Rahotanni sun nuna cewa barayi sun sace wayar babban sakataren Majalisar Musulmai ta duniya dake Saudiyya, Dakta Abdullahi Bin Abdul, kamar yadda majiyarmu ta The Nation ta rawaito.
Jami'an tsaro wadanda suka nuna rashin jin dadin su game da aukuwar hakan, yanzu haka suna kan gudanar da bincike domin gano wanda ya yi satar.
Majiyarmu ta gano cewa shi kansa babban bakon da aka sace masa wayar ya nuna damuwarsa kan aukuwar lamarin.
Bincike ya nuna cewa Bin Abdul shi aka nada domin jagorantar sallar Juma'a a babban Masallacin Abuja a ranar Juma'ar da ta gabata. Don haka ne aka sanya masu matakan tsaro da yawa.
Bayan sallar Juma'ar, Malamai da dama da sauran wadanda suka gudanar sallah a masallacin sun yi kokarin kusantarasa, wanda hakan ya sa jami'an tsaron suka yi kokarin hana su. Wanda a dalilin haka ne daga bisani babban bakon ya gano cewa an sace masa waya a wannan rububin.
Saidai wasu dake wurin a lokacin da lamarin ya auku, sun bayyana aukuwar hakan a matsayin abin kunya ga kasar Nijeriya baki daya, kasancewar baki ne wadanda suka shigo Nijeriya da nufin gudanar da taro kan harkokin Musulunci.
Saidai jami'an tsaro sun sha alwashin bankado wadanda suka yi satar, duk da cewa har zuwa yanzu babu tabbacin ko an kama wasu da ake zarginsu da aikata lamarin.
Bincike ya nuna cewa kafin aukuwar lamarin, barayi sun kwashe wasu sassa na na'urar kwamfutar dake cikin ofishin majilisar kololuwa ta harkokin Musulunci ta kasa (NSCIA) dake cikin maallacin. Wanda hakan ya sa majalisar korar wasu kungiyoyin da ke kusa da ofishin.
Title :
Wayar Sakataren Majalisar Musulunci Ta Duniya Ta Yi Layar Zana A Masallacin Abuja
Description : Rahotanni sun nuna cewa barayi sun sace wayar babban sakataren Majalisar Musulmai ta duniya dake Saudiyya, Dakta Abdullahi Bin Abdul, kamar...
Rating :
5