Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana sane da irin halin da ‘yan kasa suke ciki, na matsi da kuncin rayuwa, kamar yadda majiyarmu ta Vanguard ta ta rawaito.
Buhari ya kara da cewa a yi hakuri da yardar Allah komsi zai dai-daita. Domin ya yi matukar mamaki da yadda ya samu kasar nan a cikin halin magagi na mutuwar tattalin arzikin kasa daga gwamnatin da ya gada ta PDP.
Don haka yazama wajibi su tabbatar da dukiyar Jijeriya ta dawo daga hannun azzaluman da suka wawushe ta ta haramtatciyar hanya. Sannan za su samu damar yi wa jama’ar kasa ayyukan da suka dace.
Buhari ya kara da cewa a ci gaba da yin hakuri, bayan kunci sai waraka da yardar Allah komai zai zama tarihi zuwa wani dan lokaci. Don haka yana kira ga al’ummar kasar nan kama daga Musulmi da Kirista da su ci gaba da yin addu’a.
Title :
Ina Sane Da Mawuyacin Halin Da Ake Ciki A Kasar Nan, Inji Shugaba Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana sane da irin halin da ‘yan kasa suke ciki, na matsi da kuncin rayuwa, kamar yadda majiy...
Rating :
5