Mazauna unguwar Gbaure,da ke yankin Gwagwalada,a birnin Abuja sun wayi gari da wani tashin hankali,Inda aka kashe wani matashin dan acaba mai suna Nura dan kimanin shekara 28 ya rasa ransa.Al’amarin ya faru ne,bayan da matashin da wasu abokansa guda biyu su ka sace wata budurwa,mai suna Binta Ali.A sirinsu dai ya tonu ne,lokacin da mahaifin Yarinyar ya Kai rahoton ga “yan bangar yankin, Wanda su ne su ka samu nasarar gano inda su ka boye ta,tare da mika su wajen “yansanda.Sai dai jimkadan da tsare su aka sallame su,al’amarin da ya yi matukar batawa kungiyar sintirin rai.
Wani mazaunin yankin,ganau ba jiyau ba,malam musa Shehu,ya ga yawa mujallarmu cewa,lokacin da “yan sintirin su Kai ido hudu da wadancan samari, sai su ka fara gayawa juna maganganu,Wanda a karshe ta janyo rigima,da ya haddasa rasuwar daya daga cikin matasan, wato Nura.
Mujallarmu ta nemi jin ta bakin mahaifin matashin, amma ya ki cewa komai,haka shi ma baturan “yan sandan yankin bai ce kala ba.
Wakilin mu Kabiru Inuwa,Hayinhago
Sources mujallarmu
Title :
Wata Budurwa Ta Sa An Kashe Wani Dan Acaba
Description : Mazauna unguwar Gbaure,da ke yankin Gwagwalada,a birnin Abuja sun wayi gari da wani tashin hankali,Inda aka kashe wani matashin dan acaba ma...
Rating :
5