DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Daruruwan jama'a mazauna garin Dan Hono dake yankin Sabuwar Kaduna, sun gudanar da wata gagarumar Zanga-zanga, da yin tofin Allah tsine akan abinda suka bayyana zaluncin El Rufa'i, na kaddamar da rusau a yankinsu, kuma ba tare da basu wata diyya ba.
Masu zanga-zangar wadanda suka yada zango a cibiyar 'Yan Jaridu dake Garin Kaduna, sun rinka rera wakoki masu ban tausayi da zubar da hawaye, akan matakan rusau na sharesu daga bayan Kasa da gwamna El Rufa'i ya kaddamar.
Mai magana da yawun jama'ar Malam Mansur Suleman, yace suna da kwararan hujjoji da suka tabbatar da cewar El Rufa'i ya ziyarci Dagajin Kauyen su na Dan' Hono, mai suna Yusuf Gajere inda ya tabbatar mishi da cewar yana bukatar ya zama shaida akan cewar dukkanin Kasar Dan'Hono mallakar gwamnatin Jihar Kaduna ne, kuma idan yaki amincewa da wannan umarni to ya sani cewar za'a yi mishi azaba irin wacce akayiwa Sarakunan Gwarawa a yankin Abuja, har saida suka bada kai bori ya hau, a lokacin da El Rufa'i yake matsayin Minista.
Mansur Suleman ya cigaba da cewar, sun gaji gidaje da gonakin sune daga wajen Iyaye da Kakannisu shekaru da dama, saboda haka babu adalci azo a yanzu a rurrushe musu gidaje, sannan ace baza'a basu ko kwabo a matsayin diyya ba.
Saidai a nata bangaren gwamnatin jihar Kaduna, ta bakin Babban Daraktan hukumar tsara Biranen Kaduna Alhaji Ibrahim Husaini, ya musanta dukkanin wadannan korafe-korafe, inda yace dukkanin wanda ya mallaki takardun gida ko fili akan ka'ida ta hannun gwamnati, to ko shakka babu zai samu kudin diyya daga gwamnati.
Source Rariya
Title :
Jama'ar Sabuwar Kaduna Sun Yi Zanga-zangar Allah Wadai Akan Rusau Din El Rufa'i
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Daruruwan jama'a mazauna garin Dan Hono dake yankin Sabuwar Kaduna, sun gudanar da wata gagarumar Zanga-za...
Rating :
5