Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina Sautus-Sunnah shine shugaban kwamitin Shirya taron kasa-da kasa da aka kammala gabatarwa a yau karkashin inuwar JIBWIS da hadin gwiwar
majalisar musulunci ta duniya. Haka zalika, daya daga cikin makusantan Magatakardar Majlisar muslunci ta duniya Ash Sheikh Turki. A zantawar wakilanmu da shugaban kwamitin,
yabayyana cewa jita jitar sace wayar babban malamin ba gaskiya bane. Inda yakara da cewa a matsayinshi na shugaban kwamitin taron, bai sami bayanin aukuwar hakan ba daga bakin
shaihun malamin ko kuma shugaban kungiyar ta JIBWIS. A wani kaulin kuma, daya daga cikin jiga-jigan kwmitin shirya taron, Dr. Ibrahim
Rijiyar Lemo ya bayyana cewa wayar daya daga cikin mukarraban shaihun malamin ne maisuna Shakir, ta bace. Inda shi mai wayar ne yamanta inda ya ajiye. Shaikh Turki de ya ziyarci kasar Nigeria ne bisa dalilin halartar taron kasa da kasa da JIBWIS gami da RABIDA suka shirya wanda taron yasamu halartar
shugaban Nigeria Muhammadu Buhari.
Harwa yau Dr. Ibrahim yabayyana rashin gamsuwar shi game da yadda jaridun
Nigeria ke yada farfaganda batare da bin
diddigiba daga jagororin shirya taron ba. Dan haka muna kira ga gidajen jaridu, da
ku kuji yada jita jita akan abin da baku
da tabbas. Yanayin tsaro da aka baiwa
Shehun malami At-Turki, babu wanda ya
isa ya tinkari inda yake, bare ma har a
sace masa waya, wannan labari bashi da asali, dan haka aji tsoron Allah. —
Title :
Izala ta Karyata Jita-Jitar Sace Wayar
Shaihun Malami,Abdul Muhsin At-Turki
Description : Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina Sautus-Sunnah shine shugaban kwamitin Shirya taron kasa-da kasa da aka kammala gabatarwa a yau karkashin i...
Rating :
5