.
Duk falon yayi tsit suna sauraren mami dake durqushe tana kuka wanda kukanta yayi matuqar tada hankalin umar da jidda Baffa yace mami Mun soma gajiya kin taramu kinsamu a gaba kina kuka shin meke faruwa Tace baffa alfarma nakeso kamin Dan Allah ka amince ka yarda karkace aa kaidasu baba Yace menene Aminatu Tace so nake Ku amince umar ya auri jidda Duk falon akayi shiru ana kallonta jidda kuwa kamar gabanta ya fadi saboda bugawar da yake Baffa yace Allah shi miki albarka Amina tabbas kinyi tunani mai kyau Allah shi Baku xaman lfy duk aka amsa da amin kuma kowa yaji dadin haka sun yaba mami da qarfin halinta Fuskarta dauke da murmushi take kallon umar da jidda taga tsantsan farinciki a tareda idanuwan umar amma taga tashin hankali a fuskar jidda nan da nan jikinta yayi sanyi ta tashi ta riqo jidda suka bar falon suna Shiga daki ta juyo tana kallon jidda Tace amaimakon inga farinciki a fuskarki kamar yanda nagani a fuskar umar sai naga sabanin haka menene jidda Sai ta fashe da kuka Tace meyasa kikamin haka meyasa kike sona haka baxan iya auren mijinkiba baxan iya kishi dakeba sai ta fashe da kuka Cikin qarfin hali mami tace ashe xaman kishi xamuyi dake jidda naxata xamuyi xamane kamar yanda muke xaune ada kafin muyi aure umar yayanmune kishin me xamuyi ta soma share mata hawaye fuskarta ynxu kika gayamin ina sonki nima ki tabbatar min da kina sona ki auri umar Sai ta fada jikinta tana kuka itama mamin kuka take sosai.
.
A daki dauke takeda jidda tana dariya tana mata tawai tana cirata sama tana mata waqa jidda marainiyar Allah jidda baiwar Allah kinata xubar da hawayenki Ni xan share miki kuka jidda ta soma dariya sosai itakuma ta fashe da kuka. Bayan saukowar masallaci ranar juma'a aka daura auren jidda da umar Rayuwa suke mai ban shaawa umar na kwatanta adalci tsakaninsu akoda yaushe yana tare dasu girkima tare suke su uku idan sun gama yaje da mami toilet ya mata wanka sannan yaje da jidda suyi wanka tare su fito cin abinci Suna son jidda suna bata kulawa duk abinda bataso suna kiyayeshi Xaka samesu falo xaune jidda kwance tayi matashi da cinyar mami qafafuwanta na saman cinyar umar yana mata tausa suna hira cike da nishadi Sai hakan ya farantawa family rai kowa hankalinsa na kwanta suka cigaba da rayuwa kamar da. Ana cikin haka jidda ta sami ciki karkuso ganin murna gun umar mami na daga gefe tana kallonsu tana dariya Ganin mami tabar falon ya dauki jidda cak ya nufi dakinsa da ita ya dorata saman gado ya shige jikinta yana kissing dinta sosai sai kuma ya fashe da kuka kukan dayayi matuqar tsorata jidda ta tallafo fuskarsa tana kallonsa Tace kukan menene Yace kukan baqin ciki da farin ciki jidda ina farincikin cika burina naganin na auri jidda xata kuma haifamin yaro sai dai mafarkina bai xama gsky ba na rayuwa da jidda ashe baxan rayu dakeba sai ya fashe da kuka Idanu a waje take kallonsa hankalinta yayi matuqar tashi Tace meyasa baxamu rayuba kagayamin dalili baqin cikinka Yakai bakinsa dai dai cibiyarta ya sumbata kafin yace idan kika mutu nima xn mutu jiddah can't do without you Tana hawaye fa rungumosa a qirjinta Tace shine kadai damuwarka ya girgixa kanshi aa Tace tor menene Yace tun yaushe kike fama da ciwon kai Tace an dade ya umar inajin tunkafin kadawo turai bn damu ba Dan bai fiye yimin ciwo sosai ba : Yace shine baki taba xuwa Asibiti aka dubaki ba kuma Baki taba gayawa kowa ba Tace eh Ya ja hannunta suka sauka saman gadon ya xauko laptop dinsa ya bude yana nuna mata Yace kinga ciwon dake kanki yaci qarfinki dayawa jidda tun jiya cikin dare danaji kanki da xafi na soma binciken kanki hrna gano ciwon Kinyi babban kuskure na rashin xiyarta asibiti kuma kinkasa gayamin amatsayina na likita sai ya fashe da kuka ya rungumeta Yace jidda kinsan wane irin ciwone ta girgixa kanta cike da tashin hankali Yana kuka yace cancer ce jidda ciwon yayi yawa akanki sosai ya qara fashewa da kuka itama kuka take sosai tana nanata innalillahi baxaki mutu kibarniba jidda nima xn mutu Hankalinta yayi matuqar tashi tace ya umar xan mutune Yayi saurin girgixa kansa cike da dabara yace aa ya tashi ya dauko magungunan daya siyo tun da safe yabata Yace ki kiyayeshansu da ixinin Allah xai daina ciwo akai akai amma dole wataran xaiyi Sanin danayi ko na fita dake asibitin waje tunda abun yayi qarfi suma magani kawai xasu baki ,na kira wani abokina dake can dubai xai dubamin wasu magungunan daya dace da ciwonki nariga na tura masa saqon hoton kanki Ta fashe da kuka Tace karka gayawa mami komi xai iya faruwa da ita kasan tanada ciwon xuciya likita yace duk abinda ya raxanata xai iyasa xuciyarta ta buga ta mutu Dan Allah yaya karka gaya mata kowama karka fadawa ya rungumota yana kuka yace I promise .
