Sojoji Sun Sake Kakkabe Sansanin 'Yan Boko Haram, Inda Suka Kashe 58 Daga Cikin 'Yan Ta'addan
A ci gaba da kokarin da dakarun sojojin Nijeriya ke yi na ganin sun kawo karshen 'yan ta'addar Boko Haram, dakarun 153 na Task Force Brigade da 5 Brigade a jiya Litinin sun fafata da 'yan Boko Haram a wani kauye da ake kira Musari a jihar Borno.
A yayin fafatawar sojojin sun taka rawar gani, inda suka kashe 'yan bindigan guda 58 tare da kwato makamai da babura guda 52 da kuma buhunhunan kayan abinci da suka hada da na wake, albasa dankali da gero da kuma kwalayen kifi.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin rundunar, Kanal Sani Kukasheka Usman.
Title :
Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Boko Haram 58 A Kauyen Musari
Description : Sojoji Sun Sake Kakkabe Sansanin 'Yan Boko Haram, Inda Suka Kashe 58 Daga Cikin 'Yan Ta'addan A ci gaba da kokarin da dakarun s...
Rating :
5