Karamin Ministan Mai, Mr Ibe Kachikwu yaba yan Najeriya haukuri a yau a zauren majalisar dattawa akan maganar da yayi game da karar da layuka a gidajen mai.
Ya bada hakurin ne a lokacin da yake bayani akan yadda za’a iya kaudar wahalar Mai a Najeriya
Ministan ya bayyana cewa maganar shi wasa ce wadda bai kamata ace an buga ta a jarida ba.
” Nasan wahalar da yan najeriya suke ciki, ina jin wahalar da suke ji a kowacce rana idan na fito ina tafiya. A lokacin hutun nan ina Legas domin tabbatar da bada Mai. Awanni 24 na kulawa na bada.
“Ina aiki ne da burin cewa kowacce matsala sai na maganace ta domin haka ne ya sanya aka dauke ni.
“Ina bawa yan Najeriya hakuri akan maganar da nayi tare da abokai na yan jarida akan maganar dana ce ni ba matsafi bane. Nayi wannan ne a cikin wasa.
“Nayi bayani akan abunda ya kamata ayi, ban san maganar da nayi zata jaza irin wannan babban lamarin ba.
“Ina bayyana cewa ni ba kwararren dan siya sa bane. Ni ma’aikaci ne kuma aiki nazo inyi.
“Wasu daga cikin maganganun da zanyi a wurin aiki na za’a karbe su, amma a siyasance baza’a karbe su ba.
“Toh idan na bata ma wani rai ina mai bada hakuri.
Ministan ya kuma bayyana cewa rashin mai zaya kare nan bada dadewa b a.
Ya kuma yi godiya ga majalisar dattawan akan damar data bashi inda yabayyana cewa wannan ya nuna muhimmancin Mai a wajen Najeriya.
Idan za’a iya tunawa a wata fira da akayi da ministan ya bayyana cewa shi ba matsafi bane dan haka ba zaya iya karar da matsalar mai a cikin kwana 1 ba. Wanda wannan ne ya jawo mashi kulubale daga wajen jigon APC, Bola Tinubu.
Title :
Kachikwu Ya Ba Yan Nijeriya Hakuri Akan Matsalar Man Fetur
Description : Karamin Ministan Mai, Mr Ibe Kachikwu yaba yan Najeriya haukuri a yau a zauren majalisar dattawa akan maganar da yayi game da karar da layuk...
Rating :
5