bawai ana kiranta da sunan ne kawai ba tbbs ita y'ar amanar ce da gaske, wacce aka bar min ita sbd da yarda akan cewa zan iya rike amanarta.
A duk sanda na dubi fuskarta ina ganinta kamar ta mahaifinta ce wanda yayi min komai a rywr duniya, ya mayar dani mutum ya taimakemu sanda muke tsananin bukatar taimako.
2n sanda na samu y'ar amana naji a jikina cewa na samu y'ar da zanyi alfahari da ita. *duk da cewa a wancan lokacin bani da wani sani akan yadda zan tafiyar da makudan kudin amanar da aka bari a hannuna amma nayi kokari na shiga kasuwanci dasu kuma Allah yasa musu albarka ckn sauri suka fara habaka, byn tsawon lkc ne kuma muka tattaro muka baro katsina izuwa kano da zama kasancewarta cibiyar kasuwanci wanda anan na kara habaka har nakai matsayin da nake kai a halin yanzu.
Duk abnd na mallaka ciki da waje babu koda sisin kwabo nawa a ciki duka mallakar Y'AR AMANA ne!!"
Yayi nuni da nusaiba byn da hannayensa.
Abba ya kawo dogon numfashi bayan daya gama dogon jawabin ya kara da cewa "wannan ne dlln da yasa bana bari ta nemi wani abu ta rasa, nake yi mata duk irin nau'in kyautar daya kamata da ita domin daga cikin dukiyar tane.
Nake kokarin janta izuwa wuraren da muke aiwatar da kasuwancinmu domin taga yadda ake juya dukiyarta, na tbbtr yanzu kowa zai yadda ina da dalili ko??"
ya tambaya yana me dubansu dukkansu.
Ba tare da gajiyawa ba abba yace "albarkacin dukiyar y'ar amana nakai duk inda nakai a ryw, sannan albarkacinta ne iyami taje hajji wanda yasa aka daina kiranta da sunan iyami sai dai hajiya."
A hnkl kuma hannunsa ya dawo nuni ga farida ckn tsawa yace "albarkacin dukiyarta kika rayu cikin jin dadi da walwala ba ckn wahala da ukuba ba, kike cin me kyau kisha me kyau wanda yasa kika girma da farinki baki kode ba.
Kika je makaranta me tsada, kike hawa mota me tsada sannan kike sa sutura me tsada wanda har ya saki gadara..."
farida tuni hannunta ke dore bisa kanta hawaye na kwararowa daga idanunta kmr ruwan sama, bin y'an falon kawai take da kallo daya bayan daya.
Abba ya kara daga murya yace "nasan yanzu kinji asalinki ko??
Kinji koke wacece da kuma yadda akai aka sameki??
Toga hanya nan zaki iya tafiya.
Yayi nuni da hanyar fita.
A hnkl ta zamo daga kan kujerar sautin kukanta ya fito fili, ckn sheshsheka tace "wlh abba dama karya nake ina fada ne kawai amma ba inda na isa na tafi, bani da kowa idan ba ku ba, bani da wadanda suka fiku...
Rashin sani da kuma gajeren 2nani yasa na aikata abinda na aikata sai yanzu na tbbtr da cewa jikina karya yake yimin yake bani cewa ni wata ce, ashe ni ba kowa bace face wulakantacciya kuma tsintacciya.
Abba na amince da duk hukuncin ko horon da zakayimin amma ka barni a cknku naci gaba da ryw sbd ku kadai gareni..."
ta zarce da kukan wanda ke tsuma zuciyar duk wanda ke falon.
Nusaiba ta share kwallar dake idonta ta kama hannun farida tana yi mata nuni data dawo ta zauna, maimakon tayi hakan sai tabita da kallo gami da cewa "na dade ina taka ki yadda raina ke so, ina cin zarafinki na muzanta miki gami da bata miki.
Nasha ce miki shegiya ashe ban sani ba nice ma shegiyar..
lkc yayi da kema zaki rama duk abnd nayi miki sbd kinfini komai, wlh nusaiba kinfi karfina gaba da baya."
nusaiba ta jawota kan kujerar tasa hannunta ta goge hawayen dake zuba a idanunta ckn grgz kai tace "ki daina cewa haka sbd abu ne da bazai taba faruwa ba har abada, kinfi karfin na wulakantaki har abada.
Ke y'ar uwata ce zan fadi haka a hnkl ko kuma da karfi, anan ko kuma a ko'ina bana shayi.
Kada wannan lbrn yasa kiji wani abu sbd dama ba wanda ya koreki kuma ba wanda zai koreki har abada. Kalli.....!"
ta fada tare da yin nuni da momi tace "wannan itace mahaifiyarki ita ta shayar dake ta raineki har zuwa girmanki".
Tayi nuni da Abba tace "wannan kuma shine mahaifinki ki fada a ko'ina kada kiji komai sunanki FARIDA JAMIL ba wanda ya isa ya canjashi daga haka."
farida ta sake fashewa da kuka da sauri suka rungume juna ita da nusaiba. Bayan kamar min2na 15 ne komai ya dawo dai-dai, har yanzu nusaiba, farida da usman zaune suke a kujerun dake jere suna fuskantar kujerun da abba da momi ke zaune.
Nusaiba tace "ka gani ko abba?? Wani sirrin boyeshi bashi da wani amfani, da ace an fada mana yadda abin yake da mun dade da zama zuri'a me cike da so da aminci amma ina fatan yau ta zama ranar karshe ta bakin ciki a wannan gdn.
