Ana zaton wuta a makera sai muka ji duriyar tashinta a masaka. A 'yan shekaru biyu da suka wuce zamanin mulkin Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, Jihar Kano ta yi kaurin suna wajen mutunta 'ya'ya mata musamman 'yan mata da zawarawa ta hanyar shirin nan na Auren Zawarawa wanda gwamnan ya kirkiro ta hanun hukumar Hizba ta Jihar Kano wacce Mallam Aminu Daurawa ke shugabanta.
Wannan shiri ya yi nasarar Alaurar da 'an mata da zawarawa fiye da 2,500, domin kaucewa mummunar ta'adar nan ta yin cikin shege a kuma haihu a yar da 'ya'yan a bola ko kan titi dakuma dakile muguwar sana'ar nan ta karuwanci.
Gwamnatin Kanon ta wancan lokaci karkashin jagorancin sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, a da ta yi tunanin aurar da zawarawa 1000 ne kawai, amma daga baya gwamnan ya kara da 'yanata kuma ya kai adadin zuwa 3000 domin yanayin yawan matan da hukumar Hizba take kamawa a wuraren lalata kamar irinsu wajen Party, Gidan karuwai da sauransu, wannan shiri kuma ya yi nasara kwarai da gaske, saboda kafin gwamnan ya bar karagar mulki sai da ya tabbatar da ya aurar da Matan fiye da 2,500 tare da yi musu kayan daki da ba su jari kyauta.
A bangaren Matan aure kuwa nan ma Kwankwaso bai yi kasa a gwiwa ba ta yadda ya dinga raba musu jarin naira 10,000 karkashin hukumar nan ta CRC wacce ita kuma Alhaji Toranke ya shugabanta. Wannan shiri an gudanar da shi ne a kafatanin kananan hukumomi guda 44 dake jihar ta Kano, inda a kowanne watan duniya hukumar ta CRC tana daukar mata 100 daga kowacce karamar hukuma daya ta ba su jarin dubu goma-goma, sannan wasu matan a ba su awaki da kaji musamman na karkara su je su yi kiwo.
Gwari-gwari Kwankwaso ya baiwa mata dubu goma sha bakwai da dari shida 17,600 jarin dubu goma-goma a tsawon shekaru 4 da ya yi yana mulkin Kano, banda wadanda aka baiwa jarin kiwon awaki da kaji.
Sai dai a wannan lokacin na mulkin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje kamar yadda na fada muku ana zaton wutane a makera sai ta tashi a masaka domin kuwa ana zaton gwamnan zai dora wancan abun alkhairi na aurar da zawarawa da 'yan mata da kuma baiwa matan aure jari kyauta, amma sai ya dauki wata ta'ada da za ta zubarwa da matan kimarsu a jihar Kano.
Acikin wannan satin duk wanda ke wucewa ta filin sukuwa dake daura da Masallacin Alfuqaan dake Kano zai ga yadda ake koyawa mata tukin mota mai dibar ya shi wato Tifa da kuma manyan motocin nan masu aikin titi. Wai dabarar gwamna a nan ita ce yanzu maza za su daina dibar shara a Kano saidai mata.
Ma'ana mace ce za ta share titi kuma ita ce za ta hau babbar motar da za ta debi sharar ta zuba a cikin tifa. Har ila yau macen dai ita ce za ta tuka Tifar ta je bayan gari ta juye sharar a inda aka tanadar ta dawo.
Yanzu haka dai Gwamnatin ta ware zawarawa guda 500 da za'a fara koyawa wadannan motoci ala bashshi idan aka yi nasara sai a kara ware wasu 500 din suma a koya musu.
Jim kadan da rantsar da Gandujen ne dai ya yi shelar korar ma'aikatan shara na jihar Kano gaba dayansu, wannan ta sa tulin shara a Kano ya zamo tamkar jamfa a Jos.
Muna kira da Al'ummar Jihar Kano masu fada a ji kama daga Sarakuna, Malaman Addini, 'Yan Kasuwa, Kungiyoyi masu zaman Kansu da Manyan 'Yan siyasa da su yi kokarin dakatar da wannan gwamna daga yin wannan kasassaba ta bawa mata tukin manyan motoci, domin ba'ada bayan zubar da mutunci 'ya mace, Allah ne kadai ya san irin hadururrukan da wadannan mata za su haifar a Kano sakamakon tukinsu. Kuma kamar kullum zan yi kara kira ga shi gwamna Ganduje da ya yi kokarin canja masu ba shi shawara, ko Allah zai sa ya samu saukin tafka kwakyariya irin wannan.
Sources Rariya
Title :
Matsayain Zawarawa Da 'Yan Mata A Gwamnatin Ganduje
Description : Ana zaton wuta a makera sai muka ji duriyar tashinta a masaka. A 'yan shekaru biyu da suka wuce zamanin mulkin Injiniya Dakta Rabi'...
Rating :
5