SHIN MUTUM NAWA KAYI MA ADDU'A AYAU?
*************************************************
Yin addu'a ga iyaye wannan WAJIBI NE. Allah ne ya fada acikin Littafinsa mai girma. To amma ko kasan cewa yin addu'arka ga sauran 'Yan uwanka Musulmai wata babbar hanya ce ta samun biyan bukatunka da yayewar damuwarka??
SAYYIDUNA ABUD DARDA'I (RA) yana daga cikin Manyan Sahabban Manzon Allah (saww). Tun da yaji wani hadisi daga Manzon Allah (saww) yana cewa : "Addu'ar Musulmi ga 'Dan uwansa Wacce yayita a'boye karbabbiya ce".
Matarsa Ummud Darda'i tace Tun daga wannan ranar ya kasance idan ya dora goshinsa a Qas (cikin Qiyamullaili) yakan ambaci sama da mutum dari uku (300) daban daban, yana yi musu addu'a.
"Ya Allah ka gafarta ma wane"
"Ya Allah ka azurta wane"
"Ya Allah ka aurar da wance"
"Ya Allah kayi ma wane kaza-da-kaza".
"Ya Allah ka bama wane lafiya".
Wannan yana nuna mana yadda Sahabbai suke kaunar junansu. To mai zai hanamu mu rika yin haka?
Lallai ya kamata muyi amfani da wannan damar domin mu yawaita addu'a ga 'Yan uwanmu Musulmi wadanda suke cikin matsalolin rayuwa. Da wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.
Acikin wani Sahihin Hadisin Manzon Allah (saww) ya tabbatar mana da cewa Akwai wani Mala'ikan da yake zuwa ya tsaya akusa dakai duk yayin da kake yima sauran musulmai addu'a.
Wannan Mala'ikan yana cewa "AAMEEEN KAIMA KANA DA MISALIN IRIN WANNAN". (ma'ana Kai ma Allah ya baka irin abinda ka roka ma sauran musulmai).
Idan ka damu da damuwar 'Yan uwanka sai Allah ya yaye maka taka damuwar. Allah zai taimaki bawansa, Mutukar shima bawan yana cikin taimakon 'Yan uwansa.
Amma yanzu zaka ga (Musamman Matasa) Mutum ya idar da Sallah, ya tashi TSALAK!! Bai tsaya yayi Zikirin Allah ba, ballantana yayi ma kansa addu'a Ballantana iyayensa ko 'Yan uwansa.. Kuma idan ya fita daga nan, harkar duniya marar amfani zai tafi. Watakil ma Majalisa zai tafi wajen hira da abokai.
'Yan uwa ya kamata mu gyara halayenmu. Mu rika yin nachi wajen addu'ar alkhairi ga kanmu da iyayenmu da 'Yan uwanmu da dukkan Musulmai maza da mata baki daya. Musamman Shugabanninmu na Mulki da na addini. Dukkansu suna bukatar addu'armu.
Title :
Shin Mutum Nawa Kayi Ma Addua A Yau
Description : SHIN MUTUM NAWA KAYI MA ADDU'A AYAU? ************************************************* Yin addu'a ga iyaye wannan WAJIBI NE. Allah...
Rating :
5