Assalamu alaikum Wato malam ciwon fitsari nake fama dashi wlh idan nazo yinsa kamar raina zai fita nayi magani nayi maganin amma har yau Allah besa nayi dace ba Malam ataimaka min da shawari da kuma addu'a ko kuma maganin da zan dinga Amfani dashi Bissalam Amma a 6oye sunana Daga Dalibinka.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Shawarar da zan baka da farkon fari ita ce :
Kaje babban asibiti wajen Qwararren Likita ya dubaka, ayi maka manya manyan Gwaje-Gwaje domin fahimtar abinda ke haddasa maka wannan matsalar.
Watakil zata yiwu ko STD ne (wato Sexualy Transmitted diseases) Ko kuma wani Urinary Tract infection ne. Ko kuma watakil abun a bladder dinka ne. Ko kuma Qodarka.
Amma kafin nan ka samo albasa ka yankata Qanana Qanana acikin zuma sannan ka cinye tare da zumar, ka taune albasar sosai. Kayi hala har kwana uku zuwa hudu. In sha Allahu zaka ga chanji sosai. Zaka samu waraka.
Sannan ka nemi Furen Albabunaj ka rika dafawa kamar shayi kana shansa da zuma. Shima yana fitar da bawali daga jikin Dan Adam in sha Allah. Amma kafin kasha zaka rika diga man Habbatus sauda cokali guda acikin ruwan shayin.
Sannan ka nisanci abubuwa kamar su Biscuits, kayan Zaki, Garin Madara, etc.
Allah ya sawwake, Allah shi baka lafiya Aaameeen.
WALLAHU A'ALAM.
Title :
Maganin Matsalar Ciwon Fitsari
Description : Assalamu alaikum Wato malam ciwon fitsari nake fama dashi wlh idan nazo yinsa kamar raina zai fita nayi magani nayi maganin amma har yau All...
Rating :
5