Wasu 'yan kunan bakin wake da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun yi sanadiyar mutuwar mutane 22 a yayin da suke kan gudanar da ibada a wani masallaci a safiyar yau Laraba a garin Maiduguri, inda kuma 35 suka samu rauni.
Majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito cewa bama-baman guda biyu sun tashi ne a cikin wani masallaci dake wata unguwa da ake kira Umurari Molai dake yankin Maiduguri
'Yan kunar bakin waken sun shigo masallacin ne a lokacin da ake kan gudanar da ibada, inda suka tada bama-baman da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Wata mace 'yar kunar bakin wake da ta yi shigar maza ita ta dasa bam na farko a cikin masallaci, yayin da kuma daya ta tsaya a waje. Inda a yayin da na farkon ya tashi mutane suka kawo dauki, sai ita ma ta tayar da nata.
Kasancewar an gano sassan mace daga cikin mutanen da suka rasa ransu, hakan ya tabbatar da cewa mata ne suka dasa bama-baman.
Title :
Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutane 22 A Wani Masallaci A Jihar Borno
Description : Wasu 'yan kunan bakin wake da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun yi sanadiyar mutuwar mutane 22 a yayin da suke kan gudanar da ibada ...
Rating :
5