A wani artabu da aka yi tsakanin dakarun sojojin Nijeriya da 'yan Boko Haram a jiya Asabar, sojojin sun yi nasarar kakkabe sansanin 'yan bindigan tare da kashe wasu da dama daga cikinsu.
Kafin nasarar da sojojin suka yi kan 'yan ta'addan, sun mamaye yankunan Jango, Dibiye da Dure, inda suke yawan kai farmaki ga mazauna wadannan yankuna.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kakakin rundunar sojojin, Kanal Sani Usman Kukasheka, inda ya kara da cewa jami'ansu suna ci gaba da samun nasara akan 'yan ta'addan.
Title :
Photos: An Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama A Jihar Borno
Description : A wani artabu da aka yi tsakanin dakarun sojojin Nijeriya da 'yan Boko Haram a jiya Asabar, sojojin sun yi nasarar kakkabe sansanin ...
Rating :
5