaki tare da kwantar da kanta jikin kujerar motar tana me bin hnyr da suke kai, Ba wacce ya kara ce da juna komai har suka isa gd. *
** misalin karfe uku na ranar nusaiba ce ita kadai kishingide akan tamfatsetsen gadon alfarmar dake dakinsu, kanta na jingine jikin fuskar gadon yayinda kyakykyawar fuskarta kai tsaye ke fuskantar wani katon lttf irin na manyan dalibai tana nazarinsa.
Rike yake a hannunta na dama yayinda hannunta na hagu ke aikin budo shafin gaba duk sanda ta gama da wanda take kai, kwayar idonta kuma na zagayawa daga sama izuwa kasan faffadan littafin. Kll daya zakayi mata kasan a nutse kuma ckn jin dadi da annushuwa take karanta lttfn, hnklnta kaso 90% ya tafi ga nazarin da take yi.
Bayan wani dan lokaci ne kuma y'ar kyakykyawar wayarta tadau kara alamun shigowar kira wanda hkn ne ya katseta daga abinda take yi, a hnkl ta mika hnnta ta jawo wayar lkc guda tayi saurin bin secreen din wayar da kll sakamakon bakuwar lambar data gani.
Takai wayar kunnenta da fadin "helloooo!!!" helloo! Ranki ya dade Y'AR amana kinsan ko waye??
Ba tare dame kiran ya jira amsarta ba yace "sunana.....
USMAN!!!!" suka fada a tare.
Ya akai kikayi saurin ganoni haka?? Ya fada ckn salon tambaya.
Ta gyara kishingidar da tayi tace "sbd kai kadai ne wanda nasan zai kirani da bakuwar lamba...
Barma ta wannan lambar taka ce ta musamman ba irinta sauran mutane ba kmr yadda kake na musamman ba kmr saura ba."
yayi dry a karona farko yace "kmr yadda ke kuma kike matsokaniya ba, kiyi hkr fa! Na katse miki hu2nki ko??
Don daga jinki daga barci kika tashi." hah! Waye ya fada maka??
Don kuma kai dan gata dakai kana hutawa sai ya zamana kowa haka ne??
Da sauri yace "wane ni?? Ina na zama dan gata??
Kin gammu nan a rana muna ta fama."
Kana nufin kana ckn ranar kana fama harka iya tsayawa ka kira waya?? Ta tambaya.
Ah.. ina nufin nadan koma inuwa na huta kafin na koma.
Ta kyalkyale da dariya tare da cewa "usman barkwancinka yana da yawa."
ya danyi shiru alamun murmushi yayi yace " haka kowa yake cewa dll kuwa ni burina a koda yaushe shine naga jama'a suna murmushi suna dariya, musamman ma irinku da bakwa dariya sai ta kama. "
Eh amma dai daka kirani yanzu ba kuka kaji inayi ba ko??
Duk suka fashe da dariya.
Ya katse dariyar da fadin "Dama cewa nayi bari in kiraki nayi miki sannu da hutawa."
ta juyar da kanta tace "shikenan dama sakon??"
kwarai shine kawai.
Tayi murmushi tace "to ngd sosai usman kuma kaima sannu da naka hutun."
to nima ngd Y'AR AMANA da fatan idan zamu hadu nan gaba ba wani tsautsayi dazai sake faruwa."
a karona biyu suka sake yin dariya.
Sai anjima. Da abnd ta rufe kenan amon dariyar na tashi daga y'ar siririyar muryarta tana me grgz kai na mamakin barkwancin usman, sai dai tayi saurin dago kai tare da dakatar da dariyar da take yi tabi farida da kll wacce tun tuni ke tsaye a kanta.
Faridar wacce ta tabe baki tana klln nusaiba tayi saurin yin dryr wulakanci tare da cewa "Allah ya biya masoya!! Soyayya ko?? Dakyau."
tayi kasa da murya sosai ckn sigar rainin hnkl wai tana kwaikwayon yadda nusaibar keyi tace "
*nagode sosai kaima kuma sannu da naka hutun* "
ta zarce da dariya.
Nusaiba ta ajiye wayar a gefenta tace " to ke waye ya gaya miki hirar soyayya muke yi?? Kenan ba wata alaka ta mu2nci da zata hadamu da wani sai soyayya kawai??"
farida ta taka gaba kadan tace "ke nusaiba! Ni ba yarinya bace da zaki raina min hnkl, ina karanta lbrn soyayya, ina jin lbrn soyayya, ina kll sannan kuma ina ganinta a zahiri daga wurin masu yinta ba abnd zaki boye min."
ta kara zarcewa da dariya tace "nice! Masoyiya!! Munafuncin banza sai munyi magana ace ai ke kamammiya ce, kaza da kaza ana wani koda ki to ynz kuma ina kamun kan??"
farida! Na fada miki nifa ba wani zancen syy tsakanina da wani, usman mu2nci ne ya hadamu ba kmr yadda kike 2nani ba.
Nusaiba ta fada.
Farida ta kara takawa nesa da nusaiba tace "karyar banza!! Dama ai irinku haka kuke majizan ciki ne sari ku noke, mu da akewa klln bamu da kirkin munfi kamun kai sbd ba wani banza dazai rudemu."
ta juya tana dry zata fice, nusaiba tace "to waima idan syy muke ina ruwanki? Meye naki a ciki??"
da sauri ta juyo tare da daga hnnta kmr me shirin yin surrender tace "wlh ba ruwana! Kawai dai ina so na fada miki ne kibi a hankali..." kina gargadi na akan haka ne??
Nusaiba ta tambaya.
Farida tace "A'a sai dai ina baki shawarane sbd mazan ne shegu ne, kada yakaiki ya baro."
to ki rike shawararki ko??
Naga dai ai ba hnkl kika fini ba.
Farida ta tabe baki tace "ban fiki hnkl ba amma nafiki sanin dny, kefa koda yaushe kina nan a nade daga gd sai makaranta. Radio baji kike ba, t.v ba kallo kike ba, jarida ba karantawa kike ba, kedai gaki nan ba abnd kika sani na harkar duniya."
nusaiba ta mike zaune tace "haka dai kika ce.."
kuma hakan ne ba, kidai bi a hnkl wlh. Farida ta fada sanda ta juya.
Nusaiba ta kara karfin muryarta tace "makaryaciya! Bakin ciki ne."
da sauri farida ta juyo da cewa "bakin ciki?? akan namiji kin isa nayi miki bakin ciki??
Nifa bari kiji idan duk mazan duniya zasu kare toba damuwata bane."
ckn mamaki nusaiba tace "Abbanmu ma ai namiji ne kina nufin har shi??"
ta gyada kai da cewa "Eh.. Harshi mana!! kaunata yake??"
bata jira amsar ba ta juya ta fice wanda ya kawo karshen doguwar hirar da ba kasafai suka fiye yin irinta ba...
Anya wannan yarinyan akwai hauka akanta...
Barkan ku da rana...
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma