******* Y'AR AMANA *******
Part 14
NA Abubakar A. Muh'd
bana jin yana da wani amfani muyi hakan sbd komai na aro abin banza ne, kuma sirri baya taba rufuwa har abada dole wataran sai ya fasu anji me kike 2nani idan muka riki da na tsawon lkc daga baya ya fhmc bamu muka haifeshi ba??
Dole zai juya mana baya ne.
Tadanyi tagumi tace "amma bana jin akwai wani abu a ciki idan ka duba ba wani wanda yasan rywrmu idan basu lubabatu ba kuma bamu da matsala dasu, indai har zaka goyi baya nidai ina son muyi hakan."
na grgz kai nace "kiyi hkr amma wannan ba mafita bace a garemu."
bata so naki yarda ba amma kuma sai bata bari munyi doguwar jayayya ba tace "to shikenan ci abncn ko??
Kada ya huce da yawa."
na kllta kawai tare da mayar da kaina ga abncn, tadan kura min ido kadan ta mike ta koma ga aikinta.
Wannan shine masomin fadawa damuwarta, tun daga wannan ranar murmushi ya ragu a fuskarta, koda yaushe ka kllta damuwa ce kawai zaka karanta a rubuce kuma karara a fuskar tata.
Nasan dlln hkn baya rasa nasaba da maganar da mukai shi yasa ban taba tmbyrta ba, abin nata kuma sai ya zamana kllm gaba yake ba illa idan ta kalli y'ar su alhaji inusa wato nusaiba ko kuma wasu y'an kananan yaran damuwarta kan kara fitowa fiye da kowanne lkc.
Akwai ranar dana farka tsakiyar dare misalin karfe 2:30 na dare tana zaune bisa gefen gado ta juya tana me fuskantar kofar fita hwy ne kawai ke zuba a idonta, a hnkl na mike zaune nabita da kll kawai.
Zuwa can na matso na zauna gaf da ita nima na kalli inda ta kalla nace "me yasa kika tashi tsakiyar dare kika zauna maimakon ace kina barci??
Me yasa kike kuka kuma??" sai sannan ta dawo daga 2nanin data tafi ta kllni ta mayar da kanta tace "kafi kowa sanin dll ai, kuma duk duniya kai kadai ne zaka iya share min hawayena."
tayaya?? Na tambaya.
Ta dubeni tace "ka yarda mu samo dan da zamu rike don Allah! Ina da burin naga d'a ko y'a a hannuna, nayi masa duk abnd uwa ke yiwa danta nima naji cewa kmr sauran mata nake ba wata daban ba."
na dan kawo gwauron numfashi ba tare da nace komai ba zuwa can nace "abnd nake so ki gane shine dan wani baya taba zama naka musamman ma a rashin dll, gdn marayun nan da kike maganar muje a bamu d'a mu rike mafi yawancin jariran gdn ba bata hanya me kyau aka samesu ba. Bamu san tayaya aka samesu ba..
Ko kuma yadda akai da dalilin da yasa aka kawosu nan!! Wannan dlln bazai iya barina na nunawa dan syyr data kamata dashi ba, kiyi hakuri mu jira ikon Allah wata kila sai kiga Allah ya kawo mana wani juyin da zamu samu namu nakanmu ko kuma dai wata kyauta daga Allah.
Ta dauke kai daga kllna tace "abune mawuyaci kaga tsammani yazo yadda aka fada ko kuma ya zama gaske, ina son mu kama abnd yake dahir ne ba gaibu ba."
na kllta nace "toni gsky bana so muyi haka".
Itama ta dubeni tace "ni kuma gsky ina so muyi haka."
na bita da kll kawai naja da baya na koma na kwanta sai dai ina! Baccin ma kin zuwa yayi sbd ko kadan bana son ganin damuwarta, tunane-tunane ne masu yawa ke kaiwa da komowa a ckn raina a wannan lokacin.
Washe da safe muna zaune muna breakfast misalin karfe 9:00 sai dai ba kmr daa ba sbd ba wata hira dake gudana a tsakaninmu, zuwa can ta ture abubuwan dake gbnta ta mike."
caraf! Na rike hannunta. Ta juyo ta dubeni kawai.
Dawo ki zauna muyi magana. Ba tare da musu ba kuwa ta zauna.
Na gyara zama nace "na lura kin damu ma2ka akan abnd kike abnd kike so wanda ni kuma ba haka naso mana ba, naso ace mun hkr munga abnd Allah zaiyi amma 2nda kin matsu da yawa ni kuma Allah ya sani bana son na rinka ganinki a damuwa makamancin wannan.
