Wani dan shekaru 50 mai suna Kamoru Oladele da rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta kama a jiya Litinin, ya bayyana yadda yake sayar da sassan mutum kan farashin naira dubu 25 ko dubu 30, inda ya kara da cewa suna da mayankar mutane a jihohin Oyo da Osun.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Leye Oyebade ya bayyana cewa jami'ansu sun yi nasarar kama mutumin ne bayan rahoton da suka samu.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa "ni mai bada magani ne. Ba ni nake sayar da sassan mutanen ba. A wurin mutane nake saye. Wannan shine karo na farko da tsinci kaina a cikin wannan sana'a. Ina sayan sassan mutum kan farashin dubu 10, sai ni kuma na sayarwa da wadanda suke bukatar yin tsafi da shi kan naira dunu 30".
Title :
Muna Da Mayanka Ta Mutane, Inda Muke Sayar Da Sassan Mutum Kan Naira Dubu 30
Description : Wani dan shekaru 50 mai suna Kamoru Oladele da rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta kama a jiya Litinin, ya bayyana yadda yake sayar da sa...
Rating :
5