Kiyayewa da gyaran nono wani lokacin yana iya zama wajibi awajen mace tun tana budurwa musamman awannan lokacinda maza da dama suke bukatar hakan...
Namiji yanason mace me gyara nononta musamman lokacinda mace tayi yaye don lokacinne nono yake kwanciya ta yanda wani ya tafi kenan bazai dawoba kuma kyakyawana nono a wajen mace ba karamin muhimmaci yake dashiba
Akwai mata wadanda sunsha jarraba maganinda zai gyara musu nono kala kala amma shiru babu wani canji wasu har matsala yake jawo musu kuma gaskiya akwai rashin sanin lokacinda mace zata gyara nono da kuma hanyoyin gyaran da kuma maganinda zaisa nono ya gyaru...
LOKACIN GYARA NONO...
Tun kina budurwa zaki fara kiyaye nononki wato kamar yawan tsalle ko daurin kirji da zani ko kuma mummunan kwanciya wanada zaki dannesu sannan akwai rigar nono (brezy) itama dole kisan wanda ya kamata kisaka wato wacce bazata matsesuba da dai sauran abubuwanda zasu wahalarda su
to idan kika kiyaye wannan har lokacin aurenki nononki zai kasance a tsaye yanda oga zai rude
Lokacinda kika zama matar aure saboda saduwar jima i da sauran uzirin mijinki a wajeni nononki zai rinka karuwa yana kwanciya to wannan lokacin zaki rinka daukar ingantattun magunguna na gargajiya Wanda zasu karawa nononki kyauwu wannan duk muna bayaninsu a posting dinmu to bayan kin haifu kuma zaki iya rabuwa da kowanne magani kedai kirinka shan abubuwanda zai karawa nononki ruwa kamarsu nonon saniya ko madara peak ko luna ko yougut ko garin madara kika jika da ruwa kika zuba garin zogale kikasha zai miki amfani ko kunun kanwane zaki iyasha ya danganta da yanayin wadatarda kike dashi har lokacinda zakiyi yaye zakiga nononki da ruwa sosai to bayan kin yaye sai kuma kiyi gyara na masuyin yaye shine zakiga kinayi kinyi nasara kuma za a dade ana miki kallon budurwa kuma zakiga yanda zaki samu kulawa da soyayya awajen mijinki kinga babu maganar kishiya a gidanki.
Title :
Shawarwari Akan Gyara Nono
Description : Kiyayewa da gyaran nono wani lokacin yana iya zama wajibi awajen mace tun tana budurwa musamman awannan lokacinda maza da dama suke bukatar ...
Rating :
5