Na yarda kije gdn marayu kuyi yarjejeniya dasu su baki jaririn da zaki rike a matsayin naki.."
da sauri ta dago kai tare da sakin fuska tace "da gaske??"
na gyada kai nace "kwarai sbd na fahimci shine kawai abnd zanyi miki ki samu farin ciki, sai dai akwai nima abnd nake so ki sani guda daya."
gyara zama kawai tayi, nace "d'an da zaki dauko ko y'a ki sani ba nawa bane da gaske, zanyi masa iya abnd zan iya ne kawai amma ba lallai ya samu kulawar da yakamata daga gareni ba."
ta kada kai tare da cewa "zaima samu sbd nafi kowa sanin halinka, tausayinka da kuma sadaukarwarka..."
karki dogara akan haka sbd nafi kowa sanin kaina duk duniya, abnd nake so kisa a ranki shine baki da bakin yimin korafi idan na kasa baiwa abnd kika dauko kulawar data dace, kin yarda?? Na tambaya ina dubanta.
Ba tare da fargabar komai ba ta gyada kai tare da cewa "na yarda."
na bita da kll kawai nace "shikenan ni yau zanje garin kano alhaji yayi min waya na sameshi acan kinsan baya jihar nan??
idan zaki je sai ki samu taxi yakaiki kuyi mgn da mahukuntan gdn marayun idan da yiwuwa kuyi yarjejeniya dasu ki samo mana kiyi amfani da kudina dake hnnki nasan dole za'a bukaci kudi, Allah ya bada sa'a."
sbd jin dadi har wani ciccilla hannu tayi daga zaune tace "amin ngd sosai mijina". Haka Muka danci gaba da hira jefi-jefi.
¤ tfyr da nayi a ranar tasa ban dawo da wuri ba sai misalin karfe 9:00 na dare, kai tsaye byn dana sauka daga mota a harabar gdn na zarce izuwa ckn gd.
Zaune take bisa ktwr darduma ta tankwashe kafarta tana rike da jaririya cikin lallausan zani launin fari ta kura mata ido, nayi turus kawai sai ynz na 2no da hkn. Motsina taji ta dago kai, nace "an samo?? Mace ko namiji??"
da sauri tace "macece y'ar wata uku a duniya."
na taka tare da duban jaririyar dakyau nace "ya sunanta??"
ta bani amsa da fadin "FARIDA!!" Na gyada kai nace "Allah ya raya!!" ban jira komai ba na wuce dakina, har ga Allah ba haka naso ba.
Wannan shine labari dangane da samuwar FARIDA da yadda akai tazo hannunmu..
Topah yau akeyinta sora NUSAUBA KEnan??
Abba ya fada sanda ya yabi dukkansu da kallo ganin yadda suka grgz dajin abin, idanun na nusaiba a waje suka hada ido shi kansa usman alamun mamaki karara sun byyn a fuskarsa.
Abba yace "nayi iya kokarina naga na manta da asalinta kodon nayi mata son da uba keyiwa dansa amma na kasa, duk da haka nayi iya kokarina ban taba tauye mata wani hakki na wajibi ba.
Sannan shine dalilin da yasa hajiya ke ma2kar kaunarta kuma take bata kulawa ta musamman sbd tun asali ita ta daukota.
2n kafin yakai haka a jawabin da yake yi caraf hannun farida ya dare bisa kanta rikitattun hwy suka kwararo mata bakinta ya fara rawa, ko ba'a fada maka ba kasan dole ta grgz don ba haka tayi zato ba.
Abba ya kwantar da kansa jikin kujerar tare da cewa da dorawa.
*haka muka cgb da tfy har izuwa sanda Allah ya aiko da kaddarar data janyo mana samuwar y'a ta biyu a garemu. Bayan watanni biyu da faruwar haka ne ranar wata talata misalin karfe 11:00 na safe, kmr yadda a wasu lktn muka saba zaune muke mu uku a bbn falon gdn zaune bisa kujeru muna hira ckn nishadi da walwala.
Ni da iyami sai kuma matar Alhaji inusa wato lubabatu dake can gefe zaune.
Iyami ta dago kai ta dubi lubabatu tace "wai kuma idan kun tafi sai yaushe kenan??"
tadan tabe baki tace "uhm! Bafa wani nesa bane yanzu zamu dawo kinganshi ma ya shige daki yaki fitowa mu tafi."
to ina nusaibar kuma?? Iyami ta sake tambaya.
Tana ciki tare zasu fito dashi amma fa bada ita zan tafi ba anan zan bar muku ita sbd rigimarta yawa gareta.
Na bisu da kll nace "toke amina sai ki shirya yara biyu gareki yau.." Amina?????
Lubabatu tayi saurin tmby tare da cewa "dama sunanta amina??"
nayi dry nace "Eh! Sunanta Amina ko don kinji ana ce mata iyami??"
ta kada kai tare da cewa "yanzu naji suna meye wani iyami??
Kai mutanen kauye akwai bata suna wallahi."
ta zarce da dariya.