.
Xaune take tana hada magungunan da tagama sha hr cikinta ya soma fitowa mami ta shigo da sauri ta rungumeta tana fadin albishirinki sis ta juyo tana kallonta fuskarta dauke da murmushi tace goro sis, caraf idanunta nakai kan magungunan a firgice tace sis bakida lfy ne meke damunki kafin jidda tayi mgn tuni ta daukosu tana dubawa cike da tashin hankali tace cancer fa wakeda cancer k ko ya umar ta tmby tana hawaye jidda tayi qoqarin saita hankalinta taja dogon tsaki tana kallonta tace nifa tsiyata dake kenan komai kuka wakike xaton keda cancer a gidan nan babu kin tabaji ko kinga alama ta girgixa kanta tace aa amma wakeshan mgn jidda ta kauda kanta na patient din ya umar ne yakawo masa ne ya duba masa nima jiya nagansu na tmby mami taja gwaron numfashi tana goge kwallarta tace ina ce kece amma hankalina ya kwanta ynxu kinsan alqawarin xuriyarmu na rayuwa tare mu mutu tare jidda ta dan dubeta ta wutsiyar ido kafin ta kawarda xance tace muyi abu mai muhimmanci sis albishir din me kike min mami taja gwaron numfashi kibarni hr ynxu xuciyata bata kwantaba tunani nakeyi idan babu k ko babu ya umar yaxan qare a duniya nan sai ta fashe da kuka jidda sai taji hankalinta ya tashi tace kin soma isata pls meyasa kike kiramin mutuwa ynxu meyasa baki yarda daniba ana boye ciwone sai ta girgixa kanta tace naji na yarda kinsan me ya kawoni ta tsura mata ido tace kitayani murna jidda cikine dani tsakaninsa danaki wata daya ne jidda ta rungumeta tana dariya da kuka tace kinga nagayamiki rabone ko karkicire tsammani daga rahamar ALLAH Mami ta gyada kai hakane sis Allah ya saukemu lfy AMIN BAYAN WATANNI jidda ta sauka lfy ta sami yar'ta mace karo na biyu sak umar yarinyar taci sunan handiya wato Aisha suna kiranta ummi tana samun kulawa sosai gun umar sun boye sirrinsu ga kowa kamar yanda umar k qoqarin boyewa jidda irin ciwon kanta gudun kada hankalinta ya tashi daka ganshi yana cikin damuwa ya rame sosai bashida wani aiki sai tunani ko a asibiti hr cikin dare yake tashi yayita kuka ba wanda yasani nan take ya kamu da ciwon xuciya batare da sanin kowaba. da sassarfa ya shigo dakin jin sautin kukan jidda ya sameta xaune tana yiwa ummi tawai tana dry da kuka taho taho ummina kyakkyawa inmiki tawai , gaki fara tamkar babanki sai kuma ta fashe da kuka umar ya rungumota ta baya yace kigayamin me kikafiso a rayuwarki kai tsaye tace ummi Aisha ina son yarinyar sosai ina sonta fiyeda jidda qarama bansan dalili ba ta fada tana kallonsa ya kawarda kansa gefe yace kinason ummi fiyeda jidda qarama saboda kinfi son baban ummi akan faisal, ta shimfide ummi ta juyo tana kallonsa hannunta cikin nasa tace na kasa haqura na kasa jurewa hrtakaiga na sanarwa ammina halin dana k ciki, ya tsura mata ido tacigaba da fadin ammi mahaifiyatace tanada haqqi akaina bansan yaxaji idan na boye mataba ciwon ya bayyana shiyasa na kasa jurewa na gayamata amma ka yafemin na karya alqawari ya umar sai ta fashe da kuka ta fada jikinsa ya qanqameta shima yana hawaye yace kowa yasan da mgn mami ce kawai saura ynxu baffa ya kirani yace a fitadake waje a qara dubaki bai yarda da cancer ce akankiba ynxu haka hankalin kowa a tashe yake jidda kika mutu nima xn mutu mami da ciwon naquda da ya tasomata taxo ta gayamasu jin maganganunsu yasa ta tsaya tana saurare hankalinta yayi matuqar tashi jiddace da cancer sai tasaki qarar dana janyo hankalinsu gareta