Sakataren kwamiti kan tallafin man fetur a majalisa, Boniface Emenalo a yau Litinin ya bayyanawa babban kotun tarayya dake Lugbe, Abuja yadda ya karbo dala dubu dari daga wurin Femi Otedola a shekarar 2012, a matsayin wani kaso daga cikin dala milyan ukun da ya yi alkawarin baiwa shugaban kwamitin na wancan lokacin, Honarabul Faruk Lawan a matsayin cin hanci.
Idan ba a mance ba, a shekarun baya Hukumar ICPC tana zargin Faruk Lawan da laifin karbar dala dubu 500 daga cikin cin hancin dala milyan ukun da ya bukata daga wurin Otedola da nufin kwamitin majalisar ta cire sunan kamfaninsa daga cikin kamfanonin da suka adawa da janye tallafin mai a shekarar 2012.
Emenalo dai shine shaida na farko da ya soma gabatar da kansa a gaban mai shari'a Angela Otakula a yau Litinin kan tuhumar da ake yi wa Faruk Lawan din.
Source Rariya
Title :
Na Karbowa Faruk Lawan Dala Dubu 100 Daga Wurin Otedola,- Emenalo
Description : Sakataren kwamiti kan tallafin man fetur a majalisa, Boniface Emenalo a yau Litinin ya bayyanawa babban kotun tarayya dake Lugbe, Abuja yadd...
Rating :
5