Bayanai dake fitowa na cewa majalisar dokokin Nijeriya ta shirya yin fito na fito da shugaba Buhari kan rashin mutunta tsarin mulki Nijeriya da kuma yiwa majalisar karan tsaye.
Mambobin majlisar daga jam'iyyar adawa ta PDP sun bayyana cewa sun shirya wajen kare rantsuwar ofis da suka yi domin a cewarsu dun gama yiwa Buhari kawaici abinda ya rage shi ne fito na fito fn kare mutumcin majalisar.
'Yan majalisar sun bayyans wasu abubuwa da gwamnatin Buhari ta yisu gaba gadi wanda suka ce ba zasu lamunta ba kasantuwar sun saɓa dokokin Nijeriya.
'Yan majalisar sun ce Buhari ya riƙa naɗee-naɗen mukamai wanda a cewarsu ya kamata a sanar dasu don su sahale amma Bhari bai mutunta haka ba. Sun kuma ce hatta maganar rarraba kamfanin mai na ƙasa wato NNPC suma jarida suka gani kamar kowa saboda gwamnatin bata ganin girman majalisansu.
'Yan majalisar sun kuma koka da yadda Bahari ya sanya Nijeriya a kasashen musulmi da zasu yaki ta'addanci karkashi kasar Saudia ba tare da sahalewarsu duk da cewa kwansitushin din Nijeriya yace duk yarjejeniyar da Nijeriya zata shiga ko wacce kasa ne dole su sani bare maganar da ya shafi ƙawancan addini
Majiyar tace ya jiyo daga bakin sanatoci na APC dana PDP suna cewa dole ayi wa tufkar hanci don su ba zasu bari ayi wa jama'arsu sakiyar da ba ruwa ba.
Title :
Majalisar ASA Na Shirin Yin Fito Na Fito Da Buhari
Description : Bayanai dake fitowa na cewa majalisar dokokin Nijeriya ta shirya yin fito na fito da shugaba Buhari kan rashin mutunta tsarin mulki Nijeriy...
Rating :
5