ta fadi sumammiya jidda ta fashe da kuka tafaru ta qare A gaggauce suka nufi asibiti da ita baa fi minti goma ba asibitin ta cika cikin minti talatin ta sumulyo itama yar ta mace kyakkyawa tamkar mamin farin babnta kawai ta dauko tun bayan haihuwarta take kuka ko yar taqi kulawa duk xumudinta akan haihuwar duk dakin akayi cirko cirko saboda tashin hankali jidda na kuka ta riqo ta tace kinsan matsalarki mami kike tayarda hankalinki ta kwace hannunta daga gareta tace ki barni ba ruwanki dani ciwona ba damuwarki bane kamar yanda kika nuna ciwonki ba damuwata bane...
.
Umar ya katseta haba mami saboda lfyrki jidda ta boye ciwonta gareki tayi saurin girgixa kanta kubarni kuje banason ganin ku kuje kuyita boye sirrinku gareni ku kyaleni sai ta juya masu baya jidda ta dora kanta jikin gadon tana kuka umar kuwa hankalinsa na tashi yace bakya buqatarmu mami meyasa dan ALLAH kiyi haquri ganin halinda suke ciki kowa yaja jiki ya fita cike da jimami suna fita ya rungomo mamin fuskarsa dai dai kafadarta yace kinyi fishi da umar dinki da gudan jiddanki saboda mun nuna qaunarmu gareki ta juyo da fuskarsa tana kallonsa tace meyasa kuka fiye sona haka meyasa kukamin haka yace ina tsoron rasa cikinki ne ina tsoron bayan kin haihu ciwon jidda ya tada hankalinki xuciyarki ta buga kubarni da jinjiran yara ba iyaye sai ya fashe da kuka ya rungumeta baxan jureba baxan iya rayuwa ba jidda da mami ba duk suma suka fashe da kuka jidda tabar dakin da sauri. Ranar suna yarinyar taci sunan maryam Tun daga lokacin suka soma rayuwar qunci bamasuba hr iyayensu koda yaushe xaka sami gidan shiru tamkar ba kowa a gidan cikin haka bixarsu ta fito suka dunguma hr baffa sadauki akaje asibitin dake dubai duk qoqarin likitocin sun kasa shawo ciwon sunriga sunsan ciwon yayi yawa hr ya xagaye kwakwalwarta sai dai sun bata magungunan ganin ba nasara suka cnxa asibiti xuwa madina gsky ba laifi ta soma samun sauqi tunda tadan rage xafin kai da lokacin hajji ya xagayo suka dunguma makkah su hudu acikin kwanakinsu na xamansu makka baa abinda suke sai addua da neman gafara basa barci koda yaushe suna cikin adduar nemawa jidda sauqi da gafara hr suka gama aikin suka dawo gida nigeria inda dangin kakaf suka taru domin jin lbr ciwon jidda sai dai hankalinsu yayi matuqar tashi jin ciwon baxai warkeba. gaba daya family sadauki cike suke da fargaba mussam ranar da ciwon ya kayarda jidda aka nufi asibiti da ita kakakaf ba wanda bai hallaraba ba wanda baiyi ma jidda kuka ba domin ta fita hayyacinta gadon da take kwance akai rawa yake saboda jikin jidda dake rawa kallo daya xakawa ammi kagane cikin tashin hankali take xatarasa yarta guda kacal a duniya nan take jininta na hau mami na maqale da jidda sai faman surutai takeyi dole kowa na dauki kuka. Misalin qarfe goma sha biyu na dare ba wanda ya rumtsa kuma kowa yakasa xuwa gida , cikin ikon ALLAH jikin jidda nayi sauqi xaxxabin na sauko hrta tashi xaune da kanta tana neman abinci duk dakin aka cika da murna da sauri umar da mami nayi yunqurin kawo mata abinci ta dubesa fuskarta dauke da murmushi ta dubi yanda mutane suka cika dakin lallai tana da gata ta yarda ana sonta sosai ta soma share hawayenta mami ta tsaya turus tana kallonta kukan me jidda gashi kinsami sauqi kibari karki tada hankalinmu ta dubi mamin tace ina kuka xuciyarmu ta kasa cika alqawarinta naxamu rayu tare mu mutu tare gashi