Dai-dai lkcnne ya fito daga ckn dakin sanye da irin shigar daya saba manyan kaya da malin-malin gami da hula, y'ar karamar kyakykyawar y'arsu nusaiba na rike a hannunsa.
meye kuma kuke ta dariya ne??
Ya tambaya dai-dai sanda yake zama.
Ta dubeshi da sauri tace "kaji ashe wai sunanta amina."
shima yayi dry yace "to tunda ynz ta baro karkara ai sai a daina gaya mata iyami a koma gaya mata sunanta na gaske, HAJIYA AMINA."
tayi saurin cewa "a tsaya a iya aminar dai amma ai ban je hajji ba."
duk muka sake yin dariya.
Ya mike tare da cewa "sai ki tashi mu gaggauta tfy ko??"
ya fada yana duban lubabatu.
Ta dan kada kai ta mike tare da ce masa "to! Amma fa nusaiba tana nan bada ita zamu tafi ba."
yabita da kll yace "me yasa???"
ta mirgina kai tace "kasan rigima ce da ita kuma ma bai kamata na tafi da goyo ba.."
to naji ai ba wani abu nace ba idan kin barta anan din ma ai duk abnd zakiyi mata za'ai mata.
Suka mike dukkansu nayi saurin duban yarinyar na bude hannayena nace "nusaibata tawo.."
takwa rugo da gudu na cafeta.
Sukai amfani da damar hakan suka fice byn da muka yi sallama, muka cgb da hira ckn walwala.
BAYAN AWA BIYU.
Har yanzu zaune muke a falon iyami na zaune rike da yara biyu tana ta fama, idanuna nakan faffadar television din dake manne a jikin bango ina klln wani shiri.
Wayata tadau kara wanda ke nuni da shigowar sako, na zarota daga aljihuna na karata kai tsaye izuwa kunnuwana byn danayi murmushi ganin lambar alhaji inusa ce.
Helloooo!!! Na fada.
Hello! Yauwa kasan me wayar nan aiko?? Aka fada.
Nayi saurin daga kai nace "eh! eh! Nasan shi lfy dai??"
me kiran yadanyi shiru jim kadan yace "kazo asibitin S. GIDADO yanzu."
idanuna suka zaro waje wuf nayi na mike tsaye da tambayar "asibiti??
Me ya faru?? Lfy kuwa??"
kazo dai! Sun sami accident ne.
Abnd aka fada kenan aka kashe wayar.
Sbd grgz wayar subucewa tayi daga hannuna na runtse ido sbd ji nayi kaina na jujjuyawa kmr zan zube a kasa.
"innalillahi wa inna lillahir raji'un" na fada ba shiri.
A hnkl ta bini da kll tare da ajiye yarinyar dake hannunta tace "lfy kuwa??"
dakyar a rikice na iya cewa "su alhaji ne sukayi hatsari... Yanzu haka suna asibiti."
a gigice ta mike gami da dafe kirji gami da maimaita abnd na fada ta dora hannu aka.
¤ba shiri muka bazama kai tsaye izuwa asibitin a mota, muna tafe iyami nata rusa kuka kmr ranta zai fita ban ma samu nutsuwa ba bare na iya bata hkr.
Da saurinmu muka isa ckn asibitin mukai tambaya aka sadamu da dakin gaggawar da aka kwantar dasu, sai dai muna zuwa mukayi turus a bakin kofar dakin ganin wadanda ake fitowa dasu daga ckn dakin a irin gadon nan na daukar gawa.
Kmr wanda aka zarewa laka haka na karasa dai-dai sanda ake fitowa dasu, nasa hannuna na yaye farin likkafanin da akasa wanda ya rufe jikinsa 2n daga kasan kafarsa har izuwa kansa nayi arba da fuskar Alhaji inusa.
Nayi saurin rufe fuskar tasa hwy suka kwararo min na dora hannayena aka, iyami kuwa tana ganin haka ta sulale kasa sumammiya.
Hkn yasa hnklna dana wasu daga cikin ma'aikatan asibitin suka yo kanta aka wuce da ita dakin duba marasa lfyr.
Bayan kamar awanni biyu ne ta farfado tana dagowa muka hada ido ina zaune a bakin gadon, ta sake fashewa da kuka tace "shikenan sun mutu ko??
Sun tafi, duk gatanmu ya rushe ko??"
dakyar na rarrasheta tadan sami nutsuwa.
¤¤kafin rasuwar alhaji ya bada wasiyar cewa ni yake so na rike y'arsa da duk dukiyarta sbd ya yarda dani fiye da kowa a duniya, haka kuwa akai bayan kwanaki arba'in aka damka nusaiba da mafi yawan dukiyar da alhaji ya mu2 ya bari wacce gadon nusaiba ce.
Shine dlln da yasa na lakaba mata sunan Y'AR AMANA sbd itace mafi grmn amanar da aka taba damkawa a hannuna.,
tafaru taqare anyima me dami 1 sata...