Rahotanni da muke samu daga majiyoyi masu yawa na cewa rundunar sojan Nijeriya sun hana 'yan Shi'a yin wani taro da suka shirya yi a birnin Katsina.
Bayanai sun ce 'yan Shia sun shirya yin taron ne a kofar babban masallacin Katsina wanda yake gab da gidan sarki.
A safiyar yau sojoji suka zo gun taron inda suka kwace tutoci da wasu kayan fara taron kamar yadda labari ya riske mu.
A bangaren 'yan shia kuma sun yi zargin cewa sojoji na shirye-shiryen kai musu hari a daren yau bayan sun hana su taron da suka kira yau.
Title :
Sojojin Najeriya Sun Hana 'Yan Shi'a Yin Taro A Katsina
Description : Rahotanni da muke samu daga majiyoyi masu yawa na cewa rundunar sojan Nijeriya sun hana 'yan Shi'a yin wani taro da suka shirya yi ...
Rating :
5