HUKUNCIN WANDA YA KASHE 'DAN FASHI
TAMBAYA TA 1891
*******************
Assallamu'alaikum wa ramatullah, da fatan ka waye gari lafiya, ya akaji da ďawainiya damu? Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi ya jikan iyayen mu ya kuma sa Al-jannatul Firdausice makoman mu baki daya, Mallam Allah ya'karama hakuri da dauriyan issar da sakonsa akoyaushe ameen. Saide nasha yin tambaya amman tunda nake tambaya saudaya akata'ba amsamin koda yake nasan tambayoyin sukan shigo dayawa akullum, dafatan za'a samu amsamin wannan.
(1) Macece keshan wuya sosai duk sanda ta samu junabiyu harma kagan kaman za'a rasa ranta duk dacewa tahaifi nafarko, nabiyi harzuwa nahuďu amman abin baicanzaba, shin za'aiya tsayamata da haihuwa?
(2) Amatsayin mutum na jamiyin tsaro sai sukayi musanyan wuta da yan ta'adda ko yan fashi da makami sai ya kashe daya ko biyu daga cikin yan fashin nan, shin zayi azumi ne dan kisa da yayi ko ya hukuncin yake.
Allah ya bada ikon amsawa ameen.
Daga (ALIYU YAKUBU ANZAKU) dalibin Zauren fiqhu.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
1. Bisa yadda aka saba gani yau da kullum, kowacce mace takan samu laulayi yayin da ta dauki juna biyu. Sai dai na wata yafi na wata.
Bisa dokar addinin Musulunci, Bai halatta Musulmi ya tsayar da haihuwa gaba daya ba, sai dai idan akwai hatsarin rasa-rai acikin ci-gaba da haihuwar.
Misali dole sai dai in Likitoci ne (Kwararru) suka tabbatar muku da cewa lallai idan ta sake daukar ciki to za'a iya rasa ranta, ko kuma rayuwar abinda take dauke dashi. To anan ya halatta a tsayar ds haihuwar baki daya.
Amma shan wahala yayin laulayin ciki, wannan ba hujjah bane. Sai dai idan laulayin cikin yana jefata cikin hauka, ko kuma hadarin rasa ranta.
Amma ya halatta ku bada tazara atsakanin 'ya'yanku domin yaranta su rika yin Qwari kafin ta samu wani cikin.
2. Shi 'dan Sanda (Police) yana daga cikin manyan ayyukansa bada kariya ga dukiyoyin al'ummah da kuma rayukansu. Don haka suke yawan samun artabu tsakaninsu da 'yan fashi.
Shi 'dan sanda Wakilin hukuma ne da kuma al'ummah. Don haka yana yin fa'da ne amadadinsu. Shi 'dan sanda Musulmi idan 'yan fashi sun kasheshi awajen aikinsa to lallai shi Shahidi ne. Hakanan idan ya kashe 'dan fashi to babu diyyah ko azumin kaffarah akansa. Koda 'dan fashin Musulmi ne.
Ga Hujjoji nan daga hadisan Manzon Allah (saww) :
a). Hadisi daga Sayyiduna Sa'eed bn Zaid (ra) yace Manzon Allah (saww) yace : "DUK WANDA AKA KASHESHI YANA KOKARIN KARE DUKIYARSA TO SHAHEEDI NE. WANDA AKA KASHESHI YANA KOKARIN KARE IYALINSA MA SHAHEEDI NE. WANDA AKA KASHESHI YANA KOKARIN KARE ADDININSA MA SHAHEEDI NE. WANDA AKA KASHESHI YANA KOKARIN KARE RANSA MA SHAHEEDI NE".
ADUBA : Sunanut Tirmidhiy hadisi na 1421. Sunanun Nisa'iy hadisi na 4095. Sunanu Abi Dawud hadisi na 4772.
b). Hadisi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace : "Wani mutum yazo wajen Manzon Allah (saww) sai yace : "Ya Rasulallahi mae kake gani idan wani yazo zai Kwace min dukiyata?".
Sai Annabi (saww) yace "KAR KA BASHI DUKIYARKA".
Sai yace "To yaya kake gani idan ya Yaqeni? (Wato yayi fa'da dani)".
Sai Annabi (saww) yace : "KAI MA KA YAQESHI".
Sai yace "To yaya kake gani idan ya kasheni?"
Sai Annabi (saww) yace "IDAN YA KASHEKA TO LALLAI KAI SHAHEEDI NE".
Sai yace "To idan ni na kasheshi fa?".
Sai Annabi (saww) yace "IDAN KA KASHESHI TO SHI YANA CIKIN WUTA"
(Aduba Sahihu Muslim hadisi na 140).
Idan mun dubi wancan hadisin na farko zamu ga cewa shi 'dan sandan yana yin fa'da ne don bada kariya ga rayuwarsa da kuma rayuwar Jama'a da dukiyoyinsu. Shi kuma 'dan fashin nan idan ya samu dama zai iya kashe 'dan sandan, ya kashe Jama'ar, sannan ya dauke dukiyarsu. Don haka don an kasheshi babu kaffara ko diyyah.
Sannan acikin hadisi na biyu, shi 'dan sanda anan shine wakilin Jama'a. In dai yana yin aikinsa ne bisa tsarin yadda hukumar Qasa ta daukeshi. To idan ya kashe 'dan fashi babu diyyah ko kaffarah akansa.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Title :
Hukunci Wanda Ya Kashe Dan Fashi
Description : HUKUNCIN WANDA YA KASHE 'DAN FASHI TAMBAYA TA 1891 ******************* Assallamu'alaikum wa ramatullah, da fatan ka waye gari laf...
Rating :
5