Abba kuma ina rokon alfarma daya don Allah!" da sauri yace "wace irin alfarma y'ar amana??"
idonta ya ciko da kwallah tace "ina so kakai ni kabarin mahaifana koda sau daya ne tak! Don nayi musu addu'a." farida ta dubeta tace "zan rakaki muje tare."
to y'ar uwata.
Nusaiba ta fada.
Usman yayi saurin yin nuni da hannunsa yace "nima zanje."
A karon farko fuskokinsu dukka suka fadada da murmushi..
Abba yayi murmushi yace "to yar amana zan kaiki ko yanzu kike so zan tashi mu tafi."
tayi saurin grgz kai tace "A'a ba yanzu ba duk sanda ka samu dama zamu tafi, amma abba baka ce komai ba don Allah kace ka yafe mata."
ya grgz kai yace "ni bata yimin laifin komai ba amma dai hkn izinah ne a gareta da duk me sha'awar hali irin nata."
nusaiba tace "momi fa baki ce komai ba!!" ta kada kai tace "to me zance??
Shiru ma ai magana ce musamman a irin wannan yanayin."
duk sukai dariya, nusaiban ta juyo ga usman tace "saura kai! Kai kadai kaji lbrnmu da tarihin rywrmu Don Allah ka rike mana sirrinmu."
yayi murmushi yace "nima ai dan gdn nan ne ko kin manta ne??
Idan zan tona sirrin gdnnan ashe zan iya tona nawa asirin kenan??
Sanin haka yasa abba ya yarda dani tayaya zanyi wasa da wannan damar. Abba ya mike tare da takawa kadan yace "idan ka samu dama ka 2romin iyayenka zamuyi magana dasu."
usman yadan juyo suka hada ido da nusaiba sukayi murmushi a tare ya juyar da kansa yace "ka shirya zuwansu a gobe ma sbd a yau dinnan zan tafi kaduna."
abba ya gyada kai kawai yace "kana da sa'a tunda na dauki kadara mafi girma na baka.."
yana me nufar dakinsa ya karasa zancen da cewa "amma kabi a hnkl ka kuma kula da ita sbd akanta zan iya fada da kowa, kai! Zan iya yaki da uban kowa a duniyar nan."
dukkansu suka rufe bakinsu sai daya shige dakin suka tuntsire da dariya, momi ta mike tare da cewa "to sai ka shirya kadai ji."
ta wuce tana dariya.
Zuwa can farida tadan gyara zama ta dubi usman tace "yauwa yayana ina neman yafiya sbd kana daya daga cikin wadanda na batawa a baya da kalamai marasa dadi don Allah kayi hkr, ban manta da shawarar daka bani ba kuma zanyi amfani da ita.
Yayi murmushi yace "karki damu kanwata ya riga ya wuce, kuma wulakanci da girman kai kawai zaki daina amma banda jan ajin nan sbd abin birgewa ne.
Duk sukai dariya.
Ya mike tare da cewa "to nima fa tfy zanyi sbd akwai bbr tfy a tare dani kaduna one way from here."
farida tace "to Allah ya tsare sai ka dawo." ya gyada kai kawai yayi waje.
To kije ki raka shi mana.
Farida ta fada sanda ta zungureta byn ya fita, nusaiba tayi murmushi kawai ta mike ta bi bayansa.
Dai-dai sanda ya isa jikin motar tashi dake a faffadar hrbr gdn ne ta karaso tare da cewa "wai da gaske kadunan zaka tafi??"
uhm! Wlh can zan tafi.
Ya fada sanda ya dubeta.
Ta tabe baki tace "amma kai dai ka fiye gaggawa wlh."
ya gyada kai yace "eh! Indai akanki ne abnd yafi gaggawa ma zanyi."
ta kauda kai tace "towai ma kaje kace musu me??"
yayi murmushi tare da dora hannunsa daya akan saman motar yace "Ahh! Nace musu na samu y'ar amana mana".
Tayi dariya tare da ja da baya tace "to Allah ya bada sa'a."
"ameen" ya amsa tare da bude kofar motar tasa ta zunburo baki tace "kuma ba zaka cemin 'sai na dawo' ba??"
yayi murmushi yace "to sai na dawo".
Tayi dariya tare da cewa "To Allah ya dawo min dakai lfy."
yayi dryr shima tare da shigewa motar tasa ya juya yabar harabar gdn bynda ya daga mata hannu, har sai daya fice sannan ta juya ta koma izuwa ckn gdn. Gaba daya farin cikin duniyar nan ya gama tattare mata yau, ji take kmr anyi mata albishir da aljanna.
*Zaune suke su biyu a falon sun hade rai kmr an aiko musu da sakon mu2wa, tana shigowa momi ta mike tare da cewa "ke nusaiba gdn uban wa kika je??"
tayi shiru kawai bakinta na rawa, farida dake gaf da momi tace "ba magana akeyi miki ba??"
ckn rawar murya tace "usman.. Na raka ya tafi.."
wa kika tambaya zaki rakashi?? Zo nan.
Momi ta fada ckn tsawa " a hnkl ta tawo jikinta na rawa ta tsaya a gbnsu.
Farida ta zaro ido gami da nuna y'ar amana tace "kin ganta sai wani kyarma take."
duk suka fashe da dariya tare da rungume juna ckn farin ciki da nishadi.
*** ¤¤¤ *** ¤¤¤ **** ¤¤¤ ****
Karshe.
ALHAMDULILLAH!!Mun kammala da wannan fatan an nishadantu gdy me yawa ga masu bibiyata tun daga farko har zuwa karshe, sai mun hadu a wani lkcn kuma.