mutuwa xata rabani da kowa nawa sai ta goge kwallah ta karbi abinci hannu umar da jikinsa yayi lagwab yana kallonta ta soma ci ba kakkautawa batare da ta damu da yanda mutanen dakin k kallontaba taga duk jikinsu yayi sanyi kuma qarfin haline take dan xuciyarsu ta kwanta amma axahirin gsky tanajin jiki sosai ta tashi ta nufi toilet umar na biye da ita ko kunyar surukansa bayaji suka shiga toilet din tare tayi fitsari suka fito ta xauna kan gado cikin dauriya take murmushi ta janyo jidda dake hannu mama bilkisu dakyar ta cirata sama ta soma yi mata tawai wannan karon dariya take da ita hr jiddan jidda marainiyar ALLAH jidda baiwar ALLAH kinata xubarda hawayenki waxai sharemiki kuka tayi waqar kusan sau uku tana mata tawai fuskar kowa dauke da damuwa ta miqata ga ammi tace ammina ga jidda halaq malaq na baki ita amaimakon ni daakiyi rashi xaki rasa jidda gakuma wata jidda ammi ta fashe da kuka ta karbi jidda jidda tayi murmushi ta karbi ummi hannu abbanta ta bata nono sosai tana kallon yarinyar ta dade tana bata nono kafin ta cirata sama sai ummin ta kyalkyale da dariya irinta yara itama jidda tayi dariya tana fadin taho taho ummina kyakkyawa inmiki tawai sai da tagama waqar ta miqata hannu handiya tace Handiyata ga ummina ina sontafiye da komai a rayuwata ta miqa mata ita ta juya tana kallon mutanen dakin ta soma neman gafarar su sai suka fashe da kuka jikinta na soma rawa da kyar ta hada hannu mami da umar tana murmushi bakinta ya kasa furta komai ganin numfashinta ya soma sarqewa tasoma kalmar shahada tana gamawa numfashinta na tsayawa cak YA SALAM mami ta daga hannuta taga ba alamar rai atare da jidda sai ta saki qara ta fadi kafin ta kai qasa tuni xuciyarta ta buga umar ya tare ta yanajin sautin numfashinta sanda take kalmar shahada kafin ranta ya aje WAYYO nan take hankalin kowa na tashi musamman umar idan ya kalli gawar jidda ya kalli ta mami hankalinsa yayi matuqar tashi tamkar yayi hauka da kyar aka samu aka fitardashi dakin ana lallashinsa washe gari ranan xuciyar umar na buga ya amsa kiran mahallicinsa NA SHIGA UKU.
.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN shine abinda daukakin xuriar sadauki da mutanen arxiki k nanatawa a bakinsu lokacin da aka jero gawarsu su uku ana masu sallah kullu nafsin xa'iqatil mauti duk mai rai mamacine ALLAH baya barin wani dan wani yaji dadi gidan ya dauki kuka lokacin da aka dauki gawarsu su uku aka fita da ita duk cikinsu handiyace tayi qarfin masu addua su uku tanayi tana kukan rashin tilon danta umar da kyar aka banbareta daga garesa duk dauriya juriya irinta iyayen maxa sai da suka xubar da kwallah ba umar ba jidda da mami ALLAH ya jiqansu AMIN (axo amin gaisuwa ) DAWOWA DAGA LBR handiya ta fashe da kuka tare da daukakin mutanen dake falon ta kalli sufyanu da farida tace kasani cikin yaranmu kaika dai ka rage mana sai jikokinmu ka janye mgnrka ta Amir ya auri jidda abar Mohd ya auri jidda abar kowa ya auri wanda yakeso kar abinda ya faru a baya a maimaitashi ta fashe da kuka.
END ALHAMDULILLAH
.
sai mun hadu a jiddah 4 anjima da yamma dan jin waxai auri jidda wayafi cancanta da auren jiddah anya AMIR xai barwa MUHD JIDDAH kuwa?
.
#Hausa Novel📓
#IP
Title :
Jiddah - Part 3
Description : . Duk falon yayi tsit suna sauraren mami dake durqushe tana kuka wanda kukanta yayi matuqar tada hankalin umar da jidda Baffa yace mami Mu...
Rating :
5