Sojojin Sun Kakkabe Sansanin 'Yan Boko Haram Dake Kala Balge
*Sun Kashe 'Yan Ta'addan Guda 25 Tare Da Ceto Mutane Sama Da 800
A kokarin da dakarun sojojin Jijeriya suke na ba date ba rana don ganin sum kawar da 'yan ta'adsan Boko Haram daga yankin Arrwa maso Gabas, a ranar Talatar da gabata dakarun bataliya na 3 da na 22 Brigadia da sauransu, sun yi nasara kakkabe sansanin 'yan ta'addan dake garin Kala Balge a jihar Borno.
Baya ga kuma kashe 22 daga cikin 'yan Boko Haram din da sojojin suka yi, sun kuma yi nasarar fatattakar su daga maboyar su dake kauyukan Wumbi, Tunish, Tilem da Malawaji. Sauran kayukan sun hada da Makaudari, Daima, Buduli, Sadigumo, Jiwe, Sidigeri da Kala. Haka kuma sojojin sun ceto mutane 309 daga wurin 'yan bindigan.
Haka kuma sun tarwatsa wurin da 'yan ta'adddan suke atisaye da kuma inda suke kera makamai a kauyen Tilem dake karamar hukumar Kala Balge.
A wani labari makamancin haka ma, dakarun bataliya ta 3 da kuma taimakon 'yan bangan sa kai sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram guda uku tare da kama daya da ransa, a kauyen Kusumma
Sun kuma ceto mutane 520 daga wurin 'yan ta'addan tare da kwato babur daya da makamai.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kakakin rundunar, Kanal Sani Kukasheka Usman.
Sources Rariya
Title :
Photos: Sojojin Najeriya Sun kashe Yan Boko Haram 25 Tare Da Ceto Mutane Sama Da 800
Description : Sojojin Sun Kakkabe Sansanin 'Yan Boko Haram Dake Kala Balge *Sun Kashe 'Yan Ta'addan Guda 25 Tare Da Ceto Mutane Sama Da 800 ...
Rating :
5